Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 39

Ra’ayin Allah Game da Jini

Ra’ayin Allah Game da Jini

Jini yana da muhimmanci. Idan ba mu da jini, ba za mu rayu ba. Allah ne ya halicce mu, saboda haka, shi ne ya kamata ya gaya mana yadda za a yi amfani da jini. Mene ne ya ce game da jini? Zai dace mu ci jini ko a saka mana a jikinmu? Kuma ta yaya za ka tsai da shawarwari masu kyau game da wannan batun?

1. Mene ne ra’ayin Jehobah game da jini?

Jehobah ya gaya wa bayinsa a zamanin dā cewa: “Rai na kowace halitta yana cikin jininta ne.” (Littafin Firistoci 17:14) Jehobah yana ɗaukan jini a matsayin rai. Tun da yake rai kyauta ce daga Allah, jini ma yana da muhimmanci a gare shi.

2. Wace hanyar yin amfani da jini ne Allah ya haramta?

Kafin a kafa ikilisiyar Kirista, Jehobah ya umurci bayinsa kada su ci jini. (Karanta Farawa 9:4 da Littafin Firistoci 17:10.) Shekaru da yawa bayan haka, ya sake ba wa Kiristoci wannan dokar cewa, “ku kiyaye kanku daga . . . jini.”​—Karanta Ayyukan Manzanni 15:​28, 29.

Mene ne kiyaye kanmu daga jini yake nufi? Idan likita ya gaya maka cewa ka kiyaye kanka daga giya, hakan yana nufin cewa kada ka sha giya. Amma kana ganin za ka iya cin abinci da aka sa giya a ciki ko kuma a yi maka allurarsa? Ba shakka, ba za ka yi hakan ba. Hakazalika, yadda Allah ya ce mu kiyaye kanmu daga jini yana nufin ba za mu sha jini ko mu ci mushe ba. Kuma ba za mu ci abinci da aka dafa da jini ba.

Idan likita ne ya ce a saka maka jini kuma fa? Wasu hanyoyin yin jinya ba su jitu da dokar Allah ba. Hakan ya ƙunshi karɓan jinin, ko kuma sassa huɗu na jini, wato jajaye da fararen ƙwayoyin jini da kamewar jini da kuma ruwan jini, (red cells, white cells, platelets, da plasma). Akwai wasu jinya da ba su saɓa wa dokar Allah kai tsaye ba. Alal misali, wasu suna amfani da sinadarai da aka samo daga cikin sassa huɗu na jini. A wasu lokuta kuma akan yi amfani da jinin mutumin da ake wa jinya. Sa’ad da muke tunanin irin jinyar da za mu yi, wajibi ne kowannenmu ya tsai da shawara da kansa. a​—Galatiyawa 6:5.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu tsai da shawara a kan irin jinyar da za a yi mana.

3. Ka zaɓi irin jinyar da za ta faranta ran Jehobah

Ta yaya za ka tsai da shawarwari game da jinyar da ta jitu da ra’ayin Allah? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna muhimmancin bin shawarwarin da ke gaba.

  • Ka yi addu’a don ka sami hikima.​—Yakub 1:5.

  • Ka bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da yadda za ka yi amfani da su.​—Karin Magana 13:16.

  • Ka yi tambaya a yankinku don ka san irin jinyar da za ka iya yi.

  • Ka yanke shawara a kan irin jinyar da ba za ka so ka yi ba.

  • Ka tabbata cewa shawarar da ka yanke ba za ta dame ka daga baya ba.​—Ayyukan Manzanni 24:16. b

  • Zai dace ka san cewa idan ya zo ga batun zaɓan jinyar da za a yi maka, ba wanda zai gaya maka shawarar da za ka yanke, ko da matarka ce ko mijinki ko dattijo ko kuma malaminka.​—Romawa 14:12.

  • Ka rubuta shawarar da ka yanke.

4. Shaidun Jehobah suna son yin jinya mafi kyau

Zai yiwu mutum ya bi dokar Allah game da jini, kuma a yi masa jinya mai kyau ba tare da an sa masa jini ba. Ku kalli BIDIYON nan.

Ku karanta Titus 3:​2, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa za mu riƙa yi wa likitoci magana yadda zai nuna cewa muna daraja su?

Waɗanda ba ma karɓa

Waɗanda kai za ka tsai da shawara

A. Ruwan jini

Sinadarai daga ruwan jini

B. Fararen ƙwayoyin jini.

Sinadarai daga fararen ƙwayoyin jini

C. Kamewar jini.

Sinadarai daga kamewar jini

D. Jajayen ƙwayoyin jini.

Sinadarai daga jajayen ƙwayoyin jini

 5. Idan za a yi amfani da sinadaran jini

Sassa huɗu na jini su ne: Jajayen ƙwayoyin jini da fararen ƙwayoyin jini da kamewar jini da kuma ruwan jini. Waɗannan sassa na jini na ɗauke da sinadarai da yawa daga jini. c Ana amfani da wasu sinadarai daga jini wajen yin magungunan da ke kāre mu daga wasu cututtuka ko kuma dakatar da zubar jini.

Idan ya zo ga batun sinadarai daga jini, kowane Kirista ne zai yanke shawarar abin da zai yi. Wasu za su iya ƙin jinyar da ta ƙunshi yin amfani da sinadarai daga jini. Wasu kuma za su iya ganin kamar ba laifi ba ne.

Kafin ka yanke shawara, ka tambayi kanka:

  • Ta yaya zan bayyana wa likita dalilin da ya sa na ƙi ko na amince da jinyar da ta ƙunshi wasu sinadarai daga jini?

WANI YANA IYA CEWA: “Karɓan jini ba laifi ba ne!”

  • Mene ne ra’ayinka?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so mu riƙa ganin jini a matsayin abu mai tsarki.

Bita

  • Me ya sa Jehobah yake ganin jini a matsayin abu mai tsarki?

  • Ta yaya muka san cewa dokar Allah da ta ce mu kiyaye kanmu daga jini, ta nuna cewa karɓan jini a asibiti ma bai dace ba?

  • Ta yaya za ka yanke shawarwari masu kyau game da yin jinya da ta shafi batun jini?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da mutum zai yi kafin ya yanke shawara game da jinyar da ake so a yi amfani da jininsa.

“Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Oktoba, 2000)

Ku karanta talifin nan don ku san abin da mutum zai yi kafin ya yanke shawara ko zai amince da sinadarai daga jini.

“Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Yuni, 2004)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa wani likita ya gaskata cewa ra’ayin Jehobah game da jini ya dace.

“Na Amince da Ra’ayin Allah Game da Jini” (Awake!, 8 ga Disamba, 2003)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda dattawa da ke hidima a Kwamitin Hulɗa da Asibitoci suke taimaka wa ’yan’uwansu.

Jehobah Yana Ƙarfafa Marasa Lafiya (10:23)

a Ka duba Darasi na 35, “Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau.”

b Ka duba  batu na 5 mai jigo, “Idan Za A Yi Amfani da Sinadaran Jini,” da Ƙarin Bayani na 3, “Hanyoyin Jinya da Suka Shafi Batun Jini.”

c Wasu likitoci suna ganin sassa huɗu na jini su ne sinadarai daga jini. Saboda haka, ya kamata ka bayyana wa likitanka da kyau cewa ba za ka karɓi jini dungum ba, wato jajayen ƙwayoyin jini ko fararen ƙwayoyin jini ko kamewar jini ko kuma ruwan jini.