Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 04

Ka San Gaskiya Game da Allah Kuwa?

Ka San Gaskiya Game da Allah Kuwa?

’Yan Adam sun kwashi shekaru da yawa suna bauta wa alloli dabam-dabam. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce akwai Allah ɗaya ‘mai girma fiye da sauran alloli.’ (2 Tarihi 2:5) Me ya sa yake da girma sosai fiye da dukan alloli da mutane suke bauta wa? A wannan darasin, za ka koyi abubuwa da dama game da Allah.

1. Mene ne sunan Allah, kuma mene ne ya tabbatar mana da cewa yana so mu san sunansa?

Allah ya gaya mana sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya ce: Ni ne Jehobah, “sunana ke nan.” (Karanta Ishaya 42:​5, 8.) Masana da yawa sun ce sunan Ibranancin nan “Jehobah” yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Jehobah yana so mu san sunansa. (Fitowa 3:15) Mene ne ya tabbatar mana da hakan? Allah ya sa an rubuta sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki fiye da sau 7,000! a Sunan nan Jehobah, sunan Allah na gaskiya ne wanda shi kaɗai ne Allah a ‘can sama, da a nan duniya.’​—Maimaitawar Shari’a 4:39.

2. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Jehobah?

Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ne kaɗai Allah na gaskiya. Me ya sa? Da akwai dalilai da yawa. Na ɗaya, Jehobah ne mafi iko kuma shi kaɗai ne “Mafi Ɗaukaka a dukan duniya.” (Karanta Zabura 83:18.) Na biyu, shi ne “Maɗaukaki” domin shi kaɗai ne yake da ikon yin duk abin da ya ga dama. Na uku, shi ne ya “halicci kome da kome,” wato sama da duniya da dukan abubuwan da ke ciki. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:​8, 11) Na huɗu, Jehobah ne kaɗai bai da mafari ko kuma ƙarshe.​—Zabura 90:2.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi bambancin da ke tsakanin laƙaban Allah da kuma sunansa. Kuma za mu ga yadda Allah ya bayyana mana sunansa da kuma dalilin da ya sa ya yi hakan.

3. Allah yana da laƙabai da yawa, amma yana da suna ɗaya

Don ka san bambancin da ke tsakanin suna da kuma laƙabi, ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Wane bambanci ne ke tsakanin laƙabi kamar “Ubangiji” da kuma suna?

A cikin Littafi Mai Tsarki, an nuna cewa mutane suna bauta wa alloli da iyayengiji da yawa. Ku karanta Zabura 136:​1-3, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane ne “Allah wanda ya fi dukan alloli” da kuma “Ubangiji wanda ya fi dukan iyayengiji”?

4. Jehobah yana so ka san sunansa kuma ka yi amfani da sunan

Ta yaya ka san cewa Jehobah yana so ka san sunansa? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Kana ganin Jehobah yana so mutane su san sunansa? Me ya sa ka ce haka?

Jehobah yana so mutane su riƙa amfani da sunansa. Ku karanta Yowel 2:​32, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne muhimmancin yin amfani da sunan Allah, Jehobah?

  • Yaya kake ji sa’ad da wani ya tuna da sunanka kuma ya kira ka da sunan?

  • Yaya kake ganin Jehobah yake ji sa’ad da ka yi amfani da sunansa?

5. Jehobah yana so ka kusace shi

Wata ’yar ƙasar Kambodiya mai suna Soten ta ce sanin sunan Allah “ya sa ta farin ciki sosai.” Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, ta yaya koyan sunan Allah ya shafi Soten?

Abu na farko da kake koya kafin ka zama abokin mutum, shi ne sunansa. Ku karanta Yakub 4:8a, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Jehobah ya ce ka yi?

  • Ta yaya sanin sunan Allah da kuma yin amfani da shi zai taimaka maka ka kusace shi?

WASU SUN CE: “Tun da Allah ɗaya ne kawai, kana iya kiransa da kowane suna.”

  • Ka gaskata cewa sunan Allah Jehobah ne?

  • Ta yaya za ka bayyana cewa Allah yana so ka yi amfani da sunansa?

TAƘAITAWA

Jehobah ne sunan Allah na gaskiya. Yana so mu san sunan kuma mu yi amfani da shi don mu kusace shi.

Bita

  • Me ya sa Jehobah ya bambanta da sauran allolin da mutane suke bauta wa?

  • Me ya sa ya dace mu yi amfani da sunan Allah?

  • Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana so ka kusace shi?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilai biyar da suka tabbatar mana da cewa akwai Allah.

“Shin Akwai Allah?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilin da ya sa ya kamata mu gaskata cewa Allah bai da farko kuma bai da ƙarshe.

“Wane ne Ya Yi Allah?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2014)

Ku karanta talifin nan don ku koyi dalilin da ya sa ya dace mu yi amfani da sunan Allah ko da ba mu san ainihin yadda ake kiran sunan a dā ba.

“Wane ne Jehovah?” (Talifin jw.org)

Sunan da muke kiran Allah yana da muhimmanci ne? Ku karanta talifin nan don ku koyi abin da ya sa muka ce yana da suna guda kaɗai.

“Sunaye Nawa Ne Allah Yake da Su?” (Talifin jw.org)

a Don ka sami ƙarin bayani game da ma’anar sunan Allah da kuma dalilan da suka sa aka cire sunan a wasu juyin Littafi Mai Tsarki, ka duba Sashe na 1 na ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah.