Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 13

Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan Allah

Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan Allah

Idan Allah ƙauna ne, me ya sa addinan da suke da’awa cewa suna bin Allah suke yin munanan ayyuka? Waɗannan addinan ƙarya ne kuma furucinsu da ayyukansu suna ɓata sunan Allah. Ta yaya suke ɓata sunansa? Yaya Allah yake ji game da abin da suke yi? Kuma mene ne zai yi game da hakan?

1. Ta yaya addinan ƙarya suke ɓata sunan Allah ta koyarwarsu?

Addinan ƙarya “sun mai da gaskiyar Allah ta zama ƙarya.” (Romawa 1:25) Alal misali, yawancin addinai ba sa koya wa mabiyansu sunan Allah. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne a yi amfani da sunan Allah. (Romawa 10:​13, 14) Idan wani mugun abu ya faru, wasu malaman addinai sukan ce nufin Allah ne, amma hakan ba gaskiya ba ne. Allah ba ya jarrabtar kowa da mugunta. (Karanta Yakub 1:13.) Abin taƙaici, ƙaryace-ƙaryace da shugabannin addinai suke yi game da Allah, ya sa mutane ba sa ƙaunar Allah.

2. Ta yaya addinan ƙarya suke ɓata sunan Allah ta ayyukansu?

Shugabannin addinan ƙarya ba su damu da mutane kamar yadda Jehobah yake yi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce zunuban su “sun yi tuli har sama.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:5) Addinan ƙarya sun yi shekaru da yawa suna saka hannu a siyasa, da goyon bayan yaƙe-yaƙe da kuma amince a kashe mutane. Wasu shugabannin addinai suna so su zama masu arziki, saboda haka, sukan sa mabiyansu su ba su kuɗi. Abubuwan da suke yi sun nuna cewa ba su san Allah ba, balle ma su ce su wakilansa ne.​—Karanta 1 Yohanna 4:8.

3. Yaya Allah yake ji game da addinan ƙarya?

Idan abubuwan da addinan ƙarya suke yi suna ɓata maka rai, yaya kake ganin Jehobah yake ji? Jehobah yana ƙaunar mutane, amma yana fushi da shugabannin addinai da suke ɓata sunansa kuma suke wulaƙanta mabiyansu. Jehobah ya yi alkawari cewa zai halaka addinan ƙarya kuma ‘ba za a ƙara ganinsu ba.’ (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:21) Nan ba da daɗewa ba, Allah zai halaka dukan addinan ƙarya.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:8.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda Allah yake ji game da addinan ƙarya da abin da addinan ƙarya suka yi. Za mu kuma ga dalilan da suka sa bai kamata ka bar hakan ya hana ka koya game da Jehobah ba.

4. Ba dukan addinai ne Allah yake amincewa da su ba

Mutane da yawa suna ganin cewa addinai suna kama da hanyoyi dabam-dabam da mutum ke bi don ya san Allah. Amma hakan gaskiya ne kuwa? Ku karanta Matiyu 7:​13, 14, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hanyar samun rai?

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Shin Littafi Mai Tsarki ya ce akwai addinai da yawa da Allah ya amince da su?

5. Shugabannin addinan ƙarya ba sa nuna ƙauna kamar Allah

Shugabannin addinan ƙarya suna ɓata sunan Allah a hanyoyi da yawa. Hanya mafi muni da suke yin hakan ita ce ta wajen saka hannu a yaƙi. Don ku ga wani misali, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Mene ne coci da yawa suka yi a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu?

  • Yaya kake ganin matakin da suka ɗauka?

Ku karanta Yohanna 13:​34, 35 da 17:16. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Yaya kake ganin Jehobah yake ji a duk lokacin da addinai suka saka hannu a yaƙi?

  • Addinan ƙarya suna da hannu a munanan abubuwan da ke faruwa. Me ka taɓa ganin shugabannin addinan ƙarya suka yi da ya nuna cewa ba sa nuna ƙauna kamar Allah?

Shugabannin addinan ƙarya ba sa nuna ƙauna kamar Allah

6. Allah yana so ya taimaka wa mutane su bar addinan ƙarya

Ku karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​4, a sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yaya kake ji yanzu da ka san cewa Allah yana so ya taimaka wa mutane su bar addinin ƙarya?

7. Ka ci gaba da koya game da Allah na gaskiya

Ya kamata ne ka bar addinan ƙarya su canja ra’ayinka game da Allah? A ce wani yaro ya ƙi bin shawara mai kyau da mahaifinsa ya ba shi. Yaron ya bar gida kuma ya soma bin salon rayuwar da bai dace ba, amma mahaifinsa bai amince da salon rayuwarsa ba. Me ya sa ba zai dace mu ɗora wa mahaifin laifin taurin kai da ɗansa ya yi ba?

  • Zai dace ne mu ɗora wa Jehobah laifi kuma mu daina koya game da shi domin abubuwan da addinan ƙarya suke yi?

WASU SUN CE: “Ba na son jin wa’azi game da addini, domin munafurci ya yi yawa a dukan addinai.”

  • Kai ma ra’ayinka ke nan?

  • Me ya sa bai kamata mu bar ayyukan addinan ƙarya su hana mu bauta wa Jehobah ba?

TAƘAITAWA

Addinan ƙarya suna ɓata sunan Allah ta munanan abubuwan da suke yi da kuma koyarwarsu. Allah ya ce zai halaka addinan ƙarya.

Bita

  • Mene ne ra’ayinka game da abin da addinan ƙarya suke koyarwa da kuma abin da suka yi?

  • Mene ne ra’ayin Jehobah game da addinan ƙarya?

  • Mene ne Allah zai yi wa addinan ƙarya?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga hanyoyi biyu da yawancin addinai suke ɓata wa Allah rai.

“Allah Yana Amincewa da Dukan Addinai Ne?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa Jehobah yake so mu riƙa halartar taro.

“Shin Wajibi Ne Mutum Ya Kasance da Addini?” (Talifin jw.org)

Wani fada ya damu don abin da ke faruwa a cocinsu. Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa hakan bai hana shi koyan gaskiya game da Allah ba.

“Dalilin da Ya Sa Wani Fada Ya Bar Cocinsa” (Awake!, Fabrairu 2015)

Addinai sun yi shekaru da yawa suna koya wa mutane ƙarya cewa Allah bai damu da mu ba, kuma shi marar tausayi ne. Ku karanta talifin nan don ku koyi gaskiya game da ƙaryace-ƙaryace uku da suka yi.

“Ƙaryace-ƙaryace da Suka Sa Ake Gani Kamar Allah Ba Ya Ƙaunarmu” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2013)

a Don ka san dalilin da ya sa littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya kwatanta addinin ƙarya da mace mai suna Babila Mai Girma, ka duba Ƙarin Bayani na 1.