Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 117

Mu Rika Yin Alheri Kamar Allah

Mu Rika Yin Alheri Kamar Allah

(2 Labarbaru 6:41)

  1. 1. Ya Jehobah, Mai alheri,

    Kai Allah ne mai ƙauna.

    Kai Allah ne mai aminci,

    Hanyoyinka na da kyau.

    Kana nuna mana jinƙai,

    Duk da kasawarmu fa.

    Kai kaɗai za mu bauta wa

    Ya Jehobah Allahnmu.

  2. 2. Duk bayinka na yin koyi

    Da irin alherinka

    Ta yadda suke rayuwa

    Da kuma yin wa’azi.

    Ana shelar koyarwarka

    A cikin duk duniya.

    Ba mu ruhunka mai tsarki

    Don mu nuna alheri.

  3. 3. Ya Allahnmu muna roƙo

    Ka albarkace mu don

    Alherin da muke nuna

    Wa dukan ’yan’uwanmu.

    Ba mu ruhunka mai tsarki

    Don ya taimaka mana,

    Mu riƙa nuna alheri

    Ga kowa a duniya.

(Ka kuma duba Zab. 103:10; Mar. 10:18; Gal. 5:22; Afis. 5:9.)