Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 09

Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah

Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah

Kana bukatar ja-goranci a rayuwa? Kana da tambayoyi masu muhimmanci da kake bukatar amsoshinsu? Kana bukatar ƙarfafawa? Za ka so ka kusaci Jehobah? Yin addu’a zai iya taimaka maka. Amma ta yaya ya kamata ka yi addu’a? Allah yana amsa dukan addu’o’i kuwa? Mene ne ya kamata ka yi don ya amsa addu’arka? Bari mu gani.

1. Ga waye ne za mu yi addu’a, kuma me za mu yi addu’a a kai?

Annabawa kamar su Nuhu da Ibrahim da kuma Dauda sun yi addu’a ga Jehobah. Alal misali, annabi Dauda ya yi addu’a cewa: Ka “ji addu’ata, ya Yahweh.” (Zabura 143:1) Idan muka yi addu’a ga Jehobah, muna ƙarfafa dangantakarmu da shi.

Muna iya yin addu’a a kan kowane batu. Amma idan muna so Allah ya amsa addu’o’inmu, wajibi ne su jitu da nufinsa. “Idan mun roƙi kome bisa ga nufinsa, [Allah] zai saurare mu.” (1 Yohanna 5:14) Yesu ya ba da misalin abubuwan da za mu iya yin addu’a a kansu. (Karanta Matiyu 6:​9-13.) Ban da yin addu’a game da matsalolinmu, wajibi ne mu gode wa Allah don abubuwan da ya yi mana kuma mu roƙe shi ya taimaka ma wasu mutane.

2. Ta yaya za mu yi addu’a?

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu gaya wa Allah dukan abin da ke ‘zuciyarmu.’ (Zabura 62:8) Don haka, ya kamata mu yi addu’a da zuciya ɗaya. Muna iya yin addu’a da babbar murya ko kuma a zuciyarmu a hanyar da ke nuna cewa muna daraja Jehobah. Muna iya yin addu’a a kowane lokaci da kuma a duk inda muke.

3. Ta yaya Allah yake amsa addu’o’inmu?

Yana yin hakan ta hanyoyi dabam-dabam. Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki don mu sami amsoshin tambayoyinmu. Karanta Kalmar Allah “yakan sa marar tunani ya sami hikima.” (Zabura 19:7; karanta Yakub 1:5.) Jehobah yana kwantar mana da hankali sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Kuma yana iya sa bayinsa su taimaka mana a lokacin da muke da bukata.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka yi addu’a da zuciya ɗaya, da kuma yadda yin addu’a za ta amfane ka.

4. Abubuwan da za mu yi don Allah ya amsa addu’armu

Waɗanne abubuwa ne za su sa Allah ya amsa addu’o’inka ko kuma ya ƙi yin hakan? Ku kalli BIDIYON nan.

Jehobah yana so mu riƙa addu’a a gare shi. Ku karanta Zabura 65:​2, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin Jehobah “mai jin addu’o’i” yana so ka yi addu’a a gare shi? Me ya sa ka ce hakan?

Muna bukatar mu riƙa bin ƙa’idodin Allah idan muna so ya amsa addu’o’inmu. Ku karanta Mika 3:4 da 1 Bitrus 3:​12, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya kamata mu yi don Jehobah ya amsa addu’o’inmu?

Idan ana yaƙi, waɗanda suke yaƙan juna suna roƙan Allah ya sa su yi nasara. Shin zai dace mu yi tunani cewa Allah zai amsa irin waɗannan addu’o’in?

5. Ya kamata mu yi addu’a daga zuciyarmu

An koya wa wasu mutane su riƙa maimaita addu’o’i ko kuma su yi addu’a a yaren da ba su sani ba. Amma yadda Allah yake so mu riƙa yin addu’a ke nan? Ku karanta Matiyu 6:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya za ka guji “dogon surutu” ko kuma maimaita abu ɗaya a addu’o’inka?

A kowace rana, kana iya yin tunani a kan abin da Allah ya yi maka kuma ka gode masa. Idan ka yi hakan a kowace rana har tsawon mako ɗaya, za ka ga cewa ka sami batutuwa bakwai da ka yi addu’a a kansu ba tare da ka maimaita ko ɗaya daga cikinsu ba.

Mahaifi nagari yana so yaronsa ya riƙa gaya masa abin da ke zuciyarsa. Hakazalika, Jehobah ma yana so mu riƙa gaya masa abin da ke zuciyarmu

6. Addu’a kyauta ce daga Allah

Ta yaya addu’a za ta taimaka mana sa’ad da muke cikin mawuyacin yanayi? Ku kalli BIDIYON nan.

Littafi Mai Tsarki ya ce addu’a za ta taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali. Ku karanta Filibiyawa 4:​6, 7, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ko da yake ba a kowane lokaci ba ne addu’a take magance matsalolinmu ba, ta yaya take taimaka mana?

  • Waɗanne abubuwa ne za ka so ka yi addu’a a kai?

Ka sani?

Kalmar nan “amin” tana nufin “ya kasance haka” ko kuma “hakika.” Tun a zamanin dā, ana amfani da kalmar nan “amin” don a kammala addu’a.​—1 Tarihi 16:36.

7. Ka nemi lokacin da za ka yi addu’a

A wasu lokuta, ayyuka suna iya yi mana yawa har mu manta yin addu’a. Shin yin addu’a yana da muhimmanci ga Yesu? Ku karanta Matiyu 14:23 da Markus 1:​35, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Yesu ya yi don ya sami lokacin yin addu’a?

  • A wane lokaci ne ya kamata ka yi addu’a?

WASU SUN CE: “Allah ba ya amsa addu’o’i da wuri.”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Yin addu’a da dukan zuciyarmu yana taimaka mana mu kusaci Jehobah, mu kasance da kwanciyar hankali kuma mu riƙa yin abin da Jehobah yake so.

Bita

  • Ga waye ne ya kamata mu yi addu’a?

  • Ta yaya ya kamata mu yi addu’a?

  • Ta yaya za mu amfana daga yin addu’a?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga amsoshin tambayoyin da mutane suke yawan yi game da addu’a.

“Abubuwa Bakwai da Ya Kamata Ka Sani Game da Addu’a” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2010)

Ku karanta talifin nan don ku koyi muhimmancin yin addu’a da kuma yadda mutum zai inganta addu’arsa.

“Mene ne Amfanin Yin Addu’a?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wanda ya kamata mu riƙa yin addu’a a gare shi.

“Shin Ya Kamata Na Yi Addu’a ga Waliyai?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga cewa za mu iya yin addu’a a ko’ina kuma a kowane lokaci.

Ka Yi Addu’a a Kowane Lokaci (1:22)