WAƘA TA 132
Yanzu Mun Zama Daya
(Farawa 2:23, 24)
-
1. A ƙarshe ga kamanina,
Da jikina, ina godiya.
Allah ya ba ni mai so na
Da mataimakiya.
Yau mun zama iyali fa,
Za mu riƙa samun albarka.
Za mu bauta wa Jehobah
Don shi ne Allahnmu.
Kalmarsa na taimaka mana,
Kalmar tana sa
Mu riƙa ƙaunar juna.
Wa’adi ne, za mu cika,
Hakan zai sa mu riƙa murna.
Idan mun daraja Allah
Za mu so junanmu sosai.
(Ka kuma duba Far. 29:18; M. Wa. 4:9, 10; 1 Kor. 13:8.)