Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 06

Ta Yaya Abubuwa Masu Rai Suka Soma Wanzuwa?

Ta Yaya Abubuwa Masu Rai Suka Soma Wanzuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ne ya “halicci kome da kome.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Ka gaskata da hakan? Wasu mutane sun ce babu wanda ya halicci abubuwa masu rai. Idan hakan gaskiya ne, wannan yana nufin cewa mun fara rayuwa ne haka kawai. Idan Jehobah ne ya halicci abubuwa masu rai, babu shakka yana da dalilin yin hakan. a Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da kuma dalilin da ya sa ya kamata mu gaskata da hakan.

1. Wane ne ya halicci sama da duniya?

Littafi Mai Tsarki ya ce: Da farko, Allah ya halicci “sama da duniya.” (Farawa 1:1) Yawancin masana kimiyya sun gaskata cewa an halicci duniya da taurari. Ta yaya Allah ya halicce su? Ya yi amfani da ‘ruhunsa’ mai tsarki don ya halicci duniya da kuma taurari.​—Farawa 1:2.

2. Me ya sa Allah ya halicci duniya?

Jehobah “bai halicci duniya ta zama wofi ba, ya yi ta domin a zauna a cikinta.” (Ishaya 45:​18) Ya halicci duniya a hanyar da ’yan Adam za su ji daɗin zama a cikinta har abada. (Karanta Ishaya 40:28; 42:5.) Masana kimiyya sun ce yadda aka halicci duniyar nan na da ban mamaki. A duniyar nan ne kaɗai abubuwa masu rai za su iya yin rayuwa.

3. Me ya bambanta ’yan Adam da dabobbi?

Jehobah ya fara halittar duniya, sai ya halicci shuke-shuke da dabbobi. Bayan haka, ‘Allah ya halicci mutum a kamanninsa.’ (Karanta Farawa 1:27.) Me ya bambanta ’yan Adam da sauran halittu a duniya? Tun da yake an halicce mu a kamannin Allah, muna iya nuna irin halayensa kamar ƙauna da adalci. Ya halicce mu don mu iya koyan yaruka, mu yi sha’awar abubuwa masu kyau kuma mu ji daɗin waƙoƙi. Kuma mun bambanta da dabbobi domin za mu iya bauta wa Mahaliccinmu.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga abubuwan da suka tabbatar mana da cewa an halicci abubuwa masu rai kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne. Za mu kuma ga abin da halaye masu kyau na ’yan Adam suka koya mana game da Allah.

4. An halicci abubuwa masu rai

Ana yabon ’yan Adam don abubuwa da suka kofa daga halittu. Amma wane ne ya kamata a yaba wa don halittun da suka kofa? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Waɗanne abubuwa da ’yan Adam suka ƙera ne suka kofa daga halittu?

Akwai wanda ya gina kowane gida. Amma waye ne ya tsara da kuma halicci kome da kome? Ku karanta Ibraniyawa 3:​4, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne abubuwa a halittu ne suke burge ka?

  • Ya dace mu gaskata cewa an halicci sama da duniya ne? Me ya sa ka ce haka?

Ka sani?

Za ka iya samun talifofi da kuma bidiyoyi game da wannan batun a jw.org ƙarƙashin sashen nan “Halittarsa Aka Yi?” da “Ra’ayoyi Game da Yadda Rayuwa ta Soma.”

“Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma Allah ne ya gina kome”

5. Zai dace mu gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da halitta

A littafin Farawa sura ta 1, Littafi Mai Tsarki ya faɗi yadda aka halicci duniya da kuma abubuwa masu rai da ke cikinta. Ka gaskata da wannan labarin, ko kuma kana ganin ƙarya ne? Ku kalli BIDIYON, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Shin Littafi Mai Tsarki ya ce an halicci duniya da kome da ke cikinta cikin kwanaki shida ne?

  • Kana ganin abin da labarin Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da halitta gaskiya ne? Me ya sa ka ce hakan?

Ku karanta Farawa 1:​1, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Masana kimiyya sun ce an halicci sama da kuma duniya. Ta yaya abin da suka faɗa ya jitu da abin da ka karanta a Littafi Mai Tsarki?

Wasu suna ganin cewa Allah ya fara halittar ƙwayoyin halittu, sai suka juya zuwa halittu masu rai. Ku karanta Farawa 1:​21, 25, 27, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Shin Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah ya fara halittar ƙwayoyin halittu ne, sai suka juya suka zama kifaye da dabbobi da kuma ’yan Adam? Ko kuma ya halicci abubuwa masu rai dabam-dabam bisa ga ‘irinsu’ ne?

6. ’Yan Adam halittu ne da babu kamarsu

Jehobah ne ya halicci ’yan Adam da dabbobi. Amma akwai abubuwan da suka bambanta ’yan Adam da dabbobi. Ku karanta Farawa 1:​26, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Da yake Allah ya halicce mu a kamanninsa, mene ne yadda muke nuna ƙauna da tausayi suke nunawa game da shi?

WASU SUN CE: “Labarin Littafi Mai Tsarki game da halitta ba gaskiya ba ne.”

  • Mene ne ra’ayinka? Me ya sa?

TAƘAITAWA

Jehobah ne ya halicci sama da duniya da kuma dukan abubuwa masu rai.

Bita

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya koyar game da yadda sama da duniya suka soma wanzuwa?

  • Shin Allah ya bar ƙwayoyin halittu dabam-dabam su juya zuwa abubuwa masu rai, ko kuwa ya halicci dukansu ne?

  • Mene ne ya sa ’yan Adam suka bambanta da dabbobi?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda halittu suka tabbatar da cewa akwai Mahalicci.

“Me Halittu Suke Koya Mana?” (Awake!, Satumba 2006)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mahaifi yake bayyana wa ɗansa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game halitta.

‘Jehobah . . . Ya Halicci Dukan Abu’ (2:37)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko koyarwar juyin halitta ta jitu da Littafi Mai Tsarki.

“Ta Juyin Halitta Ne Allah Ya Yi Abubuwa Masu Rai?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko ƙasusuwan dabbobi da aka tono da binciken da masana kimiyya suka yi sun nuna cewa an halicci rai ne ko kuma ya wanzu ne haka kawai.

Muhimman Tambayoyi Biyar Game da Yadda Rai Ya Soma (ƙasida)

a A darasi na 25 za mu tattauna dalilin da ya sa Allah ya halicci ’yan Adam.