Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 111

Dalilan da Suke Sa Mu Murna

Dalilan da Suke Sa Mu Murna

(Matta 5:12)

  1. 1. Muna da dalilan yin murna

    Da yawa babu iyaka.

    Jama’a daga duk al’umma

    Na bauta wa Maɗaukaki.

    Gaskiyar da ke Kalmar Allah

    Na sa mu yin murna sosai.

    Shi ya sa muke nazarin ta

    Domin mu kusaci Allah.

    Muna da dalilan yin murna

    Daga cikin zuciyarmu.

    Ko da muna fama da ƙunci,

    Jehobah zai taimake mu.

    (AMSHI)

    Jehobah Allah mun gode,

    Duk ayyukanka na da kyau

    Da hikimarka da ayyukanka,

    Na sa mu yi murna sosai!

  2. 2. In mun lura da ayyukanka,

    Duniya, sararin sama,

    Da kuma sauran halittunka,

    Muna miƙa maka yabo.

    Mun ƙudurta mu sa a sani

    Game da Mulkin Allahnmu.

    Da albarkun da za mu samu,

    Muna koya wa mutane.

    Za mu yi murna har abada,

    Za mu ji daɗin rayuwa,

    Rayuwa a cikin aljanna

    Zai kawo albarka sosai.

    (AMSHI)

    Jehobah Allah mun gode,

    Duk ayyukanka na da kyau

    Da hikimarka da ayyukanka,

    Na sa mu yi murna sosai!

(Ka kuma duba K. Sha. 16:15; Isha. 12:6; Yoh. 15:11.)