Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 33

Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Mulkin Allah ya riga ya soma sarauta a sama. Nan ba da daɗewa ba, zai soma sarauta bisa duniya kuma ya sa duniya ta zama wuri mai kyau. Bari mu tattauna abubuwa masu kyau da Mulkin Allah zai yi.

1. Ta yaya Mulkin Allah zai kawo salama da adalci a duniya?

Yesu, Sarkin Mulkin Allah zai halaka mugayen mutane da gwamnatin ’yan Adam a yaƙin Armageddon. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba da daɗewa ba mugaye za su ɓace.” (Zabura 37:10) A lokacin da Mulkin Allah zai soma sarauta a duniya, Yesu zai tabbatar da cewa an sami salama da adalci a ko’ina a duniya.​—Karanta Ishaya 11:4.

2. Yaya rayuwa za ta kasance a lokacin da za a yi nufin Allah a duniya?

A Mulkin Allah, “masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.” (Zabura 37:29) Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a duniyar da dukan mutane za su zama masu adalci, masu ƙaunar Jehobah da kuma juna! Babu wanda zai yi rashin lafiya kuma mutane za su rayu har abada.

3. Mene ne Mulkin Allah zai yi bayan an halaka mugaye?

Bayan an halaka mugaye, Yesu zai yi sarauta na shekara 1,000. A lokacin, shi da mutane 144,000 za su yi sarauta, kuma su taimaka wa mutane su zama marasa zunubi. A ƙarshen shekara 1,000, duniya za ta zama aljanna, cike da mutane masu farin ciki domin suna yin biyayya ga Jehobah. Sa’an nan Yesu zai mayar da Mulkin ga Ubansa, Jehobah. Hakan zai sa a ‘kiyaye sunan [Jehobah] da tsarki.’ (Matiyu 6:​9, 10) A lokacin, mutane za su ga cewa Jehobah Sarki ne da ya damu da mutanen da yake mulki a kansu. Sa’an nan, Jehobah zai halaka Shaiɗan da aljannunsa da dukan mutane da suka yi tawaye da sarautarsa. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:​7-10) Canjin da Mulkin Allah zai kawo zai kasance har abada.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi dalilin da ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Mulkin Allah zai cika dukan alkawuran da aka yi a Littafi Mai Tsarki game da nan gaba.

4. Mulkin Allah zai halaka gwamnatin ’yan Adam

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wani yana da iko a kan waɗansu, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don ya kawo ƙarshen dukan rashin adalci a duniya.

Ku karanta Daniyel 2:44 da 2 Tasalonikawa 1:​6-8, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Jehobah da Ɗansa Yesu, za su yi wa gwamnatin ’yan Adam da masu goyon bayansu?

  • Ta yaya abin da ka koya game da Jehobah da Yesu suka tabbatar maka cewa matakin da za su ɗauka zai amfane mu?

5. Yesu ne Sarki mafi dacewa

A matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah, Yesu zai taimaka wa mutane a duniya a hanyoyi da yawa. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga cewa Yesu yana so ya taimaka wa mutane kuma Jehobah ya ba shi ikon yin hakan.

Abubuwan da Yesu ya yi sa’ad da yake duniya, soma taɓi ne na abin da Mulkin Allah zai yi mana. Wanne cikin albarkun da aka ambata kake ɗokin ganin ya faru? Ku karanta nassosin nan da suka yi magana game da albarkun.

DA YESU YAKE DUNIYA, YA . . .

DAGA SAMA, YESU ZAI . . .

  • dakatar da iska mai ƙarfi.​—Markus 4:​36-41.

  • gyara dukan abubuwan da aka lalata a duniya.​—Ishaya 35:​1, 2.

  • ciyar da dubban mutane ta hanyar mu’ujiza.​—Matiyu 14:​17-21.

  • kawar da yunwa a duniya.​—Zabura 72:16.

  • warkar da mutane da yawa da suke rashin lafiya.​—Luka 18:​35-43.

  • tabbatar da cewa dukan mutane sun sami ƙoshin lafiya.​—Ishaya 33:24.

  • ta da mutane daga mutuwa.​—Luka 8:​49-55.

  • sa a daina mutuwa.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4.

6. Mulkin Allah zai kawo albarku a nan gaba

Mulkin Allah zai cika nufin Jehobah ga ’yan Adam. Mutane za su yi rayuwa har abada a aljanna a duniya. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga yadda Jehobah zai yi amfani da Ɗansa Yesu don ya cika nufinsa.

Ku karanta Zabura 145:​16, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yaya kake ji yanzu da ka san cewa Jehobah zai “biya bukatar zuciyarka”?

WASU SUN CE: “Idan an sami shugaba ɗan Adam nagari, zai iya magance matsalolinmu.”

  • Waɗanne matsaloli ne Mulkin Allah zai magance da gwamnatocin ’yan Adam ba za su iya yi ba?

TAƘAITAWA

Mulkin Allah zai cika nufin Jehobah. Zai sa duniya ta zama aljanna inda mutane za su bauta wa Jehobah har abada.

Bita

  • Ta yaya Mulkin Allah zai kiyaye sunan Jehobah?

  • Me ya sa za mu gaskata cewa Mulkin Allah zai cika dukan alkawuran da aka yi a Littafi Mai Tsarki?

  • A cikin dukan abubuwan da Mulkin Allah zai yi, wane ne kake ɗokin ganin ya faru?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da Armageddon yake nufi.

“Mene ne Yakin Armageddon?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da zai faru a lokacin da Yesu yake sarauta na shekaru 1,000 da kuma abin da zai faru bayan hakan.

“Mene Ne Zai Faru a Ranar Shari’a?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2012)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda iyalai za su iya tunanin yadda rayuwa a aljanna za ta kasance.

Ka Ga Kanka a Aljanna (1:50)

Ku karanta labarin Raudel Rodríguez don ku ga yadda wani ɗan adawa da gwamnati ya sami amsoshin tambayoyin da yake da su.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2012)