Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 108

Kauna ta Gaskiya Daga Allah

Kauna ta Gaskiya Daga Allah

(Ishaya 55:1-3)

  1. 1. Allahnmu mai ƙauna

    Ya damu da mu ajizai.

    Ya aiko mana mai ceto

    Don ya ’yantar da mutane.

    Ya sa dukanmu mu rayu

    Har abada a aljanna.

    (AMSHI)

    Duk masu ƙaunar Allah,

    Zo ga ruwan rai kyauta.

    Ku zo ku sha ku ƙoshi,

    Don ku sami ceto.

  2. 2. Allah na da ƙauna,

    Ayyukansa sun bayyana

    Ƙaunarsa ga duk mutane.

    Ya naɗa Sarkin Mulkinsa

    Domin ya cika nufinsa,

    Kuma Mulkinsa ya kafu.

    (AMSHI)

    Duk masu ƙaunar Allah,

    Zo ga ruwan rai kyauta.

    Ku zo ku sha ku ƙoshi,

    Don ku sami ceto.

  3. 3. Mu riƙa yin ƙauna

    Don Jehobah na da ƙauna.

    Mu taimaka wa adalai

    Su riƙa biɗar adalci.

    Za mu riƙa yin wa’azi

    Da ƙarfin zuciya sosai.

    (AMSHI)

    Duk masu ƙaunar Allah,

    Zo ga ruwan rai kyauta.

    Ku zo ku sha ku ƙoshi,

    Don ku sami ceto.

(Ka kuma duba Zab. 33:5; 57:10; Afis. 1:7.)