Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 43

Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Giya?

Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Giya?

Mutane a faɗin duniya suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da giya. Wasu suna jin daɗin shan giya da abokansu a wasu lokuta. Wasu kuma ba sa sha gabaki ɗaya. Wasu ma suna sha har su bugu. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da giya?

1. Laifi ne idan mutum ya sha giya?

Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ambata giya a matsayin ɗaya daga cikin abubuwa masu kyau da Allah ya ba mu. Ya ce, “ruwan inabi” yana “faranta wa mutum zuciya.” (Zabura 104:​14, 15) A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata wasu mata da maza masu aminci da suka sha ruwan inabi.​—1 Timoti 5:23.

2. Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba waɗanda suka zaɓi su sha giya?

Jehobah ya haramta yawan shan giya da buguwa. (Galatiyawa 5:21) Kalmarsa ta ce: “Kada ka haɗa kai da masu buguwa.” (Karin Magana 23:20) Idan muka zaɓi mu sha giya ko da mu kaɗai ne ko kuma muna tare da wasu, bai kamata mu sha giya har mu bugu ba. Domin yin hakan zai iya sa mu yi abubuwan da ba su dace ba ko mu jawo wa kanmu lahani. Idan ba mu san yadda za mu rage shan giya ba, ya kamata mu daina sha gabaki ɗaya.

3. Ta yaya za mu daraja shawarwarin da wasu suka yanke game da shan giya?

Kowane mutum ne zai tsai da shawara ko zai sha giya ko a’a. Bai kamata mu ga waɗanda suka zaɓi su sha giya daidai-wa-daida a matsayin masu laifi ba, kuma bai kamata mu matsa wa wani ya sha giya idan ya ce ba ya so ya sha ba. (Romawa 14:10) Bai kamata mu sha giya ba idan hakan zai iya sa wasu cikin matsala. (Karanta Romawa 14:21.) Littafi Mai Tsarki ya ce “kowanne mutum ya ci gaba da neman abin da zai amfani wani, ba abin da zai amfani kansa kaɗai ba.”​—Karanta 1 Korintiyawa 10:​23, 24.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka ka yanke shawara ko za ka sha giya da kuma yawan giya da ya dace ka sha. Za mu kuma ga abin da za ka yi idan kana da matsalar shan giya da yawa.

4. Ka yanke shawara ko za ka sha giya ko a’a

Mene ne ra’ayin Yesu game da shan giya? Don ka san amsar, ka yi la’akari da mu’ujiza ta farko da Yesu ya yi. Ku karanta Yohanna 2:​1-11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya mu’ujizar nan da Yesu ya yi ta nuna ra’ayinsa game da giya da kuma waɗanda suke sha?

  • Tun da Yesu bai hana shan giya ba, yaya ya kamata Kirista ya ɗauki waɗanda suke shan giya?

Tun da yake ba a hana Kiristoci shan giya ba, hakan yana nufin cewa a kowane lokaci ne za su riƙa shan giya? Ku karanta Karin Magana 22:​3, sai ku lura da abubuwan da aka ambata a gaba don ku san yanayoyin da za ka yanke shawara ko za ka sha giya ko a’a:

  • Lokacin da za ka yi tuƙi ko kuma za ka yi aiki da wani inji.

  • Idan mace tana da juna biyu.

  • Idan likita ya ce kada ka sha giya.

  • Idan yana maka wuya ka rage yawan giya da kake sha.

  • Idan dokar ƙasarku ta hana ka shan giya.

  • Idan kana tare da wani da ya yi masa wuya ya rage shan giya a dā, amma yanzu ya daina sha.

Zai dace a raba giya a bikin aure ko a lokacin liyafa? Don ku san shawarar da za ku yanke, ku kalli BIDIYON nan.

Ku karanta Romawa 13:13 da 1 Korintiyawa 10:​31, 32. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya bin wannan ƙa’idar za ta taimaka maka ka yanke shawarar da za ta faranta ran Jehobah?

Kowane Kirista ne zai yanke shawara ko zai sha giya ko a’a. Ko da yana shan giya, zai iya ƙin yin hakan a wasu lokuta

5. Ka yanke shawara a kan yawan giyar da za ka sha

Idan ka yanke shawarar shan giya, ka tuna cewa: Ko da yake Jehobah bai haramta shan giya ba, ya haramta buguwa da giya. Me ya sa? Ku karanta Hosiya 4:​11, 18, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me zai iya faruwa idan mutum ya sha giya da yawa?

Ta yaya za mu guji shan giya da yawa? Muna bukata mu san iyakar giyar da ya kamata mu sha. Ku karanta Karin Magana 11:​2, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa zai dace ka yanke shawara a kan yawan giya da za ka sha?

6. Abin da zai taimaka maka ka daina yawan shan giya

Ku ga abin da ya taimaka wa wani mutum ya daina buguwa da giya. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, ta yaya shan giya ya shafi Dmitry?

  • Ya yi masa sauƙi ya daina shan giya nan da nan kuwa?

  • Me ya taimaka masa ya daina buguwa da giya?

Ku karanta 1 Korintiyawa 6:​10, 11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da buguwa da giya?

  • Mene ne ya nuna cewa mutum da ke buguwa da giya zai iya canjawa?

Ku karanta Matiyu 5:​30, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Sa’ad da Yesu ya ce mutum ya yanke hannunsa ya yar, hakan yana nufin cewa muna bukatar mu daina wani abu don mu faranta ran Jehobah. Mene ne za ka yi idan kana fama da yadda za ka daina buguwa da giya? a

Ku karanta 1 Korintiyawa 15:​33, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me zai faru da kai idan kana tarayya da mutane da suke shan giya da yawa?

WANI YANA IYA CEWA: “Shan giya laifi ne?”

  • Me za ka ce wa mutumin?

TAƘAITAWA

Giya kyauta ce da Jehobah ya ba mu don mu ji daɗi, amma ya haramta yawan shan giya da kuma buguwa.

Bita

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da giya?

  • Me ya sa yawan shan giya bai da kyau?

  • Me ya sa ya dace mu daraja shawarwarin da wasu suka yanke game da shan giya?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda matasa za su iya yanke shawara mai kyau game da shan giya.

Ka Yi Tunani da Kyau Kafin Ka Sha Giya (2:31)

Ku karanta talifin nan don ku ga matakan da mutum zai iya ɗauka idan yana fama da yawan shan giya.

“Ra’ayin da Ya Dace Game da Giya” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2010)

Ya kamata Kiristoci su riƙa kara kofi ne, wato toasting? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Fabrairu, 2007)

Ku karanta labarin Luka Šuc don ku ga yadda ya daina shan giya da yawa.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Mayu, 2012)

a Mutane da suke yawan buguwa da giya ƙila za su bukaci taimakon likita don su daina. Likitoci da yawa sun ce mutanen da suke yawan buguwa da giya su daina shan giya kwata-kwata.