Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 41

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Jima’i?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Jima’i?

Mutane da yawa ba sa son tattaunawa game da jima’i. Amma idan Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da jima’i, yana yinsa ne a hanyar da ta dace da kuma dalla-dalla. Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai amfane mu domin Jehobah ne Mahaliccinmu. Ya san abin da zai fi taimaka mana. Ya gaya mana abin da za mu yi don mu faranta masa rai da kuma abin da za mu yi don mu sami rai na har abada.

1. Mene ne ra’ayin Jehobah game da jima’i?

Jima’i abu ne mai kyau da Jehobah ya ba wa ’yan Adam. Yana so mata da miji su ji daɗin yin jima’i. Yin jima’i ba don kawai ma’aurata su haifi yara ba ne. Amma yana ba wa ma’aurata dama su nuna wa juna ƙauna kuma su ji daɗin aurensu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi farin ciki da matarka ta ƙuruciyarka.” (Karin Magana 5:​18, 19) Jehobah yana so ma’aurata su kasance da aminci ga juna, ba ya son su yi zina.​—Karanta Ibraniyawa 13:4.

2. Mece ce lalata?

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da masu halin lalata cewa, “ba waninsu da zai shiga mulkin Allah.” (1 Korintiyawa 6:​9, 10) Marubutan Littafi Mai Tsarki da suka yi rubutunsu a Helenanci sun yi amfani da kalmar nan por·neiʹa don su kwatanta halin lalata. Hakan ya ƙunshi (1) yin jima’i a tsakanin mutane biyu da ba su auri juna ba, (2) luwaɗi da kuma (3) yin jima’i da dabbobi. Idan mun “guje wa halin lalata,” za mu faranta ran Jehobah kuma za mu amfana.​—1 Tasalonikawa 4:3.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka guji halin lalata da yadda za ka amfana idan ka yi hakan.

3. Ka guji yin lalata

Yusufu ya ƙi yin lalata da wata mata. Ku karanta Farawa 39:​1-12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya sa Yusufu ya gudu?​—Ka duba aya ta 9.

  • Kana ganin Yusufu ya tsai da shawara mai kyau kuwa? Me ya sa?

Ta yaya matasa za su yi koyi da Yusufu kuma su guji yin lalata? Ku kalli BIDIYON nan.

Jehobah yana so kowannenmu ya guji yin lalata. Ku karanta 1 Korintiyawa 6:​18, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wane yanayi ne zai iya sa mutum ya yi lalata?

  • Ta yaya za ka guji yin lalata?

4. Zai yiwu ka guji faɗawa cikin jarrabawa

Mene ne zai iya sa ya yi wa mutum wuya ya guji jarabar yin lalata? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Wane mataki ne ɗan’uwan da ke bidiyon ya ɗauka sa’ad da ya gane cewa tunaninsa da ayyukansa za su sa ya ci amanar matarsa?

A wasu lokuta, Kiristoci masu aminci ma suna fama da tunanin banza. Ta yaya mutum zai iya guji irin tunanin nan? Ku karanta Filibiyawa 4:​8, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wane irin tunani ne ya kamata mu riƙa yi?

  • Ta yaya karanta Littafi Mai Tsarki da kuma duƙufa a hidimar Jehobah za su taimaka maka ka guji yin zunubi?

5. Ƙa’idodin Jehobah suna amfanar mu

Jehobah ya san abin da ya fi dacewa da mu. Ya gaya mana yadda za mu guji yin lalata da kuma amfanin yin hakan. Ku karanta Karin Magana 7:​7-27 ko ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Ta yaya matashin ya faɗa cikin jaraba?​—Ka duba Karin Magana 7:​8, 9.

  • Karin Magana 7:​23, 26, sun nuna cewa yin lalata na kawo mummunan sakamako. Idan muka kāre kanmu daga yin lalata, waɗanne matsaloli ne za mu guje wa?

  • Ta yaya guje wa lalata zai sa mu ji daɗin rayuwa har abada?

Wasu mutane suna ganin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da luwaɗi bai dace ba. Amma Jehobah, Allah ne mai ƙauna kuma yana son kowa ya ji daɗin rayuwa har abada. Don mu yi hakan, wajibi ne mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. Ku karanta 1 Korintiyawa 6:​9-11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yin luwaɗi kawai ne Allah ya haramta?

Dukanmu muna bukatar mu yi canje-canje idan muna so mu faranta wa Allah rai. Kana ganin ya dace mu yi hakan? Ku karanta Zabura 19:​8, 11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin ƙa’idodin Jehobah game da guje wa lalata sun dace? Me ya sa?

Jehobah ya taimaka wa mutane da yawa su bi ƙa’idodinsa game da guje wa lalata. Kai ma zai taimaka maka

WASU SUN CE: “Ba laifi ba ne mutane biyu da suke son juna su yi jima’i.”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Jima’i abu ne mai kyau da Jehobah ya ba mata da miji don su ji daɗin aurensu.

Bita

  • Mene ne halin lalata ya ƙunsa?

  • Mene ne zai taimaka mana mu guji yin lalata?

  • Ta yaya za mu amfana idan muka bi ƙa’idodin Jehobah game da guje wa lalata?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilin da ya sa Allah yake so namiji da ta mace su yi aure in suna so su zauna tare.

“Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zaman Dadiro?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku koyi dalilin da ya sa ko da yake halin ’yan luwaɗi bai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, ba mu tsani ’yan luwaɗi ba.

“Yin Luwadi Zunubi Ne?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda dokokin Allah game da lalata suke kāre mu.

“Yin Jima’i Ta Baki Shi Ma Jima’i Ne?” (Talifin jw.org)

Ku karanta labarin nan mai jigo, “Sun Daraja Ni,” don ku ga yadda wani ɗan daudu ya canja salon rayuwarsa don ya faranta wa Allah rai.

“Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2011)

a Irin wannan jima’in ya haɗa da yin jima’i ta al’aura, ko ta baki ko ta ɗuwawu ko kuma tattaɓa al’aurar wani don tayar masa da sha’awa.