Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 45

Abin da Nisanta Kanmu Daga Harkokin Duniya Yake Nufi

Abin da Nisanta Kanmu Daga Harkokin Duniya Yake Nufi

Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa bai kamata su zama “na duniya ba.” (Yohanna 15:19) Hakan yana nufin cewa ba za su saka hannu a siyasa da kuma yaƙi ba. Gaskiyar ita ce, nisanta kanmu daga harkokin duniya yana da wuya. Mutane za su iya yi mana ba’a don hakan. Ta yaya za mu iya nisanta kanmu daga harkokin duniya kuma mu kasance da aminci ga Jehobah?

1. Ta yaya Kiristoci na gaskiya suke ɗaukan gwamnatocin ’yan Adam?

Kiristoci suna daraja gwamnati. Muna yin abin da Yesu ya faɗa cewa mu “ba Kaisar abin da yake na Kaisar,” wato mu yi biyayya da dokokin ƙasarmu kamar wanda ya ce mu riƙa biyan haraji. (Markus 12:17) Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa gwamnatocin ’yan Adam suna mulki ne domin Jehobah ya ƙyale su su yi hakan. (Romawa 13:1) Saboda haka, mun fahimci cewa gwamnatocin ’yan Adam ba su da cikkaken iko. Allah ne ta wurin Mulkinsa zai magance matsalolin ’yan Adam.

2. Ta yaya za mu nuna cewa muna nisanta kanmu daga harkokin duniya?

Kamar Yesu, ba ma saka hannu a siyasa. Sa’ad da mutane suka ga wata mu’ujiza da Yesu ya yi, sai suka yi ƙoƙari su naɗa shi ya zama sarkinsu, amma bai yarda ba. (Yohanna 6:15) Me ya sa? Yesu ya ce, “Mulkina ba iri na duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) A matsayinmu na mabiyan Yesu, muna nuna cewa mun nisanta kanmu daga harkokin duniya a hanyoyi da yawa. Alal misali, ba ma zuwa yaƙi. (Karanta Mika 4:3.) Muna daraja abubuwa kamar su tutar ƙasa amma ba ma bauta musu. (1 Yohanna 5:21) Kuma ba ma goyon bayan wani rukunin siyasa ko wani ɗan siyasa. A waɗannan hanyoyi da kuma wasu, muna nuna cewa muna goyon bayan Mulkin Allah.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yanayoyin da za su iya sa ya yi mana wuya mu guji saka hannu a harkokin duniya, kuma za mu ga yadda za mu yanke shawarwari da za su faranta ran Jehobah.

3. Kiristoci na gaskiya ba sa saka hannu a harkokin duniya

Yesu da mabiyansa sun kafa mana misali mai kyau. Ku karanta Romawa 13:​1, 5-7 da 1 Bitrus 2:​13, 14. Sai ku kalli BIDIYON nan kuma ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa daraja masu mulki?

  • A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna yi musu biyayya?

A lokacin yaƙi, wasu ƙasashe suna yin kamar ba ruwansu da yaƙin, amma suna taimakawa ɓangarori biyu da ke yaƙin. Mene ne ake nufin da ƙin saka hannu a harkokin duniya? Ku karanta Yohanna 17:16. Sai ku kalli BIDIYON nan kuma ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Mene ne ake nufi da ƙin saka hannu a harkokin duniya?

Idan gwamnati ta ce mu yi abin da ya saɓa wa dokar Allah kuma fa? Ku karanta Ayyukan Manzanni 5:​28, 29. Sai ku kalli BIDIYON nan kuma ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Idan dokar ’yan Adam ta saɓa wa dokar Allah, wane ne za mu bi?

  • A waɗanne yanayoyi ne Kiristoci ba za su yi biyayya da masu mulki ba?

4. Zai dace tunaninmu da ayyukanmu su nuna cewa ba ruwanmu da harkokin duniya

Ku karanta 1 Yohanna 5:21. Sai ku kalli BIDIYON nan kuma ku tattauna tambayoyi da ke gaba.

  • A bidiyon, me ya sa Ayenge ya ƙi shigan jam’iyar siyasa na ƙasarsu, kuma ya ƙi sara wa tuta?

  • Kana ganin ya yanke shawara mai kyau kuwa?

Waɗanne yanayoyi ne za su iya jarraba amincinmu? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna nisanta kanmu daga harkokin duniya sa’ad da ƙasashe dabam-dabam suke wasa?

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna nisanta kanmu daga harkokin duniya idan shawarar da ’yan siyasa suka yanke ta shafe mu?

  • Ta yaya yawan jin labaran siyasa daga kafofin yaɗa labarai, ko kuma cuɗanya da mutane da suke son magana game da siyasa zai iya shafan mu?

A waɗanne yanayoyi ne ya kamata Kiristoci su nisanta kansu daga harkokin duniya a tunaninsu da kuma ayyukansu?

WANI YANA IYA CEWA: “Me ya sa ba kwa sara wa tuta ko ku rera taken ƙasa?”

  • Me za ka ce masa?

TAƘAITAWA

Kiristoci suna iya ƙoƙarinsu don kada su goyi bayan wani jam’iyar siyasa a tunaninsu ko furucinsu ko kuma a ayyukansu.

Bita

  • Me ya kamata mu riƙa yi wa gwamnatin ’yan Adam?

  • Me ya sa ba ma saka hannu a harkokin siyasa?

  • Waɗanne yanayoyi ne za su iya jarraba amincinmu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abubuwan da za mu sadaukar idan muna so mu nisanta kanmu daga harkokin duniya.

Jehobah Bai Bar Mu Ba (3:14)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda iyalai za su iya shiri don su kasance da aminci sa’ad da suka fuskanci jarrabawa.

Kasancewa da Aminci A Dukan Lokaci (4:25)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda bauta wa Jehobah ya fi ƙoƙarin kāre ƙasarmu.

“Kowane Abu Mai Yiwuwa Ne a Wurin Allah” (5:19)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda mutum zai nisanta kansa daga harkokin duniya a lokacin da yake so ya yanke shawara game da aikin da zai yi.

“Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2006)