Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 40

Ta Yaya Za Mu Zama Masu Tsabta a Gaban Allah?

Ta Yaya Za Mu Zama Masu Tsabta a Gaban Allah?

Idan mahaifiya tana shirya yaronta don ya je makaranta, za ta yi masa wanka ta kuma saka masa kaya masu kyau da kuma tsabta. Hakan zai sa yaron ya kasance da ƙoshin lafiya kuma mutane za su ga cewa iyayensa suna kula da shi. Hakazalika, Jehobah yana so jikinmu da halinmu da tunaninmu da kuma furucin su kasance da tsabta. Idan muka kasance da tsabta, za mu amfana kuma hakan zai ɗaukaka Jehobah.

1. Ta yaya za mu zama masu tsabta?

Jehobah ya umurce mu cewa: “Ku zama da tsarki.” (1 Bitrus 1:16) Don mu zama masu tsarki, wajibi ne mu kasance da tsabta da kuma halin kirki. Za mu zama masu tsabta idan muna wanka a kai a kai da wanke rigunanmu da kuma tsabtace gidanmu da motarmu da dai sauransu. Ban da haka, zai dace mu taimaka wajen tsabtace Majami’ar Mulki. Idan mun kasance da tsabta, za mu ɗaukaka Jehobah.​​—2 Korintiyawa 6:​3, 4.

2. Don mu kasance da tsabta, waɗanne halaye ne ya kamata mu guje wa?

Littafi Mai Tsarki ya umurce mu, “mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu ya ƙazantu.” (2 Korintiyawa 7:1) Hakan yana nufin cewa mu guji duk wani abin da zai ƙazamtar da jikinmu ko kuma ya gurɓata zuciyarmu. Ya kamata tunaninmu ya ɗaukaka Jehobah. Saboda haka, mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji tunanin banza. (Zabura 104:34) Kuma wajibi ne mu guji maganganun banza.​​—Karanta Kolosiyawa 3:8.

Mene ne kuma za mu yi don mu kasance da tsabta? Akwai wasu abubuwa da za su iya yi wa jikinmu lahani. Saboda haka, ya kamata mu guji wasu abubuwa kamar su shan taba da miyagun ƙwayoyi. Yin hakan zai sa mu kasance da ƙoshin lafiya kuma zai nuna muna daraja ran da Allah ya ba mu. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu guji halayen da za su sa mu zama marasa tsabta, kamar yin wasa da al’aurarmu da kuma kallon hotuna ko bidiyon batsa. (Zabura 119:37; Afisawa 5:5) Zai iya yin wuya mu daina waɗannan halayen. Amma Jehobah zai iya taimaka mana mu yi nasara.​—Karanta Ishaya 41:13.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda kasancewa da tsabta yake ɗaukaka Jehobah kuma mu ga yadda mutum zai iya daina halayen banza.

3. Kasancewa da tsabta yana ɗaukaka Jehobah

Idan mun karanta dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa, za mu fahimci ra’ayinsa game da tsabta. Ku karanta Fitowa 19:10 da 30:17-19, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya waɗannan ayoyin suka nuna ra’ayin Jehobah game da tsabta?

  • Mene ne za ka yi a kai a kai don ka kasance da tsabta?

Ko da yake kasancewa da tsabta na bukatar sa ƙwazo da kuma lokaci sosai, muna iya yin hakan a duk inda muke ko da mu masu arziki ne ko talakawa. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Idan muna da tsabta kuma mun shirya kayan wa’azinmu da kyau, ta yaya hakan zai sa mutane su ɗaukaka Jehobah?

4. Yadda za ka daina halayen banza

Jehobah zai iya taimaka mana mu daina kowane irin halin banza

Idan ka taɓa shan taba ko ƙwayoyi, za ka san cewa bai da sauƙi mutum ya bar wannan halin. Me zai taimaka maka? Ka yi tunanin yadda wannan halin yake shafanka. Ku karanta Matiyu 22:​37-39, sai ku tattauna yadda shan taba ko miyagun ƙwayoyi ke shafan . . .

  • dangantakar mutum da Jehobah.

  • iyalin mutum da kuma wasu.

Ka shirya yadda za ka daina wani halin da bai dace ba. a Ku kalli BIDIYON nan.

Ku Karanta Filibiyawa 4:​13, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya yin addu’a a kai a kai da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro zai taimaka wa mutum ya daina wani hali marar kyau?

5. Yadda mutum zai guji tunani da kuma ayyuka da ba su dace ba

Ku karanta Kolosiyawa 3:​5, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya muka san cewa Jehobah ba ya so mu riƙa kallon batsa, ko aika saƙonnin batsa ko hotunan tsiraici ko bidiyo ko kuma yin wasa da al’aura?

  • Kana ganin ya dace da Jehobah ya ce mu guji halayen banza? Me ya sa?

Ka koyi yadda za ka daina tunanin banza. Ku kalli BIDIYON nan.

Yesu ya yi amfani da misali don ya nuna matakin da za mu ɗauka don mu kasance da halin kirki. Ku karanta Matiyu 5:​29, 30, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ko da yake Yesu ba ya nufin cewa mu ji wa kanmu rauni amma ya nuna cewa ya kamata mu ɗauki mataki. Wane mataki ne mutum zai iya ɗauka don ya guji tunanin banza? b

Jehobah yana alfahari da kai idan kana ƙoƙarin daina halin banza. Ku karanta Zabura 103:​13, 14, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Idan kana fama da halin banza, ta yaya wannan nassin ya ƙarfafa ka ka ci gaba da ƙoƙarin daina wannan halin?

Kada ka yi sanyin gwiwa

Za ka iya yin tunani cewa, ‘Na yi ƙoƙari kuma na kasa, don haka na gaji.’ Amma ka tuna cewa idan mai gudun dogon zango ya yi tuntuɓe ya faɗi, hakan ba ya nufin cewa na shi ya ƙare ke nan, ko kuma yana bukatar ya koma ya fara daga farko. Hakazalika, idan mutum ya ɗan koma halinsa na dā, hakan ba ya nufin cewa ba zai iya barin halin banzan ba. Hakan kuma ba ya nufin cewa duk ƙoƙarin da ya yi ya zama banza. Yayin da kake ƙoƙarin daina halin banza, wataƙila za ka iya koma wa gidan jiya. Amma kar ka yi sanyin gwiwa, za ka yi nasara da taimakon Jehobah.

WASU SUN CE: “Ba zan iya dainawa ba, ya riga zama mini jiki.”

  • Wane nassi ne za ka iya karanta wa mutumin don ka nuna masa cewa zai iya daina halin banza da taimakon Jehobah?

TAƘAITAWA

Za mu faranta wa Jehobah rai idan mun kasance da tsabta a jikinmu da zuciyarmu da kuma halinmu.

Bita

  • Me ya sa kasancewa da tsabta yake da muhimmanci?

  • Ta yaya za ka tsabtace kanka?

  • Ta yaya za ka guji tunani da kuma halin banza?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abubuwan da mutum zai iya yi don ya kasance da tsabta ko da shi talaka ne.

Kiwon Lafiya​​—Wanke Hannu (3:01)

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwan da mutum zai iya yi don ya daina shan taba.

“Yadda Za Ka Daina Shan Taba” (Awake!, Mayu 2010)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda kallon batsa yake shafan mutum.

“Batsa​—Tana da Lahani ko A’a?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2013)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani mutum ya daina kallon batsa, duk da yake ya zama masa jiki.

“Na Ji Jiki Sosai Kafin Na Yi Nasara” (Hasumiyar Tsaro Na 4 2016)

aYadda Za Ka Daina Shan Taba,” da ke sashen Ka Bincika a wannan darasin ya bayyana abubuwan da mutum zai iya yi don ya daina shan taba ko da ya riga ya zama masa jiki.

b Don ka san abin da zai taimaka maka ka daina yin wasa da al’aura, ka duba “Ta Yaya Zan Daina Halin Wasa da Al’aura?Tambayoyin da Matasa Suke Yi​—Amsoshin da Suka Dace, Littafi na 1, babi na 25.