WAƘA TA 144
Mu Rika Dokin Samun Ladan!
(2 Korintiyawa 4:18)
-
1. A aljanna a duniyar nan,
Allah za ya cire duk cuta.
Waƙar yara, murna, salama,
Duk za su cika ko’ina,
Kuma za a ta da matattu
Domin su zauna har abada.
(AMSHI)
Allah zai yi abubuwan nan,
In muna ɗokin ladan nan.
-
2. A aljanna dukan dabbobi
Za su kasance da mutane.
Ƙaramin yaro zai bi da su,
Duk za su bi umurninsa.
Jin tsoro da kuma mutuwa,
Za su daina damun mutane.
(AMSHI)
Allah zai yi abubuwan nan,
In muna ɗokin ladan nan.
(Ka kuma duba Isha. 11:6-9; 35:5-7; Yoh. 11:24.)