Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 48

Ka Zabi Abokan Kirki

Ka Zabi Abokan Kirki

Abokanmu sukan taya mu murna a lokacin da muke farin ciki, kuma su ƙarfafa mu sa’ad da muke cikin matsala. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ba kowa ba ne abokin kirki. To, ta yaya za ka iya zaɓan abokan kirki? Ka yi la’akari da tambayoyi na gaba.

1. Ta yaya abokanka za su iya sa ka zama mutumin kirki ko na banza?

Muna yin koyi da mutane da muke cuɗanya da su. Hakan zai iya sa mu kasance da halin kirki ko halin banza, ko da muna cuɗanya da su a zahiri ne ko ta dandalin sada zumunta. Littafi Mai Tsarki ya ce, “wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima, amma abokin tafiyar wawaye [waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah] zai lalace.” (Karin Magana 13:20) Abokan da suke ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa, za su taimaka maka ka ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. Kuma za su iya taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau. Amma abokan da ba sa ƙaunar Jehobah za su iya sa mu daina bauta masa. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu zaɓi abokan kirki! Idan abokanmu mutanen da suke ƙaunar Jehobah ne, za mu taimaki juna, mu “ƙarfafa juna” kuma mu “yi ta gina juna.”​​—1 Tasalonikawa 5:11.

2. Jehobah yana son irin abokan da kake cuɗanya da su?

Jehobah yana zaɓan abokan kirki. Littafi Mai Tsarki ya ce, “yana amincewa da mai gaskiya a zuci.” (Karin Magana 3:32) Yaya Jehobah zai ji idan muna cuɗanya da mutanen da ba sa ƙaunar sa? Hakan zai sa shi baƙin ciki sosai! (Karanta Yakub 4:4.) Amma Jehobah zai yi farin ciki kuma za mu zama abokansa idan muka guji abokan banza, kuma muka kusace shi da kuma waɗanda suke ƙaunar sa.​—Zabura 15:​1-4.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abin da ya sa yake da muhimmanci ka zaɓi abokan kirki da kuma yadda za ka ƙulla abokantakar da za ta taimaka maka sosai.

3. Ku guji abokan banza

Mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah kuma ba sa bin ƙa’idodinsa abokan banza ne. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya za mu soma cuɗanya da abokan banza ba tare da saninmu ba?

Ku karanta 1 Korintiyawa 15:​33, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne irin mutane ne bai kamata mu yi tarayya da su ba? Me ya sa?

Ku karanta Zabura 119:​63, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me zai taimaka maka ka san ko yin abota da wani ya dace?

Idan ’ya’yan itace guda ɗaya ya lalace zai iya ɓata sauran. Ta yaya tarayya da abokan banza zai iya ɓata halinka?

4. Za mu iya yin abota da mutanen da shekarunmu ko yanayinmu ya bambanta

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Dauda da Jonathan da suke Isra’ila ta dā. Jonathan ya girme Dauda sosai kuma shi yarima ne. Duk da haka, su abokai ne na kud da kud. Ku karanta 1 Sama’ila 18:​1, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa bai kamata mu riƙa zaɓan tsaranmu ko waɗanda matsayinmu ɗaya ne kawai su zama abokanmu ba?

Ku karanta Romawa 1:​11, 12, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya abokan da suke ƙaunar Jehobah suke ƙarfafa juna?

A bidiyon nan, ku ga yadda wani matashi ya sami abokai a wurin da bai yi zato ba. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, me ya sa iyayen Akil suka yi masa gargaɗi game da abokansa a makaranta?

  • Me ya sa Akil ya so waɗannan abokan?

  • Mene ne ya taimaka masa ya shawo kan matsalarsa?

5. Yadda za ka sami abokan kirki

Za ka koyi yadda za ka sami abokan kirki da kuma yadda kai ma za ka zama aboki na ƙwarai. Ku kalli BIDIYON nan.

Ku karanta Karin Magana 18:24 da 27:17, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya abokai na ƙwarai suke taimaka wa juna?

  • Kana da irin waɗannan abokan? Idan ba ka da su, ta yaya za ka iya samun su?

Ku karanta Filibiyawa 2:​4, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Don ka sami abokan kirki, kai ma kana bukatar ka zama abokin kirki. Ta yaya za ka iya yin hakan?

Don ka sami abokan kirki, kai ma kana bukatar ka zama abokin kirki

WASU SUN CE: “Ko da wane irin hali ne mutum yake da shi, zai iya zama abokina, idan har yana mutunta ni.”

  • Mene ne ra’ayinka?

TAƘAITAWA

Idan muka zaɓi abokan kirki, hakan zai sa Jehobah farin ciki kuma za mu amfana.

Bita

  • Me ya sa Jehobah yake damuwa game da irin abokan da muka zaɓa?

  • Waɗanne irin mutane ne bai kamata su zama abokanmu ba?

  • Ta yaya za ka iya ƙulla abokantaka na kud da kud da mutanen da suke ƙaunar Jehobah?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda abokan kirki za su iya taimaka mana a mawuyacin lokaci.

“Ku Yi Abokan Kirki Kafin Ƙarshe Ya Zo” (Hasumiyar Tsaro, Nuwamba 2019)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da ya kamata ku sani game da yin abokantaka a dandalin sada zumunta na Intane.

Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta na Intanet (4:12)

Ku karanta labarin nan “Na Yi Begen Samun Uba,” don ku ga dalilin da ya sa wani mutum ya daina tarayya da wasu abokansa.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2012)