Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 07

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah?

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah?

A ganinka wane irin Allah ne Jehobah? Kana ganin cewa yana da girma ainun, kuma ba za a iya kusantarsa ba? Kana ganin cewa yana da iko sosai amma ba shi da tausayi da ƙauna? Wane irin Allah ne Jehobah? Ta Kalmarsa, Jehobah ya bayyana halayensa da kuma yadda ya damu da kai.

1. Me ya sa ba ma iya ganin Allah?

‘Allah Ruhu ne.’ (Yohanna 4:24) Jehobah ba shi da irin jikin ’yan Adam. Shi Ruhu ne da ke zama a sama, wato wurin da ba ma iya gani.

2. Waɗanne halaye ne Jehobah yake da su?

Ba za mu iya ganin Jehobah ba, amma idan muka san shi, za mu ƙaunace shi domin yana da halaye masu kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: Jehobah “yana ƙaunar shari’ar gaskiya, ba zai ƙyale masu ƙaunarsa ba.” (Zabura 37:28) Jehobah “mai jinƙai ne, mai yawan tausayi” musamman ga waɗanda ke shan wahala. (Yakub 5:11) “Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa,” Jehobah “yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.” (Zabura 34:18) Ka san cewa muna iya sa Jehobah farin ciki ko kuma baƙin ciki? Mutumin da ya zaɓi yin abubuwan da ba su dace ba yana sa Jehobah baƙin ciki. (Zabura 78:​40, 41) Amma mutumin da ke yin abubuwan da suka dace yana sa shi farin ciki.​​—Karanta Karin Magana 27:11.

3. Ta yaya Jehobah yake nuna cewa yana ƙaunar mu?

Halin Jehobah na musamman shi ne ƙauna. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Jehobah ya nuna mana ƙaunarsa a Littafi Mai Tsarki da kuma a abubuwan da ya halitta. (Karanta Ayyukan Manzanni 14:17.) Alal misali, Jehobah ya halicce mu a hanyar da za mu iya ganin kaloli masu kyau da jin waƙoƙi masu daɗi da kuma cin abinci mai ɗanɗano. Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa sosai.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda Jehobah ya yi abubuwa masu ban-mamaki. Hakan zai sa ka ga yadda Jehobah ya nuna mana halayensa masu kyau.

4. Allah yana yin amfani da ruhu mai tsarki don ya cim ma nufinsa

Kamar yadda muke yin amfani da hannayenmu, haka ne Jehobah yake amfani da ruhu mai tsarki. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ruhu mai tsarki ba Allah ba ne, amma iko ne da Allah yake amfani da shi don ya cim ma nufinsa. Ku karanta Luka 11:13 da Ayyukan Manzanni 2:​17, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Allah zai ‘zuba’ ruhunsa mai tsarki a kan waɗanda suka roƙe shi. Don haka, kana ganin cewa ruhu mai tsarki Allah ne ko kuma ikon da Allah yake amfani da shi ne? Me ya sa ka ce hakan?

Jehobah yana yin amfani da ruhu mai tsarki don ya yi abubuwa masu ban-mamaki. Ku karanta Zabura 33:6 a da 2 Bitrus 1:​20, 21, sai ku tattauna tambayar nan:

  • A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki?

5. Jehobah yana da halaye masu kyau

Musa ya bauta wa Allah da aminci, duk da haka, yana so ya ƙara sanin Mahaliccinsa. Shi ya sa ya ce: “Ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka.” (Fitowa 33:13) Sai Jehobah ya gaya wa Musa wasu daga cikin halayensa. Ku karanta Fitowa 34:​4-6, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne halaye ne Jehobah ya nuna wa Musa?

  • Waɗanne cikin halayen Jehobah ne ka fi so?

6. Jehobah ya damu da mutane

Akwai lokacin da Ibraniyawa mutanen Jehobah ne kuma su bayi ne a ƙasar Masar. Yaya Jehobah ya ji sa’ad da mutanensa suke shan wahala? Ku kunna SAUTIN nan ku saurara, ko ku karanta Fitowa 3:​1-10. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Mene ne wannan labarin ya koya maka game da yadda Jehobah yake ji don wahalar da muke sha?​—Ka duba ayoyi na 7 da 8.

  • Kana ganin da gaske Jehobah yana so ya taimaka wa ’yan Adam, kuma zai iya in hakan? Me ya sa ka ce hakan?

7. Muna iya koyan halayen Jehobah daga halittunsa

Jehobah ya nuna halayensa ta abubuwan da ya halitta. Ku kalli BIDIYON nan. Ku karanta Romawa 1:​20, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Waɗanne halayen Jehobah ne kake gani a halittunsa?

WASU SUN CE: “Allah bai damu da ni ba.”

  • Mene ne ra’ayinka?

  • Me ya sa ka ce hakan?

TAƘAITAWA

Jehobah Ruhu ne kuma yana da halaye da yawa masu kyau, musamman ƙauna.

Bita

  • Me ya sa ba ma iya ganin Jehobah?

  • Mene ne ruhu mai tsarki?

  • Waɗanne halaye ne Jehobah yake da su?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku koyi game da halayen Jehobah huɗu masu muhimmanci.

“Yaya Halayen Allah Suke?” (Hasumiyar Tsaro Na 1 2019)

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwan da suka tabbatar mana da cewa Jehobah ba ya ko’ina.

“Shin Allah Yana Ko’ina Ne a Sama da Ƙasa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce ruhu mai tsarki hannun Allah ne.

“Mene ne Ruhu Mai Tsarki?” (Talifin jw.org)

Ya yi ma wani makahon wuya ya gaskata cewa Allah ya damu da shi. Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa ya canja ra’ayinsa.

“Yanzu na san zan iya taimaka wa mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2015)

a A Ibrananci, kalmar nan “numfashi” da ke Zabura 33:6 tana kuma nufin “ruhu mai tsarki.”