Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 19

Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?

Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?

Me ya sa Shaidun Jehobah suka gaskata cewa su Kiristoci ne na gaske? Daga ina ne muka sami abin da muka yi imani da shi? Ta yaya muka sami sunan nan Shaidun Jehobah? Ta yaya muke nuna cewa muna ƙaunar juna?

1. Daga ina ne Shaidun Jehobah suka samo abin da suka yi imani da shi?

Yesu ya ce: “Kalmar [Allah] kuwa ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Kamar Yesu, Shaidun Jehobah sun samo abin da suka yi imani da shi daga Kalmar Allah. Alal misali, ka yi la’akari da tarihinmu. A misalin shekara ta 1870, wasu mutane sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki don su fahimci ainihin abin da yake koyarwa. Sun yi imani da duk abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, ko da ya yi dabam da abin da ake koyarwa a coci. Sai suka soma koya wa mutane abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. a

2. Ta yaya muka sami sunan nan Shaidun Jehobah?

Jehobah yana kiran bayinsa shaidunsa domin suna koyar da gaskiya game da shi. (Ibraniyawa 11:4–12:1) Alal misali, a zamanin dā, Allah ya gaya wa mutanensa cewa: “Ku ne shaiduna.” (Karanta Ishaya 43:10.) An kira Yesu “amintacce mai shaida.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:5) Abin da ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah a shekara ta 1931 ke nan. Muna alfahari da wannan sunan.

3. Ta yaya Shaidun Jehobah suke nuna ƙauna kamar Yesu?

Yesu ya ƙaunaci almajiransa sosai, har sun zama kamar iyali a gare shi. (Karanta Markus 3:35.) Hakazalika, Shaidun Jehobah suna da haɗin kai kamar iyali a duk faɗin duniya. Shi ya sa muke kiran juna ’yan’uwa. (Filimon 1, 2) Muna biyayya da umurnin nan da ya ce: “Ku ƙaunaci ’yan’uwa masu bin Yesu.” (1 Bitrus 2:17) Shaidun Jehobah suna nuna wannan ƙaunar a hanyoyi da yawa. Alal misali, muna taimakon ’yan’uwanmu a faɗin duniya a lokacin da suke cikin matsala.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi tarihin Shaidun Jehobah da kuma wasu abubuwan da suka nuna cewa mu Kiristoci ne na gaske.

Kiristoci na gaske sun samo abin da suka yi imani da shi a Littafi Mai Tsarki kuma suna koya wa mutane

4. Mun samo abin da muka yi imani da shi daga Littafi Mai Tsarki

Jehobah ya annabta cewa za mu ƙara fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ku karanta Daniyel 12:​4, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne zai ‘ƙaru’ yayin da mutanen Allah suka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki?

Za ka koyi yadda ɗaliban Littafi Mai Tsarki, har da Charles Russell suka yi nazarin Kalmar Allah. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, ta yaya Charles Russell da sauran ɗaliban suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?

Ka sani?

A wasu lokuta, mukan canja wasu abubuwan da muka yi imani da su. Me ya sa? Kamar yadda hasken rana yake ɓullowa a hankali, haka ma Allah yake sa mu fahimci Kalmarsa a hankali. (Karanta Karin Magana 4:18.) Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai canja ba, mukan ɗan yi gyara a kan abubuwan da muka yi imani da su yayin da muka ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki.

5. Muna rayuwar da ta yi daidai da sunanmu

Me ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Me ya sa sunan nan Shaidun Jehobah ya dace?

Me ya sa Jehobah ya zaɓi mutane su zama shaidunsa? Domin su ne za su gaya wa mutane cewa shi ne Allah na gaskiya, da yake an yi ƙaryace-ƙaryace da yawa game da shi. Ka yi la’akari da biyu cikinsu.

Wasu addinai suna koya wa mabiyansu cewa Allah yana so su yi amfani da gumaka a bautarsu. Amma ku karanta Littafin Firistoci 26:​1, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Abin da suka faɗa gaskiya ne? Yaya Jehobah yake ji game da gumaka?

Wasu malaman addinai suna koyar cewa Yesu shi ne Allah. Amma, ku karanta Yohanna 20:​17, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Abin da suka faɗa gaskiya ne? Yesu shi ne Allah?

  • Yaya kake ji game da yadda Jehobah ya tura Shaidunsa su koyar da gaskiya game da shi da kuma Ɗansa?

6. Muna ƙaunar juna

Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata Kiristoci su kasance da haɗin kai kamar gaɓoɓin jikin ’yan Adam. Ku karanta 1 Korintiyawa 12:​25, 26, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya kamata Kiristoci na gaske su yi sa’ad da ’yan’uwansu suke shan wahala?

  • Mene ne ra’ayinka game da yadda Shaidun Jehobah suke ƙaunar juna?

Idan Shaidun Jehobah a wani wuri suna shan wahala, ’yan’uwansu a faɗin duniya suna taimaka musu nan da nan. Don ku ga wani misali, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya yadda Shaidun Jehobah suke tsara aikin ba da agaji ya nuna cewa suna ƙaunar juna?

Kiristoci na gaske suna taimaka wa waɗanda suke cikin matsala

WASU SUN CE: “Shaidun Jehobah sabon addini ne kawai.”

  • Tun wane lokaci ne Jehobah ya soma kiran bayinsa shaidu?

TAƘAITAWA

Shaidun Jehobah Kiristoci ne na gaske. Mu ’yan’uwa ne a faɗin duniya, mun samo abin da muka yi imani da shi a Littafi Mai Tsarki kuma muna koya wa mutane gaskiya game da Jehobah.

Bita

  • Me ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah?

  • Ta yaya muke nuna cewa mun damu da juna?

  • Kana ganin Shaidun Jehobah Kiristoci ne na gaske?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Shaidun Jehobah suka fallasa koyarwar ƙarya.

Bayin Allah Suna Ɗaukaka Sunansa (7:08)

Ku karanta talifin nan don ku sami amsoshin tambayoyi game da Shaidun Jehobah.

“Tambayoyin da Ake Yawan Yi Game da Shaidun Jehobah” (talifin jw.org)

Stephen ya tsani mutanen da launin fatarsu dabam ne da nasa, har ma yana kai musu hari. Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa ya canja ra’ayinsa sa’ad da ya soma cuɗanya da Shaidun Jehobah.

“Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Dā” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2015)

a Tun daga shekara ta 1879 ne bayin Jehobah suka soma wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro don su bayyana abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.