Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bayani ga Waɗanda Suka Halarci Taron

Bayani ga Waɗanda Suka Halarci Taron

TARO NA MUSAMMAN

MAKARANTAR MASU YAƊA BISHARAR MULKI Majagaban da ke tsakanin shekaru 23 da 65 da ke son faɗaɗa hidimarsu su halarci taron da za a yi don Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki a ranar Lahadi da safe. Za a sanar da wuri da kuma lokacin da za a yi wannan taron.

BAYANI GA WAƊANDA SUKA HALARCI TARON

BA DA KYAUTA An kashe kuɗaɗe da yawa don shirya wajen zama da sauti da kuma wasu abubuwa da suka sa muka ji daɗin wannan taron kuma hakan ya taimaka mana mu daɗa kusantar Jehobah. Gudummawar da za ka bayar za ta taimaka wajen biyan waɗannan kuɗaɗen, kuma za ta taimaka a aikin da ake yi a dukan duniya. An saka akwatuna da rubutu a kansu a wurare dabam-dabam a wannan majami’ar don ka iya ba da gudummawarka a sauƙaƙe. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana gode muku domin yadda kuke ba da gudummawa saboda aikin Mulkin Allah.

BAFTISMA Ya kamata waɗanda za su yi baftisma su zauna a wurin da aka keɓe musu kafin a soma jawabin baftisma a ranar Asabar da safe. Kowa ya zo da tawul nasa da kuma rigar da ta dace don yin baftisma.

HIDIMAR BA DA KAI Idan kana so ka taimaka da wasu ayyukan da ake yi a wannan taron, ka je Sashen Yaɗa Labarai da Ayyuka.

JINYAR GAGGAWA Ka tuna, wannan wurin jinyar GAGGAWA CE KAWAI.

MATATTARIN TSINTUWA A kai dukan kayayyaki da aka tsinta wannan sashen. Idan ka ɓatar da wani abu, ka je wannan sashen ka neme ta. A kai yaran da suka ɓace zuwa wannan sashen. Amma, wannan sashen ba wajen renon yara ba ne. Saboda haka, muna roƙonku ku kula da ’ya’yanku, kuma su riƙa kasancewa tare da ku.

TSARIN ZAMA Don Allah, ku nuna sanin yakamata. Ku tuna cewa iyalinku da waɗanda kuke tafiya tare a cikin mota da waɗanda kuke zama a gida ɗaya ko kuma waɗanda kuke nazari da su ne kawai za ku kama wa wurin zama. Kada ku ajiye abubuwa a kan kujerun da ba ku kama ba, domin wasu su sami wurin zama.

’YAN ATENDA An sanya ’yan atenda su taimake ku. Muna roƙonku ku bi umurnin da suka ba ku game da faka motoci da shiga da fita daga wurin taro da kama kujera da dai makamantansu.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce ta shirya wannan taron