Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 12

Me Zai Taimaka Maka Ka Ci Gaba da Nazarin Kalmar Allah?

Me Zai Taimaka Maka Ka Ci Gaba da Nazarin Kalmar Allah?

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana da amfani sosai, amma ba a kowane lokaci ne yake da sauƙi ba. A wasu lokuta, kana iya ji kamar ba za ka iya ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Me ya sa ya kamata ka yi ƙoƙari ka ci gaba? Me zai taimaka maka ka nace ko da kana fuskantar matsaloli?

1. Me ya sa yin nazarin Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kalmar Allah tana da rai, tana da ƙarfin aiki kuma.” (Ibraniyawa 4:​12) Littafi Mai Tsarki yana da amfani domin yana bayyana ra’ayin Allah da kuma yadda yake ji game da kai. Zai taimaka maka ka san Jehobah kuma ka kasance da hikima da bege. Mafi muhimmanci ma, zai taimaka maka ka zama aminin Jehobah. Idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka fi yin farin ciki a rayuwa.

2. Me ya sa yake da muhimmanci ka san amfanin koyarwar Littafi Mai Tsarki?

Koyarwar Littafi Mai Tsarki tana kama da abubuwa masu daraja. Shi ya sa Kalmar Allah ta ce, mu ‘sayi gaskiya, kada mu sayar’ da ita. (Karin Magana 23:23) Idan muka san amfanin koyarwar Littafi Mai Tsarki, za mu ƙoƙarta mu ci gaba da nazari ko da muna fuskantar ƙalubale.​​—Karanta Karin Magana 2:​4, 5.

3. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ka ci gaba da yin nazari?

Da yake Jehobah ne Mahaliccinka da kuma Amininka, yana so ya taimaka maka ka koya game da shi. Zai sa ka ‘yi niyya, ka kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.’ (Karanta Filibiyawa 2:13.) Saboda haka, Jehobah zai taimaka maka a duk lokacin da kake bukatar ƙarfafawa don yin nazari ko kuma don ka yi abin da ka koya. Zai iya ba ka ƙarfin jimre matsaloli ko kuma tsanantawa. Ka riƙa roƙan Jehobah a kai a kai don ya taimaka maka ka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki.​—1 Tasalonikawa 5:17.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki ko da aiki ya maka yawa ko kuma wasu suna tsananta maka. Za mu ga yadda Jehobah zai taimaka maka ka ci gaba da nazari.

4. Ka sa nazarin Littafi Mai Tsarki ya fi muhimmanci a gare ka

A wasu lokuta, muna iya ganin cewa muna fama da ayyuka da yawa har ba mu da isashen lokacin yin nazari. Me zai iya taimaka maka? Ku karanta Filibiyawa 1:​10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne abubuwa ne kake ganin sun fi muhimmanci a rayuwa?

  • Ta yaya za ka sa yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya fi muhimmanci a gare ka?

  1. Idan ka fara zuba ƙasa a bokiti kuma ka yi ƙoƙari ka sa duwatsu a ciki, ba za ka sami wurin sa dukan duwatsun ba

  2. Amma idan ka fara sa duwatsu a bokitin, za ka samu wurin zuba ƙasar. Hakazalika, idan ka saka abubuwan da suka fi muhimmanci a kan gaba a rayuwarka, za ka yi su kuma ka sami lokacin yin wasu abubuwa

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana sa mu iya biyan bukatarmu ta sanin Allah da kuma bauta masa. Ku karanta Matiyu 4:​4, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya za mu amfana idan muka mai da nazarin Littafi Mai Tsarki abu mafi muhimmanci?

5. Ka ci gaba da yin nazari sa’ad da ake tsananta maka

A wasu lokuta, mutane za su yi ƙoƙari su sa ka daina nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka ga abin da ya faru da Francesco. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, mene ne abokan Francesco da mahaifiyarsa suka yi sa’ad da ya gaya musu abin da yake koya?

  • Wace albarka ce ya samu don bai karaya ba?

Ku karanta 2 Timoti 2:​24, 25, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Yaya ’yan gidanku da abokanka suke ji game da abubuwan da kake koya?

  • Kamar yadda aka nuna a waɗannan ayoyin, me za ka yi idan wani ba ya farin ciki don kana nazarin Littafi Mai Tsarki? Me ya sa za ka yi hakan?

6.Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka

Yayin da muke kusantar Jehobah, za mu daɗa so mu faranta masa rai. Duk da haka, zai iya yi mana wuya mu canja salon rayuwarmu don ya jitu da ƙa’idodinsa. Idan ka taɓa jin hakan, kada ka karaya. Jehobah zai taimaka maka. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, waɗanne canje-canje ne Jim ya yi don ya faranta ran Jehobah?

  • Mene ne ya burge ka game da shi?

Ku karanta Ibraniyawa 11:​6, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Jehobah zai yi wa “waɗanda suke nemansa” wato, waɗanda suke ƙoƙari su san shi kuma su faranta masa rai?

  • Yaya Jehobah yake ji sa’ad da ya ga kana iya ƙoƙarinka don ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?

WANI YANA IYA CEWA: “Me ya sa kake nazarin Littafi Mai Tsarki?”

  • Mene ne za ka ce?

TAƘAITAWA

Ko da yake bai da sauƙi, yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka ji daɗin rayuwa har abada. Ka ci gaba da dogara ga Jehobah, kuma zai albarkace ka.

Bita

  • Me ya sa koyarwar Littafi Mai Tsarki take da amfani?

  • Ta yaya za ka san abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa?

  • Me ya sa ya kamata ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwa huɗu da suka taimaka wa mutane da yawa su yi amfani da lokacinsu yadda ya dace.

“Yadda Za Ka Yi Amfani da Lokacinka da Kyau” (Awake!, Fabrairu 2014)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Jehobah ya taimaka wa wata mata da mijinta yake tsananta mata don tana bauta wa Allah.

Jehobah Yana Ƙarfafa Mu Don Mu Jure Wahala (5:05)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mutum ya amfana don matarsa ta ci gaba da bauta wa Jehobah.

Na Yi Bincike don In San Gaskiya (6:30)

A wasu lokuta, ana zargin Shaidun Jehobah cewa suna raba kan iyalai. Ku karanta talifin nan don ku ga ko hakan gaskiya ne.

“Shaidun Jehobah Suna Raba Kan Iyalai Ne ko Suna Sa Su Zauna Lafiya?” (Talifin jw.org)