Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 148

Jehobah Zai Cece Bayinsa

Jehobah Zai Cece Bayinsa

(2 Sama’ila 22:​1-8)

  1. 1. Jehobah ayyukanka sun nuna mini,

    Kai ne Mahaliccin

    sammai da duniya.

    Na san ka kusan cire duk masu yin

    ​—mugunta

    A duniyar nan fa.

    (AMSHI)

    Jehobah zai taimaki mai aminci.

    Allahnmu zai ceci dukan aminansa.

    Mu dogara da ikon Allah

    da cetonsa,

    Mu yabe shi, mu yi wa’azin

    bisharar nan.

  2. 2. Maƙiyana suna so su hallaka ni.

    “Jehobah Allahna,

    na dogara da kai.”

    Ka ji kukana da addu’o’ina,

    “Allahna

    Ka kāre ni sosai.”

    (AMSHI)

    Jehobah zai taimaki mai aminci.

    Allahnmu zai ceci dukan aminansa.

    Mu dogara da ikon Allah

    da cetonsa,

    Mu yabe shi, mu yi wa’azin

    bisharar nan.

  3. 3. Jehobah zai hallaka

    duk maƙiyansa.

    Dukan amintattu

    za su rera yabo.

    Duk abin da kake so za ka zama,

    Ubanmu,

    Za mu sami ceto.

    (AMSHI)

    Jehobah zai taimaki mai aminci.

    Allahnmu zai ceci dukan aminansa.

    Mu dogara da ikon Allah

    da cetonsa,

    Mu yabe shi, mu yi wa’azin

    bisharar nan.

(Ka kuma duba Zab. 18:​1, 2; 144:​1, 2.)