Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 35

Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau

Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau

Dukanmu mukan tsai da shawarwari. Waɗannan shawarwarin za su iya sa mu yi nasara ko su sa mu shiga matsala, kuma za su iya shafan dangantakarmu da Jehobah. Alal misali, muna bukatar mu yanke shawara game da inda za mu zauna da irin sana’ar da za mu yi. Kuma mu da kanmu ne za mu yanke shawara ko za mu yi aure ko a’a. Idan mun yanke shawarwari masu kyau, za mu yi farin ciki kuma mu faranta ran Jehobah.

1. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau?

Kafin ka tsai da shawara, ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka bincika Littafi Mai Tsarki don ka san ra’ayinsa game da batun. (Karanta Karin Magana 2:​3-6.) A wasu lokuta, Jehobah yana ba da umurni dalla-dalla game da wani batu. Idan haka ne, yin biyayya ga umurnin zai sa mu yi nasara.

Amma me za mu yi idan babu umurni a cikin Littafi Mai Tsarki game da wani batu? Jehobah zai taimaka maka ka san ‘hanyar da za ka bi.’ (Ishaya 48:17) Ta yaya zai yi hakan? Akwai ƙa’idodin da za su taimaka maka. Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna sa mu san ra’ayin Jehobah. Sau da yawa, mukan san ra’ayin Allah a kan wani batu sa’ad da muka karanta wani labari a Littafi Mai Tsarki. Idan muka san ra’ayin Jehobah, za mu iya yanke shawarwarin da za su faranta ransa.

2. Waɗanne abubuwa ne za mu yi tunani a kai kafin mu yanke shawara?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” (Karin Magana 14:15) Hakan yana nufin cewa kafin mu yanke shawara, ya kamata mu yi tunani sosai a kan abin da muke so mu yi. Yayin da kake tunani a kan abin da za ka yi, ka tambayi kanka: ‘Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne zan iya yin amfani da su a wannan yanayin? Wane zaɓi ne zai sa in sami kwanciyar hankali? Shawarar da zan yanke za ta sa mutane farin ciki ne ko baƙin ciki? Mafi muhimmanci ma, za ta sa Jehobah farin ciki ne?’​—Maimaitawar Shari’a 32:29.

Jehobah yana da ikon gaya mana abin da ya dace da abin da bai dace ba. Idan muka san dokokinsa da ƙa’idodinsa kuma muka yanke shawarar bin su, zuciyarmu ba za ta dame mu ba. Zuciyarmu ce take gaya mana ko abin da muka yi ya dace ko a’a. (Romawa 2:​14, 15) Idan zuciyarmu tana aiki da kyau, za ta taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma zuciyarmu suke taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau.

3. Ka bi shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki

Ta yaya ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana sa’ad da muke yanke shawarwari? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Mene ne Jehobah ya ba mu damar yi?

  • Me ya sa Jehobah ya ba mu damar yanke shawarwari?

  • Mene ne Jehobah ya ba mu don mu iya yanke shawarwari masu kyau?

Don ku ga wata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki, ku karanta Afisawa 5:​15, 16. Sa’an nan ku tattauna yadda za “ku yi amfani da kowane zarafi” don ku . . .

  • riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum.

  • zama miji ko mata ko iyaye ko ɗa ko kuma ’yar kirki.

  • riƙa halartan taron ikilisiya.

4. Ka sa zuciyarka ta riƙa taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau

Idan an ba da umurni a kan wani batu a cikin Littafi Mai Tsarki, zai yi mana sauƙi mu tsai da shawarar da ta dace. Amma me za mu yi idan babu umurni kai tsaye? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, mene ne ’yar’uwar ta yi don ta riƙa tsai da shawarwari da za su faranta ran Jehobah?

Me ya sa ya kamata mu riƙa tsai da shawarwari da kanmu? Ku karanta Ibraniyawa 5:​14, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Idan mutane suka gaya mana abin da za mu yi, hakan ya fi yanke shawara da kanmu sauƙi, amma me ya kamata mu yi ƙoƙarin yi da kanmu?

  • Waɗanne tanadodi ne za su horar da zuciyarka don ka tsai da shawarwari masu kyau?

Kamar yadda taswira take taimaka mana mu san hanyar da za mu bi, haka ma zuciyarmu za ta taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau

5. Ka riƙa daraja ra’ayin mutane

Mutane suna da ra’ayi dabam-dabam, hakan yana sa su tsai da shawarwari dabam-dabam. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ra’ayin mutane? Ka yi la’akari da waɗannan misalai biyu:

Misali na 1: Wata ’yar’uwa mai son yin kwalliya ta koma ikilisiyar da mata da yawa ba sa son yin kwalliya.

Ku karanta Romawa 15:1 da 1 Korintiyawa 10:​23, 24, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kamar yadda ayoyin nan suka nuna, wace shawara ce ’yar’uwar za ta iya yankewa? Mene ne za ka yi sa’ad da kake tare da wani da ba ya son abin da kake gani ba laifi ba ne?

Misali na 2: Wani ɗan’uwa ya san cewa Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya ba, amma ya yanke shawara cewa ba zai riƙa sha ba. Sai wata rana, aka gayyace shi zuwa liyafa kuma ya ga ’yan’uwa suna shan giya.

Ku karanta Mai-Wa’azi 7:16 da Romawa 14:​1, 10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kamar yadda ayoyin nan suka nuna, wace shawara ce ɗan’wan zai iya yankewa? Mene ne za ka yi sa’ad da ka ga wani yana yin abin da ba ka so?

 Abubuwan da za su taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau.

1. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka san abin da za ka yi.​—Yakub 1:5.

2. Ka bincika Littafi Mai Tsarki da kuma Littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki don ka sami ƙa’idodin da za su taimaka maka. Za ka kuma iya tattaunawa da Kiristoci da suka manyanta.

3. Ka yi la’akari da yadda shawararka za ta shafe ka da kuma wasu.

WASU SUN CE: “Kana da ’yancin yin duk abin da ka ga dama. Ba ruwan kowa da kai.”

  • Me ya sa ya kamata ka damu da yadda Allah da kuma mutane suke ji?

TAƘAITAWA

Za mu tsai da shawarwari masu kyau idan muka san ra’ayin Jehobah a kan wani batu. Kuma zai dace mu yi tunani sosai don mu ga ko ayyukanmu za su taimaka wa mutane ko za su yi musu lahani.

Bita

  • Ta yaya za ka tsai da shawarwarin da za su faranta ran Jehobah?

  • Ta yaya za ka sa zuciyarka ta riƙa taimaka maka ka yanke shawarwari masu kyau?

  • Ta yaya za mu riƙa daraja ra’ayin mutane?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda za ku iya yanke shawarwarin da za su sa ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah.

“Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Afrilu, 2011)

Ku kalli bidiyon nan don ku daɗa fahimtar irin shawarwarin da Jehobah yake ba mu.

Jehobah Yana Yi wa Mutanensa Ja-goranci (9:50)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abubuwan da suka taimaka ma wani mutum ya tsai da shawara mai kyau a mawuyacin yanayi.

Jehobah Yana Yi wa Bayinsa Albarka (5:46)

Ku karanta talifin nan don ku koyi yadda mutum zai riƙa yin abin da Jehobah yake so ko da babu doka kai tsaye game da batun.

“Wajibi Ne A Kafa Doka a kan Kowane Batu?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Disamba, 2003)