WAƘA TA 124
Mu Kasance da Aminci
(Zabura 18:25)
-
1. Za mu riƙa yin biyayya
Ga Jehobah Allahnmu.
Za mu bi duk umurninsa,
Za mu riƙe aminci.
Bin dokokinsa na da kyau,
Suna taimaka mana.
Ya Jehobah, mai aminci,
Za mu bi umurninka.
-
2. Za mu riƙa yin alheri
Ga dukan ’yan’uwanmu.
Za mu riƙa nuna cewa
Muna ƙaunar su sosai.
Za mu daraja su sosai
Da dukan zuciyarmu.
Da aminci, za mu bauta
Wa Jehobah Allahnmu.
-
3. Da aminci za mu riƙa
Bin umurnin dattawa.
In suna yin ja-goranci,
Mu riƙa yin biyayya.
Yin hakan zai sa Jehobah
Ya yi mana albarka.
Sai mu riƙe amincinmu,
Ga Jehobah Allahnmu.
(Ka kuma duba Zab. 149:1; 1 Tim. 2:8; Ibran. 13:17.)