Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 32

Mulkin Allah Yana Sarauta!

Mulkin Allah Yana Sarauta!

Mulkin Allah ya soma sarauta a sama a shekara ta 1914. Kuma a lokacin ne aka shiga kwanaki na ƙarshe na sarautar ’yan Adam. Ta yaya muka san hakan? Za mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta, da yanayin da ake ciki a duniya da kuma halayen mutane tun shekara ta 1914.

1. Me annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna?

Littafin Daniyel ya nuna cewa Mulkin Allah zai soma sarauta a ƙarshen “lokaci bakwai.” (Daniyel 4:​16, 17) Shekaru da yawa bayan haka, Yesu ya kira wannan lokacin “zamanan al’ummai,” kuma ya ce ƙarshen bai zo ba tukun. (Luka 21:​24, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Kamar yadda za mu gani, wannan lokaci bakwai ya ƙare a shekara ta 1914.

2. Ta yaya abubuwa suka canja tun shekara ta 1914?

Almajiran Yesu sun tambaye shi cewa: “Mece ce alamar dawowarka da kuma ta ƙarshen zamani?” (Matiyu 24:3) Yesu ya annabta abubuwa da yawa da za su faru bayan ya soma sarauta a sama a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Wasu daga cikin abubuwan sun ƙunshi yaƙi da yunwa da kuma girgizar ƙasa. (Karanta Matiyu 24:7.) Littafi Mai Tsarki ya kuma annabta cewa halayen mutane “a kwanakin ƙarshe” za su jawo “sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:​1-5) Abubuwan nan kuwa sun daɗa muni tun shekara ta 1914.

3. Me ya sa mugunta ta ƙaru bayan da aka kafa Mulkin Allah?

Jim kaɗan bayan da Yesu ya zama Sarkin Mulkin Allah, ya yaƙi Shaiɗan da aljannunsa a sama. Shaiɗan bai yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki ya ce an jefo shi “duniya tare da mala’ikunsa.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​9, 10, 12) Shaiɗan yana cike da fushi domin ya san za a halaka shi. Saboda haka, ya sa wahala ta cika duka duniya. Shi ya sa duniya take cike da mugunta! Amma Mulkin Allah zai kawar da dukan matsalolin nan.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda muka san cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914 da kuma yadda za mu amfana.

4. An yi annabci a Littafi Mai Tsarki game da shekara ta 1914

Allah ya sa Sarkin Babila ta dā, mai suna Nebukadnezzar ya yi mafarki. A mafarkin, Allah ya nuna masa abubuwan da za su faru a nan gaba. Mafarkin da kuma ma’anarsa da Daniyel ya faɗa, ya nuna cewa mafarkin game da mulkin Nebukadnezzar ne da kuma Mulkin Allah.​—Ku karanta Daniyel 4:17. a

Ku karanta Daniyel 4:​20-26, sai ku yi amfani da akwatin “Alaƙa Tsakanin Mafarkin Bishiya da Mulkin Allah” don ku amsa tambayoyi na gaba:

  • (A) Mene ne Nebukadnezzar ya gani a mafarkinsa?​—Ka duba ayoyi na 20 da 21.

  • (B) Mene ne zai faru da bishiyar? ​—Ka duba aya ta 23.

  • (C) Mene ne zai faru a ƙarshen “lokaci bakwai”?​—Ka duba aya ta 26.

Alaƙar da Ke Tsakanin Mafarkin Bishiya da Mulkin Allah

ANNABCIN (Daniyel 4:​20-36)

Sarauta

(A) Wata babbar bishiya

An dakatar da sarautar

(B) Za “a sare” bishiyar, sai a bar ta na “tsawon lokaci bakwai”

An ci gaba da sarauta

(C) “Za a tabbatar maka da mulkinka”

Yadda annabcin ya cika da farko . . .

  • (D) Waye ne bishiyar take wakilta?​—Ka duba aya ta 22.

  • (E) Yaushe ne aka dakatar da sarautarsa?​—Ku karanta Daniyel 4:​29-33.

  • (F) Mene ne ya faru da Nebukadnezzar a ƙarshen “lokaci bakwai”?​—Ku karanta Daniyel 4:​34-36.

YADDA ANNABCIN YA CIKA DA FARKO

Sarauta

(D) Nebukadnezzar, Sarkin Babila

An dakatar da sarautar

(E) Bayan shekara ta 606 K.H.Y., b Nebukadnezzar ya sami taɓin hankali kuma ya kasa yin sarauta har tsawon shekaru bakwai

An ci gaba da sarauta

(F) Nebukadnezzar ya dawo cikin hankalinsa kuma ya ci gaba da sarauta

Yadda annabcin ya cika a karo na biyu . . .

  • (G) Waye ne bishiyar take wakilta? ​—Ku karanta 1 Tarihi 29:23.

  • (H) Yaushe ne aka dakatar da sarautarsu? Ta yaya muka san cewa an dakatar da sarautar har lokacin da Yesu yake duniya?​—Ku karanta Luka 21:24.

  • (I) Yaushe ne aka ci gaba da sarautar kuma a ina ne ya faru?

YADDA ANNABCIN YA CIKA A KARO NA BIYU

Sarauta

(G) Sarakunan Isra’ilawa da suke wakiltar sarautar Allah

An dakatar da sarautar

(H) An halaka Urushalima, kuma hakan ya sa an dakatar da sarautar sarakunan Isra’ilawa har tsawon shekaru 2,520

An ci gaba da sarauta

(I) Yesu ya soma sarauta a sama a matsayin Sarkin Mulkin Allah

Shekaru nawa ne wannan lokaci bakwai?

Wasu ayoyi a Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana mu fahimci wasu ayoyi. Alal misali, littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya ce lokatai uku da rabi, kwanaki 1,260 ne. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​6, 14) Don haka, kafin a sami lokaci bakwai sai an ninka adadin sau biyu, sai ya zama kwanaki 2,520. A wasu lokuta a Littafi Mai Tsarki, kwana ɗaya yana nufin shekara ɗaya. (Ezekiyel 4:6) Saboda haka, lokaci bakwai da ke littafin Daniyel yana wakiltar shekaru 2,520.

5. Duniya ta canja sosai tun daga shekara ta 1914

Yesu ya annabta yadda duniya za ta zama bayan ya zama Sarki. Ku karanta Luka 21:​9-11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wanne cikin waɗannan yanayoyin ne ka taɓa gani ko ji?

Manzo Bulus ya bayyana irin halayen da mutane za su kasance da su a kwanakin ƙarshe na sarautar ’yan Adam. Ku karanta 2 Timoti 3:​1-5, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mutane suna nuna irin waɗannan halayen a yau kuwa?

6. Abin da Mulkin Allah zai sa mu yi

Ku karanta Matiyu 24:​3, 14, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wane aiki na musamman ne ya nuna cewa Mulkin Allah ya soma sarauta?

  • Ta yaya za ka iya yin wannan aikin?

Mulkin Allah yana sarauta yanzu, kuma ranar da za ta mallaki dukan duniya ta kusa. Ku karanta Ibraniyawa 10:​24, 25, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya kamata kowannenmu ya yi da yake “ranar nan tana matsowa kusa”?

Me za ka yi idan ka san abin da zai taimaka wa mutum ko kuma ya ceci rayuwarsa?

WANI YANA IYA CEWA: “Me ya sa Shaidun Jehobah suke yawan magana game da shekara ta 1914?”

  • Me za ka ce masa?

TAƘAITAWA

Annabci da ke Littafi Mai Tsarki, da abubuwa da suke faruwa a duniya sun nuna cewa Mulkin Allah yana sarauta yanzu. Za mu nuna cewa mun gaskata da wannan ta wurin halartar taron Shaidun Jehobah.

Bita

  • Mene ne ya faru a ƙarshen lokaci bakwai da aka ambata a littafin Daniyel?

  • Me ya tabbatar maka cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914?

  • Ta yaya za ka nuna ka gaskata cewa Mulkin Allah yana sarauta yanzu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da marubutan tarihi da kuma wasu suka faɗa game da canje-canjen da suka faru a duniya tun shekara ta 1914.

“Lokacin da Ɗabi’un ’Yan Adam Suka Taɓarɓare” (Awake!, Afrilu 2007, English)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda annabci da ke Matiyu 24:14 ya taimaki wani mutum.

“Ina Son Kwallon Baseball Fiye da Kome!” (Hasumiyar Tsaro Na 3 2017)

 Ta yaya muka san cewa annabci da ke littafin Daniyel sura 4 yana magana ne game da Mulkin Allah? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta? (Sashe na 1)” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2014)

Me ya nuna cewa “lokaci bakwai” da ke Daniyel sura 4 ya ƙare a shekara ta 1914? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta? (Sashe na 2)” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2015)

a Ku duba  talifofi biyu na ƙarshe da ke sashen Ka Bincika a wannan darasin.

b Alamar nan K.H.Y. yana nufin kafin haihuwar Yesu, B.H.Y. kuma yana nufin bayan haihuwar Yesu.