Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 30

Matattu Za Su Sake Rayuwa!

Matattu Za Su Sake Rayuwa!

Idan wani namu ya mutu, muna kuka da baƙin ciki sosai. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira mutuwa abokiyar gāba. (1 Korintiyawa 15:26) A Darasi na 27, ka koyi cewa Jehobah zai yi nasara a kan abokiyar gābar nan. Amma me zai faru da mutanen da sun riga sun mutu? A wannan darasin, za ka ga alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai ta da biliyoyin mutanen da suka mutu don su more rayuwa har abada. Amma hakan zai yiwu kuwa? Za a ta da su don su yi rayuwa a sama ne ko a duniya?

1. Mene ne Jehobah yake so ya yi ma wani namu da ya mutu?

Jehobah yana so ya ta da ’yan’uwa da abokanmu da suka mutu. Wani mutum mai aminci da ake kira Ayuba ya kasance da tabbaci cewa Allah ba zai manta da shi ba sa’ad da ya mutu. Ya ce: “Za ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka [daga kabari].”​—Karanta Ayuba 14:​13-15.

2. Ta yaya muka sani cewa za a ta da matattu?

Sa’ad da Yesu yake duniya, Allah ya ba shi ikon ta da mutane daga mutuwa. Yesu ya ta da wata ’yar shekara 12 da kuma ɗan wata gwauruwa. (Markus 5:​41, 42; Luka 7:​12-15) Daga baya, Li’azaru abokin Yesu ya mutu. Duk da cewa Li’azaru ya yi kwana huɗu da mutuwa kuma an binne shi, Yesu ya ta da shi. Bayan Yesu ya yi addu’a, sai ya ce: “Li’azaru, fito!” Sai “mutumin da ya mutu ɗin ya fito” da rai! (Yohanna 11:​43, 44) Babu shakka, danginsa da abokansa sun yi farin ciki sosai!

3. Wane bege ne waɗanda suka mutu suke da shi?

A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya yi alkawari cewa: “Za a tā da matattu.” (Ayyukan Manzanni 24:15) A lokacin da Yesu yake duniya, mutanen da ya ta da daga mutuwa ba su je sama ba. (Yohanna 3:13) Ya ta da su ne a duniya kuma sun yi farin ciki. Hakazalika nan ba da daɗewa ba, Yesu zai ta da biliyoyin mutane don su rayu har abada a aljanna a duniya. Yesu ya ce za a ta da dukan waɗanda Allah ya tuna da su, ko da babu ɗan Adam da ya tuna cewa sun taɓa wanzuwa.​​—Yohanna 5:​28, 29.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga tabbaci daga Littafi Mai Tsarki cewa Yesu zai ta da matattu a nan gaba. Za mu kuma ga yadda tashin matattu zai ta’azantar da mu, ya kuma sa mu kasance da bege.

4. Yesu ya nuna cewa zai iya ta da matattu

Za mu koyi abin da Yesu ya yi wa abokinsa Li’azaru. Ku karanta Yohanna 11:​14, 38-44, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya muka san cewa Li’azaru ya mutu da gaske?​—Ka duba aya ta 39.

  • Da a ce sama ne Li’azaru ya tafi bayan ya mutu, kana ganin Yesu zai dawo da shi wannan duniyar?

Ku kalli BIDIYON nan.

5. Za a ta da mutane da yawa!

Ku karanta Zabura 37:​29, sai ku tattauna tambayar nan:

  • A ina ne biliyoyin mutanen da za a ta da daga mutuwa za su zauna?

Yesu zai ta da mutane da yawa har ma da waɗanda ba su bauta wa Jehobah ba. Ku karanta Ayyukan Manzanni 24:​15, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane ne za ka so ka ga an ta da daga mutuwa?

Ka yi la’akari da wannan: Yesu zai ta da matattu kamar yadda mahaifi yake ta da ɗansa daga barci

6. Begen tashin matattu zai ta’azantar da kai

Labarin ’yar Yayirus ya ta’azantar da mutane da yawa da wani nasu ya rasu kuma ya ƙarfafa su. Ka karanta labarin a Luka 8:​40-42, 49-56.

Kafin Yesu ya ta da ’yar Yayirus, ya gaya wa mahaifinta cewa: “Kada ka ji tsoro, ka dai ba da gaskiya.” (Ka duba aya ta 50.) Ta yaya begen tashin matattu zai taimaka maka . . .

  • a lokacin da wani naka ya rasu?

  • sa’ad da ranka yake cikin haɗari?

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya begen tashin matattu ya ta’azantar da iyayen Phelicity kuma ya ƙarfafa su?

WASU SUN CE: “A sama ne za a ta da matattu, ba a duniya ba.”

  • Mene ne ra’ayinka?

  • Wane nassi ne za ka yi amfani da shi don ka nuna cewa za a ta da matattu?

TAƘAITAWA

A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ta da biliyoyin mutane da suka mutu. Yana so su sake rayuwa, kuma ya ba wa Yesu ikon ta da su.

Bita

  • Yaya Jehobah da Yesu suke ji game da tashin matattu?

  • A ina ne biliyoyin mutanen da za a ta da daga mutuwa za su zauna, a sama ne ko a duniya? Me ya sa ka ce hakan?

  • Me ya tabbatar maka da cewa wani naka da ya rasu zai sake rayuwa?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga wasu abubuwan da mutum zai iya yi sa’ad da wani nasa ya rasu.

“Taimako don Waɗanda Suke Makoki” (Awake! Na 3 2018, English)

Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa wanda wani nasa ya rasu ne? Ku kalli bidiyon nan don ku ga amsar.

Me Zai Taimaka Idan Wani Naka Ya Rasu? (5:06)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda yaran da wani nasu ya rasu za su sami ta’aziyya.

Mutuwar Yesu (2:07)

Akwai waɗanda za a ta da su zuwa sama kuwa? Su waye ne ba za a ta da su ba? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Tashin Matattu?” (Talifin jw.org)