WAƘA TA 109
Mu Kasance da Kauna ta Gaske
(1 Bitrus 1:22)
-
1. Allah zai yi murna da mu
In muna yin ƙauna sosai.
Ƙauna na da muhimmanci,
Halin Jehobah ne.
In muna ƙauna da gaske
Abokantaka zai yi kyau,
Za mu mutunta mutane
In muna da ƙauna.
Zai dace mu taimaka
In ’yan’uwa na da bukata,
Domin hakan zai nuna
Mun san yadda suke ji.
Yesu ya nuna mana duk
Irin ƙauna ta Allahnmu,
Don mu riƙa nuna ƙauna,
Ƙauna ga duk mutane.
Mu zama masu ƙauna.
(Ka kuma duba 1 Bit. 2:17; 3:8; 4:8; 1 Yoh. 3:11.)