Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 107

Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Kauna

Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Kauna

(1 Yohanna 4:19)

  1. 1. Jehobah Allah ya kafa misali

    Na ƙauna, na ƙauna.

    Ya nuna ƙauna ga dukan ’yan Adam,

    Mu ƙaunaci mutane ma.

    Jehobah Uba, ya aiko da Yesu

    Don ya gafarta laifofin ’yan Adam.

    Babu mai ƙauna irin ta Jehobah,

    Jehobah mai ƙauna ne sosai.

  2. 2. In mun bi misalin Allah Jehobah

    Yadda ya yi ƙauna.

    Za mu ƙaunaci dukan ’yan’uwanmu,

    Ba ƙiyayya, ba bambanci.

    Kar mu ce muna ƙaunar Maɗaukaki,

    Amma mu ƙi bin dokar da ya ba mu.

    Mu so ’yan’uwa duk da kasawarsu,

    Mu yi ƙauna da duk zuciya.

  3. 3. Ƙauna tana sa mu zama tsintsiya

    Mai maɗauri ɗaya.

    Shi ya sa Jehobah ke gayyatar mu:

    “Mu kasance da haɗin kai.”

    Mu zauna tare, mu more salama,

    Kalmarsa da ruhunsa na da iko.

    Suna sa mu ƙaunaci ʼyan’uwanmu

    Domin Jehobah na da ƙauna.

(Ka kuma duba Rom. 12:10; Afis. 4:3; 2 Bit. 1:7.)