Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 50

Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?

Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?

Yara kyauta ne daga wurin Jehobah. Yana so iyaye su kula da yaransu sosai. Akwai shawarwari masu kyau da Jehobah ya bayar da za su taimaka wa iyaye su yi hakan. Shawarwarin za su taimaka wa yara su sa iyayensu farin ciki.

1. Wace shawara ce Jehobah ya ba iyaye?

Jehobah yana so iyaye su ƙaunaci yaransu kuma su riƙa kasancewa tare da su sosai. Ƙari ga haka, yana so iyaye su kāre yaransu kuma su yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su koyar da su. (Karin Magana 1:8) Jehobah ya gaya wa ubanni cewa: “Kuna koyar [da yaranku] da kuma yi musu horo yadda Jehobah yake so.” (Karanta Afisawa 6:4.) Jehobah yana farin ciki idan iyaye suka bi ja-gorancinsa sa’ad da suke renon yaransu kuma ba su danƙa wa wani wannan hakkin ba.

2. Wace shawara ce Jehobah ya ba yara?

Jehobah ya gargaɗi yara cewa: “Ku yi wa iyayenku biyayya.” (Karanta Kolosiyawa 3:20.) Idan yara suka girmama iyayensu kuma suka yi musu biyayya, suna sa Jehobah da iyayensu farin ciki. (Karin Magana 23:​22-25) Yesu ya kafa misali mai kyau sa’ad da yake yaro. Ya yi wa iyayensa biyayya kuma ya girmama su ko da yake shi kamiltacce ne.​—Luka 2:​51, 52.

3. Ta yaya iyaye da yara za su kasance da dangantaka mai kyau da Allah?

Idan kana da yara, babu shakka za ka so su ƙaunaci Jehobah yadda kake ƙaunar sa. Ta yaya za ka iya cim ma hakan? Ta wurin yin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: “Da ƙwazo za ku koyar da [kalmar Jehobah] ga ’ya’yanku. Za ku dinga magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya.” (Maimaitawar Shari’a 6:7) Wajibi ne ka riƙa maimaita wa yaranka abubuwa don kada su manta. Wannan nassin yana nufin cewa ya kamata ka nemi zarafin gaya wa yaranka game da Jehobah a kai a kai. Iyaye, ya kamata ku keɓe lokaci kowane mako don ku riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki tare da yaranku. Idan ba ku da yara, za ku amfana sosai idan kuka keɓe lokaci kowane mako don ku yi nazarin Kalmar Allah.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga shawarwarin da za su sa kowa a iyali ya riƙa farin ciki kuma ya kasance da kwanciyar hankali.

4. Ku koyar da yaranku don kuna ƙaunar su

Koyar da yara yakan yi wuya. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka? Ku karanta Yakub 1:​19, 20, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya iyaye za su nuna suna ƙaunar yaransu sa’ad da suke tattaunawa da su?

  • Me ya sa bai kamata iyaye su horar da yaransu sa’ad da iyayen suke fushi ba? a

5. Ka kāre yaranka

Don ka kāre yaranka, yana da muhimmanci ka yi wa kowannensu magana game da jima’i. Yin hakan zai iya yi maka wuya. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Me ya sa yake wa wasu iyaye wuya su tattauna da yaransu game da jima’i?

  • Ta yaya wasu iyaye suka yi wa yaransu bayani game da jima’i?

Kamar yadda aka ambata a Littafi Mai Tsarki, duniyar nan tana daɗa muni. Ku karanta 2 Timoti 3:​1, 13, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wasu mugayen mutane da aka ambata a aya ta 13 suna ɓata yara. Saboda haka, me ya sa yake da muhimmanci iyaye su koya wa yaransu game da jima’i da kuma yadda yaran za su kāre kansu daga masu ɓata ƙananan yara?

Ka sani?

Shaidun Jehobah sun wallafa littattafai da ke taimaka wa iyaye su koya wa yaransu game da jima’i da kuma kāre su daga masu ɓata yara. Alal misali, ku duba:

6. Ku riƙa yi wa iyayenku ladabi

Yara da matasa suna yi wa iyayensu ladabi ta yadda suke musu magana. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Me ya sa ya dace yaro ko matashi ya riƙa yi wa iyayensa magana da ladabi?

  • Ta yaya matashi zai riƙa yi wa iyayensa magana a hanyar da za ta nuna cewa yana girmama su?

Ku karanta Karin Magana 1:​8, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne ya kamata matashi ya yi sa’ad da iyayensa suka ba shi umurni?

7. Ku keɓe lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki tare

Shaidun Jehobah suna keɓe lokaci kowane mako don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare a iyalinsu. Mene ne za ku iya yi a wannan lokacin? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Mene ne zai taimaka wa iyalai su riƙa yin Ibada ta Iyali ba tare da fashi ba?

  • Mene ne iyaye za su yi don iyalinsu su riƙa jin daɗin ibada ta iyali?​—Ka duba hoton shafin farko na darasin nan.

  • Mene ne zai iya sa ya yi muku wuya ku yi nazari tare?

A Isra’ila ta dā, Jehobah yana so iyalai su riƙa tattauna Nassosi a kai a kai. Ku karanta Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya za ka bi wannan ƙa’idar?

Abubuwan da iyalai za su iya yi a ibada ta iyali:

  • Ku shirya taron ikilisiya.

  • Ku karanta kuma ku tattauna wani labari a Littafi Mai Tsarki da iyalinku za su ji daɗinsa.

  • Idan kuna da ƙananan yara, ku yi amfani da ayyuka don yara da ke dandalin jw.org.

  • Idan kuna da matasa, ku tattauna wani talifin matasa a dandalin jw.org.

  • Ku yi kwaikwayon wani labari a Littafi Mai Tsarki tare da yaranku.

  • Ku kalli wani bidiyo a dandalin jw.org kuma ku tattauna shi.

WASU SUN CE: “Muna da ayyuka da yawa, ba mu da lokacin koya wa yaranmu Littafi Mai Tsarki.”

  • Me za ka gaya musu?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so iyaye su riƙa ƙaunar yaransu, su koyar da su kuma su kāre su. Yana so yara su riƙa yi wa iyayensu ladabi da biyayya. Ƙari ga haka, Jehobah yana so iyalai su riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki tare.

Bita

  • Ta yaya iyaye za su riƙa koyar da yaransu kuma su kāre su?

  • Ta yaya yara za su riƙa girmama iyayensu?

  • Mene ne amfanin keɓe lokaci kowane mako don yin ibada ta iyali?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwan da za su taimaka wa yaranku idan sun yi girma.

“Abubuwa Shida da Ya Kamata Yara Su Koya” (Awake! Na 2 2019, English)

Ku karanta talifin nan don ku ga shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba waɗanda suke kula da iyayensu tsofaffi.

“Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kula da Iyaye da Suka Tsufa?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mutum da bai san yadda zai yi renon yaransa ba ya yi nasara.

Jehobah ne Ya Koya Mana Yadda Za Mu Horar da Yaranmu (5:58)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda iyaye maza za su ƙarfafa dangantakarsu da yaransu maza.

“Ta Yaya Iyaye Maza Za Su Kusaci ’Ya’yansu Maza?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2012)

a A Littafi Mai Tsarki, “horarwa” tana nufin a koyar da yara da yi musu ja-goranci da kuma taimaka musu su canja wani ra’ayi ko halin da bai dace ba. Hakan ba ya nufin zaginsu ko kuma wulaƙanta su.​—Karin Magana 4:1.