WAƘA TA 138
Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja
(Misalai 16:31)
-
1. ʼYan’uwanmu tsofaffi
Muna ƙaunar ku.
Mun san cewa kun jimre
Da jarrabawa.
Yanzu ba ku da ƙarfi,
Kuna ciwo ma.
Don amincinsu Uba,
Ka sa su rayu.
(AMSHI)
Ya Uba, ka tuna
Da amincinsu.
Bari su san cewa
Kana ƙaunar su.
-
2. Tsofaffi amintattu
Masu daraja.
Jehobah na ƙaunar su
Don amincinsu.
Akwai lokacin da su
Matasa ne fa,
Kuma sun yi hidima
Da ƙwazo sosai.
(AMSHI)
Ya Uba, ka tuna
Da amincinsu.
Bari su san cewa
Kana ƙaunar su.
(Ka kuma duba Zab. 71:9, 18; Mis. 20:29; Mat. 25:21, 23; Luk. 22:28; 1 Tim. 5:1.)