Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 135

Jehobah Ya Ce: “Dana Ka Yi Hikima”

Jehobah Ya Ce: “Dana Ka Yi Hikima”

(Misalai 27:11)

  1. 1. ’Ya’ya ƙaunatattu

    Ku riƙa bauta min.

    Maƙiyi zai ji kunya

    in kun bauta min.

    Ku riƙa bauta min

    da duk zuciyarku

    Domin in riƙa yin

    alfahari da ku.

    (AMSHI)

    Ku yarana da nake ƙauna,

    Ku sa in riƙa yin murna.

    In kun zaɓi ku bauta mini,

    Ku yi hakan da yardar rai.

  2. 2. Ku yi murna sa’ad da

    Kuke bauta min,

    In kun shiga matsala

    Zan taimake ku.

    In maƙiya suna

    Ƙuntata ku sosai,

    Zan taimaka muku

    Kome matsaloli.

    (AMSHI)

    Ku yarana da nake ƙauna,

    Ku sa in riƙa yin murna.

    In kun zaɓi ku bauta mini,

    Ku yi hakan da yardar rai.

(Ka kuma duba K. Sha. 6:5; M. Wa. 11:9; Isha. 41:13.)