Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 02

Littafi Mai Tsarki Ya Ce Za Mu Ji Dadin Rayuwa

Littafi Mai Tsarki Ya Ce Za Mu Ji Dadin Rayuwa

Mutane da yawa suna da matsaloli da ke sa su baƙin ciki da kuma damuwa. Ka taɓa samun kanka a cikin irin wannan yanayin ne? Wataƙila kana baƙin ciki don rashin lafiya ko kuma wani naka ya rasu. Kana iya yin tunani, ‘Yanayina zai taɓa gyaruwa kuwa?’ An amsa wannan tambayar a Littafi Mai Tsarki.

1. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a nan gaba?

Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin da ya sa matsaloli suka cika duniya, kuma ya bayyana cewa matsalolin nan ba za su dawwama ba. Alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki za su sa mu ga cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba. (Karanta Irmiya 29:​11, 12.) Alkawuran nan sun tabbatar mana da cewa za mu iya yin farin ciki a yanzu, kuma a nan gaba za mu yi farin ciki har abada.

2. Waɗanne alkawura masu ban sha’awa ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

Littafi Mai Tsarki ya ce a nan gaba, ba za a riƙa “mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.) Matsaloli da suke sa mutane baƙin ciki a yau kamar talauci da rashin adalci da rashin lafiya da kuma mutuwa ba za su ƙara kasancewa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ’yan Adam za su ji daɗin rayuwa har abada a cikin Aljanna a duniya.

3. Ta yaya za ka tabbata cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru?

Mutane da yawa suna sa rai cewa abubuwa za su gyaru a duniya, amma ba su da tabbaci ko hakan zai taɓa faruwa ba. Babu shakka, alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su cika. ‘Bincika’ Nassosi sosai zai taimaka mana mu amince da alkawuran nan. (Ayyukan Manzanni 17:11) Yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, kai ne za ka tsai da shawara ko za ka amince da abin da ya ce zai faru a nan gaba ko a’a.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga wasu alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki da za su cika a nan gaba da kuma yadda Littafi Mai Tsarki yake taimaka wa mutane a yau.

4. Littafi Mai Tsarki ya ce za mu yi rayuwa har abada ba tare da matsaloli ba

Ga wasu alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wanne cikinsu ne ka fi so? Me ya sa ka ce haka?

Karanta kowane nassi da ke ƙasa, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin waɗannan nassosin za su amfane ka? Kana ganin za su taimaka wa iyalinka da abokanka?

Ka yi tunanin yin rayuwa a duniyar da

BABU WANDA ZAI . . .

KOWA ZAI . . .

  • riƙa baƙin ciki, ko tsufa ko kuma mutuwa.​—Ishaya 25:8.

  • ga an tā da wani nasa da ya rasu.—Yohanna 5:​28, 29.

  • yi rashin lafiya ko kuma ya naƙasa.​—Ishaya 33:24; 35:​5, 6.

  • kasance da ƙoshin lafiya da kuzari.​—Ayuba 33:25.

  • fuskanci rashin adalci.​—Ishaya 32:​16, 17.

  • samu isashen abinci da gida mai kyau da kuma aiki mai kyau.​—Zabura 72:16; Ishaya 65:​21, 22.

  • sha wahala a sakamakon yaƙi.​—Zabura 46:9.

  • kasance da kwanciyar hankali.​—Zabura 37:11.

  • riƙa baƙin ciki don abin da ya taɓa faruwa.​—Ishaya 65:17.

  • yi rayuwa har abada a yanayi mai kyau.​—Zabura 37:29.

5. Alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa mutane

Mutane da yawa suna baƙin ciki ko fushi don matsalolin da suke gani a ko’ina. Wasu suna ƙoƙari sosai don su kawo canji mai kyau a duniya. Bari mu ga yadda alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki da suke nuna cewa abubuwa za su gyaru suke taimaka wa mutane a yau. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, wane rashin adalci ne ya dami Rafika?

  • Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya taimaka mata, duk da cewa ba a daina rashin adalcin ba?

Alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu daina baƙin ciki kuma mu riƙa farin ciki duk da cewa muna fuskantar matsaloli. Ku karanta Karin Magana 17:22 da Romawa 12:​12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin abubuwa masu kyau da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a nan gaba za su iya taimaka maka a yau? Me ya sa ka ce hakan?

WASU SUN CE: “Alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki ba za su taɓa cika ba.”

  • Me ya sa ya dace ka yi bincike da kanka cewa alkawuran Littafi Mai Tsarki za su cika?

TAƘAITAWA

Littafi Mai Tsarki ya ce za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba. Kuma sanin hakan na inganta rayuwarmu yanzu.

Bita

  • Me ya sa mutane suke bukatar su ji game da waɗannan alkawuran?

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a nan gaba?

  • Ta yaya sanin abin da zai faru a nan gaba zai taimaka maka yanzu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda kasancewa da bege zai taimaka maka a lokaci da kake fama da matsaloli.

“Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Bege?” (Awake!, 22 ga Afrilu, 2004)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda albarkun da za mu samu a nan gaba za su taimaka wa waɗanda suke rashin lafiya mai tsanani.

“Jimrewa da Ciwo Mai Tsanani​—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimakawa Kuwa?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan kuma ku yi tunanin yadda ku da iyalinku za ku ji daɗin rayuwa a Aljanna a duniya.

Ka Ɗauka Muna Aljanna (3:37)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani da ke neman canji a duniya ya canja ra’ayinsa sa’ad da ya koyi game da albarkun da za mu more a nan gaba.

“Na Daina Ɗauka Cewa Zan Iya Gyara Yanayin Duniya” (Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 2013)