WAƘA TA 121
Mu Rika Kame Kanmu
(Romawa 7:14-25)
-
1. Muna son Allah Jehobah sosai,
Amma wajibi ne mu kame kanmu.
Sha’awar jiki matsala ce
Bin dokar Allah na ba da rai.
-
2. Shaiɗan na jarabtar mu koyaushe.
Ajizanci na sa jimrewa wuya,
Amma Allah na taimakon mu.
Muna godiya ga Allahnmu.
-
3. Mutane za su ɗaukaka Allah
Domin halayenmu da ayyukanmu.
Sai mu ƙudura niyyar cewa
Duk za mu riƙa kame kanmu.
(Ka kuma duba 1 Kor. 9:25; Gal. 5:23; 2 Bit. 1:6.)