Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 46

Me Ya Sa Za Ka Yi Alkawarin Bauta wa Allah?

Me Ya Sa Za Ka Yi Alkawarin Bauta wa Allah?

Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kaɗai, hakan yana nufin cewa za ka saka yin nufinsa a kan gaba a rayuwarka. (Zabura 40:8) Bayan haka, sai ka yi baftisma. Hakan zai nuna wa mutane cewa ka yi alkawarin bauta wa Allah. Yanke shawarar bauta wa Jehobah ce shawara mafi muhimmanci da za mu yi a rayuwa. Mene ne zai iya motsa ka ka yanke wannan shawarar da za ta canja rayuwarka?

1. Mene ne ke motsa mutum ya yi alkawarin bauta wa Allah?

Ƙauna ce take sa mu yi alkawarin bauta wa Jehobah. (1 Yohanna 4:​10, 19) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.” (Markus 12:30) Muna nuna ƙaunarmu ga Allah ta furucinmu da ayyukanmu. Kamar yadda saurayi da budurwa da suke ƙaunar juna suke yin aure, hakazalika, idan muna ƙaunar Jehobah, za mu yi alkawarin bauta masa kuma mu yi baftisma.

2. Waɗanne albarku ne Shaidun Jehobah da suka yi baftisma suke samu?

Sa’ad da ka yi baftisma, za ka zama ɗaya cikin waɗanda suke bauta masa da farin ciki. Hakan zai sa Jehobah ya ƙaunace ka sosai kuma za ka kusace shi fiye da dā. (Karanta Malakai 3:​16-18.) Ƙari ga haka, Jehobah zai zama Uba a gare ka, kuma za ka sami ’yan’uwa a faɗin duniya da suke ƙaunar Jehobah kuma suke ƙaunar ka. (Karanta Markus 10:​29, 30.) Amma, akwai wasu matakai da za ka ɗauka kafin ka yi baftisma. Kana bukatar ka koyi game da Jehobah, ka ƙaunace shi kuma ka ba da gaskiya ga Ɗansa. A ƙarshe, wajibi ne ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. Idan ka yi waɗannan abubuwan kuma ka yi baftisma, hakan zai sa ka ji daɗin rayuwa har abada. Kalmar Allah ta ce: “Baftisma . . . ta cece ku a yanzu.”​—1 Bitrus 3:21.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abin da ya sa yake da muhimmanci ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma.

3. Wajibi ne mu zaɓi wanda za mu bauta masa

A Isra’ila ta dā, wasu suna ganin za su iya bauta wa Jehobah da kuma Ba’al, allahn ƙarya. Jehobah ya tura annabinsa Iliya don ya daidaita ra’ayinsu. Ku karanta 1 Sarakuna 18:​21, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane zaɓi ne ya kamata Isra’ilawa su yi?

Kamar Isra’ilawa, wajibi ne mu ma mu zaɓi wanda za mu bauta wa. Ku karanta Luka 16:​13, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa bai kamata mu bauta wa Jehobah kuma mu bauta wa wani mutum ko abu ba?

  • Ta yaya za mu nuna wa Jehobah cewa mun zaɓa mu bauta masa?

4. Ka yi tunanin yadda Jehobah yake ƙaunar ka

Jehobah ya ba mu abubuwa da yawa masu kyau. Mene ne za mu iya ba shi? Ku kalli BIDIYON nan.

A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna yana ƙaunar ka? Ku karanta Zabura 104:​14, 15 da 1 Yohanna 4:​9, 10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya ba ka da kake alfahari da su?

  • Yaya waɗannan abubuwa suke sa ka ji game da shi?

Idan aka ba mu kyauta da muke so sosai, za mu nuna godiya ga wanda ya ba mu kyautar. Ku karanta Maimaitawar Shari’a 16:​17, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Idan ka yi tunani a kan dukan abubuwan da Jehobah ya yi maka, mene ne za ka yi don ka nuna godiya?

5. Yin alkawarin bauta wa Jehobah zai sa ka sami albarku da yawa

Mutane da yawa suna ganin cewa yin suna, ko aiki mai kyau ko kuma kuɗi zai sa su farin ciki. Hakan gaskiya ne? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Ko da yake ɗan wasa da aka nuna a bidiyon yana son buga ƙwallo sosai, me ya sa ya bari?

  • Ya tsai da shawarar ɗaukan ibadarsa ga Jehobah da muhimmanci fiye da buga ƙwallo. Kana ganin ya tsai da shawara mai kyau? Me ya sa?

Kafin manzo Bulus ya zama Kirista, yana da babban matsayi a aikin da yake yi. Shi lauya ne kuma sanannen malami ne ya koyar da shi. Amma ya bar matsayinsa don ya zama Kirista. Shin Bulus ya yi da-na-sani ne? Ku karanta Filibiyawa 3:​8, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa Bulus ya ce abubuwan da ya yi a dā kafin ya zama Kirista kayan “banza” ne ko kuma bola?

  • Wace albarka ce ya samu?

  • Kana ganin za ka fi jin daɗin rayuwa idan ka bauta wa Jehobah? Me ya sa?

Sa’ad da Bulus ya zama Kirista, albarkun da ya samu sun fi abubuwan da ya rasa

WASU SUN CE: “Na san cewa kuna koyar da gaskiya amma ban yi shirin yin baftisma ba tukuna.”

  • Me ya sa kake ganin ya dace ka yi alkawarin bauta wa Jehobah?

TAƘAITAWA

Ƙauna ce take sa mu yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma mu yi baftisma.

Bita

  • Me ya sa muke bukatar mu ƙaunaci Jehobah kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu?

  • Wace albarka ce Shaidun da suka yi baftisma suke samu?

  • Za ka so ka yi alkawarin bauta wa Jehobah?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da ya sa wata mawaƙiya da wani ɗan wasa suka zaɓa su yi alkawarin bauta wa Jehobah.

Tambayoyin Matasa​—Me Zan Yi da Rayuwata?​—Tuna Baya (6:54)

Ku karanta talifin nan don ku ga ƙarin dalilai da za su sa mutum ya yi alkawarin bauta wa Jehobah.

“Me Ya Sa Za Ka Keɓe Kanka Ga Jehobah?” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Janairu, 2010)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda waɗanda suka yi alkawarin bauta wa Jehobah suke farin ciki.

Na Ba Jehobah Rayuwata (4:30)

Ku karanta labarin Rosalind John don ku ga abin da ya sa ta yi tunanin abin da ya fi muhimmanci a rayuwarta.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2012)