Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 27

Ta Yaya Mutuwar Yesu Za Ta Cece Mu?

Ta Yaya Mutuwar Yesu Za Ta Cece Mu?

Mu masu zunubi ne, muna shan wahala kuma muna mutuwa domin Adamu da Hauwa’u sun yi wa Allah rashin biyayya. a Amma muna da mafita. Jehobah ya aiko Ɗansa, Yesu Kristi zuwa duniya ya mutu don ya kuɓutar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ya mutu don ya fanshe mu. Fansa kuɗi ne da ake biya don a yi belin wani. Yesu ya ba da kamiltaccen ransa don ya fanshe mu. (Karanta Matiyu 20:28.) Yesu yana da damar yin rayuwa har abada a duniya, amma ya ba da ransa domin mu sami duk abin da Adamu da Hauwa’u suka rasa. Yesu ya kuma nuna cewa shi da Jehobah suna ƙaunar mu sosai. Wannan darasin zai taimaka mana mu ƙara nuna godiya don mutuwar Yesu.

1. Yaya za mu amfana daga mutuwar Yesu a yau?

Domin mu masu zunubi ne, muna yin abubuwa da yawa da suke ɓata wa Jehobah rai. Amma za mu iya zama aminan Jehobah idan muka tuba daga zunubanmu kuma muka roƙi Jehobah ta sunan Yesu Kristi ya gafarta mana. Ƙari ga haka, za mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu maimaita zunubin. (1 Yohanna 2:1) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Almasihu . . . mai adalci ya mutu saboda mu marasa adalci, ya mutu sau ɗaya ne tak ba ƙari domin ya kai mu ga Allah.”​—1 Bitrus 3:18.

2. Ta yaya za mu amfana daga mutuwar Yesu a nan gaba?

Jehobah ya aiko Yesu ya ba da ransa ‘domin dukan wanda ya ba da gaskiya ga [Yesu] kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.’ (Yohanna 3:16) Da yake Yesu ya ba da ransa, nan ba da daɗawa ba, Jehobah zai kawar da dukan munanan abubuwan da suke faruwa a yau don rashin biyayyar Adamu. Hakan yana nufin cewa idan mun ba da gaskiya ga hadayar Yesu, za mu sami zarafin yin rayuwa a aljanna a duniya har abada!​—Ishaya 65:​21-23.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abin da ya sa Yesu ya ba da ransa domin mu da kuma yadda za ka amfana daga hadayarsa.

3. Mutuwar Yesu ta kuɓutar da mu daga zunubi da mutuwa

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Wane zarafi ne Adamu ya rasa sa’ad da ya yi rashin biyayya?

Ku karanta Romawa 5:​12, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya zunubin Adamu ya shafe ka?

Ku karanta Yohanna 3:​16, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa Jehobah ya aiko da Ɗansa zuwa duniya?

  1. Da farko, Adamu kamiltaccen mutum ne, amma ya yi rashin biyayya ga Allah. Don haka, dukan mutane sun zama masu zunubi kuma suna mutuwa

  2. Yesu kamiltaccen mutum ne da ya yi biyayya ga Allah. Don haka dukan mutane suna da damar zama kamiltattu kuma su yi rayuwa har abada

4. Dukan mutane za su iya amfana daga mutuwar Yesu

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya mutuwar mutum ɗaya za ta amfani dukan mutane?

Ku karanta 1 Timoti 2:​5, 6, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Adamu kamiltacce ne da farko, amma domin ya yi zunubi, dukan mutane sun zama masu zunubi kuma suna mutuwa. Yesu kamiltacce ne kamar yadda Adamu yake da farko. Amma mene ne Yesu ya yi?

5. Fansa kyauta ce daga Jehobah

Aminan Jehobah suna ɗaukan fansa a matsayin kyauta da Jehobah ya ba su. Alal misali, ku karanta Galatiyawa 2:​20, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa yana ɗaukan fansa a matsayin kyauta?

Sa’ad da Adamu ya yi zunubi, shi da dukan ’ya’yansa sun soma mutuwa. Amma Jehobah ya aiko Ɗansa don mu sami damar jin daɗin rayuwa har abada a nan gaba.

Sa’ad da kake karanta ayoyin nan, ka yi tunanin yadda Jehobah ya ji a lokacin da Ɗansa yake shan azaba. Ku karanta Yohanna 19:1-7, 16-18, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yaya kake ji don abin da Jehobah da Yesu suka yi maka?

WANI YANA IYA CEWA: “Ta yaya mutum ɗaya zai mutu don dukan mutane?”

  • Me za ka gaya masa?

TAƘAITAWA

Mutuwar Yesu ce ta sa Jehobah yake gafarta mana zunubanmu kuma mu sami rai na har abada.

Bita

  • Me ya sa Yesu ya mutu?

  • Ta yaya hadayar Yesu ta ’yantar da mu daga zunubi da mutuwa?

  • Ta yaya za ka amfana daga mutuwar Yesu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa ake kiran kamiltaccen ran Yesu abin fansa.

“A Wace Hanya ce Hadayar Yesu Ta Zama ‘Abin Fansar Mutane da Yawa’?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da muke bukatar mu yi don mu sami ceto.

“Ta Yaya Yesu Ya Cece Mu?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko Jehobah zai iya gafarta zunubai masu tsanani.

“Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Mayu, 2013)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda mutuwar Yesu ta taimaka wa wani mutum ya canja halinsa.

“Na Daina Zalunci” (Talifin jw.org)

a Zunubi ba yin abu marar kyau ba ne kawai. Amma yana kuma nufin cewa muna yawan son yin abubuwa da ba su dace ba don mu ’ya’yan Adamu ne.