Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 133

Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu

Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu

(Mai-Wa’azi 12:1)

  1. 1. Allah yana ƙaunar mu matasa,

    Mu bauta masa da duk ƙarfinmu.

    Don haka, zai riƙa kula da mu,

    Zai albarkace mu har abada.

  2. 2. Mu riƙa daraja iyayenmu

    Domin suna kula da mu sosai.

    Allah da mutane za su so mu,

    Kuma za mu kusaci Jehobah.

  3. 3. Mu riƙa tunawa da Jehobah,

    Mu ci gaba da son koyarwarsa.

    Mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu, don hakan

    Zai sa Jehobah murna.

(Ka kuma duba Zab. 71:17; Mak. 3:27; Afis. 6:​1-3.)