Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 54

Mene ne Aikin “Bawan nan Mai Aminci, Mai Hikima”?

Mene ne Aikin “Bawan nan Mai Aminci, Mai Hikima”?

Yesu ne shugaban ikilisiya. (Afisawa 5:23) Shi ne yake yi wa mabiyansa ja-goranci ta wurin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Karanta Matiyu 24:45.) Yesu ne ya naɗa wannan “bawan” kuma ya ba shi ikon yanke wasu shawarwari. Duk da haka, wajibi ne bawan nan ya yi biyayya ga Yesu kuma ya yi wa shafaffu hidima. Wane ne wannan bawan? Ta yaya bawan yake kula da mu?

1. Wane ne “bawan nan mai aminci, mai hikima”?

Jehobah ya sha amfani da mutum ɗaya ko mazaje kaɗan don su ja-goranci mutanensa. (Malakai 2:7; Ibraniyawa 1:1) Bayan mutuwar Yesu, manzanninsa da wasu dattawa a Urushalima ne suka soma ja-goranci. (Ayyukan Manzanni 15:2) A yau, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne take tanadar mana da abubuwan da muke bukata don ibada kuma take yi mana ja-goranci a wa’azi. Hukumar nan ita ce “bawan nan mai aminci, mai hikima, wanda maigidansa [Yesu] ya” naɗa. (Matiyu 24:45a) Dukan membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu shafaffu ne, waɗanda za su yi sarauta da Yesu a Mulkin sama bayan rayuwarsu a duniya.

2. Mene ne bawan nan mai aminci yake tanadar mana?

Yesu ya ce bawan nan zai ba Kiristoci “abincinsu a kan lokaci.” (Matiyu 24:45b) Kamar yadda abinci yake ba mu ƙarfi da lafiya, haka ma umurnan da ke Kalmar Allah suke ba mu ƙarfi mu kasance da aminci ga Jehobah kuma mu yi aikin da Yesu ya ce mu yi. (1 Timoti 4:6) Muna samun umurnan nan daga taron ikilisiya da taron da’ira da taron yanki da littattafanmu da kuma bidiyoyi. Dukan abubuwan nan suna taimaka mana mu san nufin Allah kuma mu ƙarfafa dangantakarmu da shi.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi dalilin da ya sa muke bukatar “bawan nan mai aminci, mai hikima,” wato Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne take tanadar mana abubuwan da muke bukata don bauta wa Jehobah, da yi mana ja-goranci da kuma taimaka wa Shaidun Jehobah a faɗin duniya

3. Wajibi ne bayin Jehobah su kasance da tsari

Yesu ne ya ja-goranci Kiristoci na farko. Hakazalika, Yesu ne yake yi wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ja-goranci a ayyukan da suke yi. Ku kalli BIDIYON nan.

Ku karanta 1 Korintiyawa 14:​33, 40, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya ayoyin nan suka nuna cewa Jehobah yana so bayinsa su kasance da tsari?

4. Bawan nan mai aminci ne yake tsara yadda muke wa’azi

Wa’azi ne aiki mafi muhimmanci da Kiristoci na farko suka yi. Ku karanta Ayyukan Manzanni 8:​14, 25, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Su waye ne suka ja-goranci wa’azin Kiristoci na farko?

  • Ta yaya Bitrus da Yohanna suka bi umurnin da sauran manzannin suka bayar?

Wa’azi ne aiki mafi muhimmanci da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take tsarawa. Ku kalli BIDIYON nan.

Yesu ya ce yin wa’azi yana da muhimmanci. Ku karanta Markus 13:​10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take ɗaukan wa’azi da muhimmanci sosai?

  • Me ya sa muke bukatar “bawan nan mai aminci, mai hikima” ya tsara wa’azin da muke yi a faɗin duniya?

5. Bawan nan mai aminci ne yake mana ja-goranci

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne take wa Kiristoci a faɗin duniya ja-goranci. Ta yaya take yanke shawara a kan umurnan da za su bayar? Bari mu ga yadda hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci na farko ta yi hakan. Ku karanta Ayyukan Manzanni 15:​1, 2, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya jawo gardama tsakanin Kiristoci na farko?

  • Daga wurin waye ne Bulus da Barnaba, da kuma sauran suka nemi taimako don su magance matsalar?

Ku karanta Ayyukan Manzanni 15:​12-18, 23-29, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kafin ta yanke shawara, mene ne hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci na farko ta yi don ta nemi taimakon Allah game da batun?​—Ka duba ayoyi na 12, 15, da 28.

Ku karanta Ayyukan Manzanni 15:​30, 31 da 16:4, 5, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me Kiristoci na farko suka yi bayan da suka sami umurni daga hukumar da ke kula da ayyukansu a lokacin?

  • Ta yaya Jehobah ya albarkace su don sun yi biyayya?

Ku karanta 2 Timoti 3:16 da Yakub 1:​5, sai ku tattauna tambayar nan:

  • A ina ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take samun ja-goranci sa’ad da take so ta yanke shawara?

WASU SUN CE: “Ra’ayin mutane ne kawai muke bi idan muna bin abin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take faɗa.”

  • Me ya nuna maka cewa Yesu ne yake wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ja-goranci?

TAƘAITAWA

Yesu ne ya naɗa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu a matsayin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” Hukumar ce take wa Kiristoci ja-goranci a faɗin duniya kuma tana tanadar da abubuwan da suke bukata don su bauta wa Allah.

Bita

  • Waye ne ya naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima”?

  • Ta yaya Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take kula da mu?

  • Ka gaskata cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne “bawan nan mai aminci, mai hikima”?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga tsarin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take bi.

“Su Waye Ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take tabbatar cewa abin da take koyarwa gaskiya ne.

Yadda Muke Wallafa Bayanai na Gaskiya a Littattafanmu (17:18)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suke ji game da aikin da Yesu ya ba su.

Hidima da Muke So Sosai (7:04)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda taron ikilisiya da na yanki suke nuna cewa Jehobah ne yake ma Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ja-goranci.

Jehobah Yana Koyar da Bayinsa (9:39)