Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 141

Rai, Kyauta Ce Daga Allah

Rai, Kyauta Ce Daga Allah

(Zabura 36:9)

  1. 1. Duk abu mai rai da ruwan sama,

    Da kuma hasken rana da abinci.

    Jehobah ne ya yi tanadin su.

    Su ne suke sa mu ji daɗin rayuwa.

    (AMSHI)

    Amma, me za mu yi da rayuwarmu?

    Mu riƙa so da kuma bauta wa Jehobah.

    Ba cancanta ba ce za ta ba mu rai ba,

    Domin rai kyauta ce, kyauta daga Allah.

  2. 2. Wasu na kamar matar Ayuba,

    Suna yin sanyin gwiwa don ƙuncinsu.

    Mu ba ma hakan, za mu yabe shi,

    Mu kuma gode masa don rayuwarmu.

    (AMSHI)

    Amma, me za mu yi da rayuwarmu?

    Mu riƙa ƙauna da kuma kula da juna.

    Ba cancanta ba ce za ta ba mu rai ba,

    Domin rai kyauta ce, kyauta daga Allah.

(Ka kuma duba Ayu. 2:9; Zab. 34:12; M. Wa. 8:15; Mat. 22:​37-40; Rom. 6:23.)