Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 125

Masu Jinkai Suna Farin Ciki!

Masu Jinkai Suna Farin Ciki!

(Matta 5:7)

  1. 1. Jehobah na da tausayi

    Kuma yana son mu sosai.

    Shi mai son yin nagarta ne,

    Yana biyan bukatunmu.

    In muka yi kurakurai

    Kuma muka yi addu’a.

    Jehobah zai gafarce mu

    Don ya san ajizai ne mu.

  2. 2. In muka yi tuban gaske

    In muna son gafartawa,

    Yesu Kristi ya ce mana

    In mun yi addu’a mu ce:

    ‘Allah ka gafarta mana,

    Yadda muke gafartawa.’

    In mun yafe wa mutane,

    Za mu sami kwanciyar rai.

  3. 3. In muna son ba da kyauta,

    Muna yin koyi da Allah.

    Mu taimaki mabukata,

    Mu yi hakan da yardar rai.

    Jehobah Allah mai ƙauna,

    Zai albarkace mu sosai.

    Masu jinƙai suna murna,

    Allah yana daraja su.

(Ka kuma duba Mat. 6:​2-4, 12-14.)