Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 47

Na Shirya Yin Baftisma Kuwa?

Na Shirya Yin Baftisma Kuwa?

Ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah a nazarinka na Littafi Mai Tsarki. Wataƙila ka yi wasu canje-canje don ka yi abin da ka koya. Mai yiwuwa kana jinkirin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma don wasu dalilai. A wannan darasin, za a tattauna wasu abubuwan da za su iya hana ka yin baftisma da kuma yadda za ka shawo kansu.

1. Kana bukata ka san duk abin da ke Littafi Mai Tsarki ne kafin ka yi baftisma?

Don ka yi baftisma, kana bukatar ka “kai ga sanin gaskiya.” (1 Timoti 2:4) Hakan ba ya nufin cewa sai ka san amsoshin dukan tambayoyin Littafi Mai Tsarki kafin ka yi baftisma. Kiristocin da suka daɗe da yin baftisma ma suna kan koyo. (Kolosiyawa 1:​9, 10) Amma akwai muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki da kake bukata ka sani. Idan kana shakka ko ka san muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki, dattawa za su iya taimaka maka.

2. Waɗanne matakai ne kake bukata ka ɗauka kafin ka yi baftisma?

Kafin ka yi baftisma, wajibi ne ka “tuba” ka kuma “juyo” ga Allah. (Karanta Ayyukan Manzanni 3:19.) Hakan yana nufin cewa za ka yi nadama a kan zunuban da ka yi a dā kuma ka roƙi Jehobah ya gafarta maka. Sa’an nan ka ƙuduri niyyar ƙin abubuwan da Allah ya tsana don ka yi abin da zai faranta masa rai. Ban da haka, ka soma halartan taro kuma ka soma wa’azi a matsayin mai shela da bai yi baftisma ba.

3. Me ya sa bai kamata ka ji tsoron yin baftisma ba?

Wasu suna tsoro cewa ba za su iya cika alkawarin da suka yi wa Jehobah ba. Gaskiyar ita ce a wasu lokuta, za ka yi kuskure kamar yadda mutanen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suka yi. Ka tuna cewa Jehobah bai bukaci bayinsa su zama kamiltattu ba. (Karanta Zabura 103:​13, 14.) Yana farin ciki idan kana iya ƙoƙarinka! Zai taimaka maka. Jehobah ya tabbatar mana cewa babu abin da zai ‘raba mu da ƙaunarsa.’​—Karanta Romawa 8:​38, 39.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka shawo kan matsalolin da za su iya hana ka yin baftisma ta wajen daɗa koya game da Jehobah da amincewa da taimakonsa.

4. Ka daɗa koya game da Jehobah

Waɗanne abubuwa ne ya kamata ka san game da Jehobah kafin ka yi baftisma? Kana bukatar ka san shi sosai, ka ƙaunace shi kuma ka riƙa faranta masa rai. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga yadda ɗaliban Littafi Mai Tsarki a faɗin duniya suke yin hakan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, me ya taimaka wa wasu mutane su shirya yin baftisma?

Ku karanta Romawa 12:​2, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki, ko kuma kana shakka cewa koyarwar Shaidun Jehobah gaskiya ne?

  • Idan haka ne, me za ka yi?

5. Yadda za ka shawo kan matsalolin da za su iya hana ka yin baftisma

Sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma muka yi baftisma, mukan fuskanci matsaloli sosai. Don ku ga wani misali, ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, waɗanne matsaloli ne Narangerel take bukatar ta shawo kansu don ta bauta wa Jehobah?

  • Ta yaya ƙaunarta ga Jehobah ta taimaka mata ta shawo kan matsalolin?

Ku karanta Karin Magana 29:25 da 2 Timoti 1:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne yake ba mu ƙarfin zuciyar shawo kan matsaloli?

6. Ka nemi taimakon Jehobah

Jehobah zai taimaka maka ka riƙa yin abin da yake so. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, me ya sa ɗalibin ya yi jinkirin yin baftisma?

  • Me ya koya da ya taimaka masa ya daɗa dogara ga Jehobah?

Ku karanta Ishaya 41:​10, 13, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa kake da tabbaci cewa za ka iya cika alkawarin da ka yi na bauta wa Jehobah?

7. Ka daɗa nuna godiya don ƙaunar da Jehobah yake nuna maka

Idan ka ci gaba da tunani game da yadda Jehobah yake ƙaunar ka, za ka daɗa gode masa kuma hakan zai sa ka so bauta masa har abada. Ku karanta Zabura 40:​5, sai ku tattauna tambayar nan:

  • A cikin albarkun da Jehobah ya yi maka, wane ne ya fi burge ka?

Annabi Irmiya ya ƙaunaci Jehobah da kuma kalmarsa, kuma ya nuna godiya sosai domin damar zaman bawan Jehobah. Ya ce: “Ga zuciyata, maganarka kuwa ta zama abin farin ciki da murna. Gama ana kirana da Sunanka, ya Yahweh Allah.” (Irmiya 15:16) Ka amsa waɗannan tambayoyin:

  • Me ya sa zama Mashaidin Jehobah gata ce ta musamman?

  • Kana so ka yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah?

  • Akwai abin da zai hana ka yin hakan?

  • Mene ne kake ganin ya kamata ka yi don ka iya ka yi baftisma?

WASU SUN CE: “Ina ganin ba zan iya cika alkawarin da na ɗauka idan na yi baftisma ba.”

  • Haka kake ji?

TAƘAITAWA

Da taimakon Jehobah, za ka shawo kan duk wata matsala da za ta iya hana ka yin baftisma.

Bita

  • Kana bukatar ka san duk abin da ke Littafi Mai Tsarki ne kafin ka yi baftisma?

  • Waɗanne canje-canje ne ya kamata ka yi don ka yi baftisma?

  • Me ya sa bai kamata ka bar tsoro ya hana ka yin baftisma ba?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da mutum ya kamata ya yi kafin ya yi baftisma.

“Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?” (Hasumiyar Tsaro, Maris 2020)

Ku karanta talifin nan don ka ga wasu matsaloli da za su iya hana ka yin baftisma.

“Mene ne Yake Hana Ni Yin Baftisma?” (Hasumiyar Tsaro, Maris 2019)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mutum ya shawo kan wata babbar matsala kafin ya yi baftisma.

‘Me Ke Hana Ka Yin Baftisma?’ (1:10)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da ya sa wani mutum mai suna Ataa ya yi jinkirin yin baftisma. Da kuma abin da ya sa ya ɗauki matakin nan mai muhimmanci.

Ni Ne Na Sami Dukan Albarkun Nan? (7:21)