Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 24

Su Waye ne Mala’iku Kuma Wane Aiki Suke Yi?

Su Waye ne Mala’iku Kuma Wane Aiki Suke Yi?

Jehobah yana so mu san game da halittunsa na sama. Waɗannan halittun sun ƙunshi mala’iku da ake kira “’ya’yan Allah.” (Farawa 6:2; Ayuba 38:7) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da mala’iku? Me mala’iku suke yi? Dukan mala’iku ne suke da aminci?

1. Su wane ne mala’iku?

Jehobah ya halicci mala’iku kafin ya halicci duniya. Ba a ganin su kamar yadda ba a ganin Jehobah domin su ruhohi ne da suke sama. (Ibraniyawa 1:14) Akwai miliyoyin mala’iku, kuma kowannensu ya bambanta da juna. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:11) Suna “aikata nufin [Jehobah]” kuma suna “biyayya da maganarsa.” (Zabura 103:20) A wasu lokuta a zamanin dā, Jehobah yana tura mala’iku su sanar da saƙonsa, kuma su taimaka wa mutanensa. A yau, mala’iku suna yi wa mutanen Allah ja-goranci zuwa wurin mutanen da suke so su koya game da Jehobah.

2. Waye ne Shaiɗan da aljannunsa?

Wasu mala’iku ba su riƙe aminci ga Jehobah ba. Mala’ika na farko da ya yi tawaye shi ne ‘wanda ake ce da shi Mugun, ko kuma Shaiɗan, wanda ke ruɗin dukan duniya.’ (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9) Shaiɗan yana so ya mulki mutane da mala’iku, shi ya sa ya ruɗi Adamu da Hauwa’u har ma da wasu mala’iku don su yi tawaye da Jehobah. Mala’ikun da suka yi tawayen nan ne ake kiran aljannu. Jehobah ya kore su daga sama zuwa duniya, kuma a nan gaba za a halaka su.​—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​9, 12.

3. Ta yaya Shaiɗan da aljannunsa suke ƙoƙarin ruɗin mu?

Shaiɗan da aljannunsa suna ruɗin mutane ta wurin amfani da sihiri, wato neman yin magana da ruhohi. Alal misali, wasu suna zuwa wurin masanan taurari, ko masu dūba, ko masu tsafi, ko bokaye, ko masu camfi ko kuma ’yan bori don su taimaka musu. Wasu kuma sukan je wurin boka don neman magani. Ana yaudarar mutane cewa za su iya yin magana da matattu. Amma Jehobah ya gargaɗe mu cewa: “Kada ku tafi wurin mai haɗa kai da ruhohin matattu ko ku nemi shawara daga boka.” (Littafin Firistoci 19:31) Ya ba mu wannan umurnin don ya kāre mu daga Shaiɗan da aljannunsa. Su maƙiyan Allah ne, kuma suna so su yi mana lahani.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abubuwa masu kyau da mala’iku suke yi, da haɗarin saka hannu a sihiri da kuma yadda za mu kāre kanmu daga Shaiɗan da aljannunsa.

4. Mala’iku suna taimaka wa mutane su koya game da Jehobah

Mala’iku ba sa wa mutane wa’azi da kansu. Maimakon haka, suna yi wa mutanen Allah ja-goranci zuwa wurin mutanen da suke so su koya game da Allah. Ku karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​6, 7, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa muke bukatar taimakon mala’iku sa’ad da muke yin wa’azi?

  • Yadda mala’iku suke taimaka mana mu je wurin mutane da suke so su ji wa’azi yana ƙarfafa ka? Me ya sa?

5. Ka guji sihiri

Shaiɗan da aljannunsa maƙiyan Jehobah ne kuma maƙiyanmu ne. Ku karanta Luka 9:​38-42, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne aljannu suke yi wa mutane?

Mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji duk wani abu da zai haɗa mu da aljannu. Ku karanta Maimaitawar Shari’a 18:​10-12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • A waɗanne hanyoyi ne aljannu suke ƙoƙari su yaudare mu kuma su yi magana da mu? A waɗanne hanyoyi ne aljannu suke yaudarar mutane a wurin da kake zama?

  • Kana ganin ya dace da Jehobah ya hana mu saka hannu a sihiri? Me ya sa?

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin nan.

  • Kana ganin layar da Palesa ta ɗaura wa ’yarta tana da lahani? Me ya sa?

  • Mene ne Palesa take bukatar ta yi don ta kāre kanta daga aljannu?

Kiristoci na gaske ba sa barin aljannu su rinjaye su. Ku karanta Ayyukan Manzanni 19:19 da 1 Korintiyawa 10:​21, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu halaka kome da muke da su da ke da alaƙa da sihiri?

6. Za ka iya yin nasara a kan Shaiɗan da aljannunsa

Shaiɗan ne shugaban aljannu. Amma Mika’ilu ne shugaban mala’iku. Mika’ilu wani suna ne da ake kiran Yesu. Wane irin iko ne Mika’ilu yake da shi? Ku karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​7-9, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waye ne ya fi iko? Mika’ilu da mala’ikunsa ne ko kuma Shaiɗan da aljannunsa?

  • Kana ganin mabiyan Yesu suna bukatar su ji tsoron Shaiɗan da aljannunsa ne?

Za ka iya yin nasara a kan Shaiɗan da aljannunsa. Ku karanta Yakub 4:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya za ka kāre kanka daga Shaiɗan da aljannunsa?

WASU SUN CE: “Yin wasannin bidiyo ko kallon fina-finai da ke nuna sihiri ba laifi ba ne. Ai wasa ne kawai.”

  • Me ya sa wannan ra’ayin bai dace ba?

TAƘAITAWA

Mala’iku masu aminci suna taimaka mana. Shaiɗan da aljannunsa maƙiyan Jehobah ne, suna yin amfani da sihiri wajen ruɗin mutane.

Bita

  • Ta yaya mala’iku suke taimaka wa mutane su koya game da Jehobah?

  • Waye ne Shaiɗan da aljannunsa?

  • Me ya sa ya kamata mu guji sihiri?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku san dalilin da ya sa aka ce Yesu ne Mika’ilu shugaban mala’iku.

“Wane ne Mika’ilu, Shugaban Mala’iku?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya nuna cewa Shaiɗan yana wanzuwa da gaske, ba wani mugun hali ko ra’ayin da mutane suke da shi ba ne.

“Shin Iblis Yana Wanzuwa da Gaske?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wata mata ta sami ’yanci daga hannun aljannu.

“Daga Baya Rayuwarta ta Kasance da Ma’ana” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 1993, English)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda Shaiɗan yake amfani da sihiri don ya ruɗi mutane.

“Gaskiya Game da Sihiri, Bokanci, da Kuma Maita” (Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa? sashe na 5)