Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bayani ga Waɗanda suka Halarci Taron

Bayani ga Waɗanda suka Halarci Taron

BAFTISMA Za a keɓe wurin zama kusa da dakalin magana don waɗanda za su yi baftisma. Ya kamata waɗanda za su yi baftisma su zauna a wurin da aka keɓe musu kafin a soma jawabin baftisma a ranar Asabar da safe. Kowa ya zo da tawul nasa da kuma rigar da ta dace don yin baftisma.

GUDUMMAWA An kashe kuɗaɗe da yawa don shirya wajen zama da sauti da kuma wasu abubuwa da suke sa mu ji daɗin taron yankinmu, kuma hakan ya taimaka mana mu daɗa kusantar Jehobah. Idan ka ba da gudummawar kuɗi, za ka taimaka wajen biyan waɗannan kuɗaɗen, kuma za ta taimaka wa hidimar da ake yi a dukan duniya. An saka akwatuna da rubutu a kansu a wurare dabam-dabam a majami’ar don ka sa gudummawar ka. Muna matuƙar godiya don gudummawar da ake bayarwa. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana alfahari da yadda kuke ba da gudummawa saboda hidimar Mulkin Allah ta sami ci gaba.

HIDIMAR BA DA KAI Idan kana so ka taimaka da wasu ayyukan da ake yi a wannan taron, ka je Sashen Samun Bayanai da Ayyuka.

JINYAR GAGGAWA Don Allah ka tuna cewa wannan wurin jinyar GAGGAWA CE KAWAI.

MATATTARIN TSINTUWA A kai dukan kayayyaki da aka tsinta Sashen Matattarin Tsintuwa. Idan ka ɓatar da wani abu, ka je wannan sashen ka neme ta. A kai yaran da suka ɓace zuwa wannan sashen. Domin a guji shiga mawuyacin hali, muna roƙonku ku kula da ’ya’yanku, kuma su riƙa kasancewa tare da ku.

TSARIN ZAMA Don Allah, ku nuna sanin yakamata. Ku tuna cewa waɗanda za ku iya kama musu wurin zama su ne, iyalinku, da waɗanda kuke tafiya tare a cikin mota, da waɗanda kuke zama a gida ɗaya, da kuma waɗanda kuke nazari da su. Kada ku ajiye abubuwa a kan kujerun da ba ku kama ba.

’YAN ATENDA Aikin da aka sa ’yan atenda shi ne, su taimaka muku. Don haka, muna roƙonku ku bi umurnin da suka ba ku game da faka motoci da shiga da fita daga wurin taro da kama kujera da dai makamantansu.

TARO NA MUSAMMAN

MAKARANTAR MASU YAƊA BISHARAR MULKI Majagaban da ke tsakanin shekaru 23 da 65 da suke so su faɗaɗa hidimarsu, su halarci taron da za a yi don Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki a ranar Lahadi da rana. Za a sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi wannan taron.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce ta shirya wannan taron