Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 58

Ka Ci gaba da Rike Aminci ga Jehobah

Ka Ci gaba da Rike Aminci ga Jehobah

Kiristoci na gaske ba za su taɓa barin kowa ko wani abu ya hana su bauta wa Jehobah ba. Babu shaka, kai ma haka kake ji. Yadda kake riƙe aminci yana sa Jehobah farin ciki. (Karanta 1 Tarihi 28:9.) Mene ne zai iya hana ka riƙe aminci, kuma me zai taimaka maka?

1. Ta yaya wasu za su iya sa riƙe aminci ga Jehobah ya yi mana wuya?

Wasu mutane za su so su sa mu daina bauta wa Jehobah. Waye ne kake ganin zai iya yin hakan? Wasu da suka daina bauta wa Jehobah suna tabka ƙarya game da ƙungiyarmu domin su hana mu kasancewa da bangaskiya. Ana kiran su ’yan ridda. Ƙari ga haka, shugabannin addinai suna yaɗa ƙarya game da mu domin su sa waɗanda ba su mai da hankali ba su daina bauta wa Jehobah. Bai kamata mu yi gardama da irin mutanen nan ba, ko mu karanta littattafansu ko shafinsu a dandalin sada zumunta ko mu shiga dandalinsu na Intane ko kuma mu kalli bidiyoyinsu. Yesu ya yi magana game da waɗanda suke so su hana mutane bauta wa Jehobah, ya ce: “Bar su kawai. Su makafi ne masu yi wa makafi ja-gora. Idan kuwa makaho ya yi wa wani makaho ja-gora, ai, dukansu za su fāɗi cikin rami.”​—Matiyu 15:14.

2. Ta yaya shawarwarin da muka yanke za su nuna cewa mun riƙe aminci ga Jehobah?

Ƙaunarmu ga Jehobah za ta sa mu guji yin sha’ani da addinin ƙarya. Bai kamata aikin da muke yi, ko wata ƙungiya da muke ciki, ko wani abin da muke yi ya kasance da alaƙa da addinin ƙarya ba. Jehobah ya gargaɗe mu cewa: “Ku fito, ya mutanena, daga [Babila Mai Girma],” wato Babila Babba.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​2, 4.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu guji barin wani ya hana mu riƙe aminci ga Jehobah, da yadda za mu nuna aminci ta wurin fita daga Babila Babba.

3. Ka yi hattara da malaman ƙarya

Me ya kamata mu yi idan muka ji an yi baƙar magana game da ƙungiyar Jehobah? Ku karanta Karin Magana 14:​15, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa bai kamata mu amince da dukan abin da muka ji ba?

Ku karanta 2 Yohanna 9-11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya kamata mu yi wa ’yan ridda?

  • Ko da ba mu yi magana da ’yan ridda kai tsaye ba, a ina ne za mu iya ganin koyarwarsu?

  • Yaya kake ganin Jehobah zai ji idan mun saurari baƙar magana game da shi ko ƙungiyarsa?

4. Ka riƙe aminci ga Jehobah idan wani ɗan’uwa ya yi zunubi

Idan ka san cewa wani ɗan’uwa ya yi zunubi mai tsanani, me ya kamata ka yi? Ka yi la’akari da wata ƙa’ida da Jehobah ya ba Isra’ilawa a dā. Ku karanta Littafin Firistoci 5:1.

Kamar yadda ayar nan ta nuna, idan mun san cewa wani ɗan’uwa ya yi zunubi mai tsanani, ya kamata mu gaya wa dattawa. Amma kafin mu yi hakan, zai dace mu gaya wa mai zunubin ya je ya faɗa musu da kansa. Idan ya ƙi zuwa, ya kamata mu je mu gaya wa dattawa don hakan zai nuna mu masu aminci ne. Ta yaya matakin da muka ɗauka zai nuna cewa muna da aminci da kuma ƙauna ga . . .

  • Jehobah?

  • mai zunubin?

  • ’yan’uwa a ikilisiya?

Ka taimaka wa ɗan’uwa da ke cikin matsala!

5. Ku fito daga Babila Babba

Ku karanta Luka 4:8 da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​4, 5, sai ka amsa tambayoyin nan:

  • Har ila ni memban wani addinin ƙarya ne?

  • Ina cikin wata ƙungiyar da ke da alaƙa da wani addinin ƙarya?

  • Aikin da nake yi yana taimaka ma wani addinin ƙarya ne?

  • Akwai wasu abubuwa a rayuwata da ya kamata in bari don suna da alaƙa da addinin ƙarya?

  • Idan amsata ‘e’ ce ga ɗaya daga cikin waɗannan tambayoyin, mene ne ya kamata in yi?

A kowane yanayi, ka yanke shawarar da za ta sa ka kasance da kwanciyar hankali kuma ka riƙe aminci ga Jehobah.

Me za ka yi idan aka ce ka ba da gudummawa don a tallafa ma wani addini?

WASU SUN CE: “Zan so in san abin da ’yan ridda suke faɗa game da Shaidun Jehobah don in gaya musu gaskiya.”

  • Kana ganin hakan ya dace? Me ya sa?

TAƘAITAWA

Don mu riƙe aminci ga Jehobah, wajibi ne mu guje ma waɗanda suke ƙoƙari su ruɗe mu.

Bita

  • Me ya sa bai dace mu saurari koyarwar ’yan ridda ba?

  • Idan mun san cewa wani ɗan’uwa ya yi zunubi mai tsanani, mene ne ya kamata mu yi?

  • Ta yaya za mu bi umurnin da Jehobah ya ba mu cewa mu fito daga addinin ƙarya?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku san abin da za ku yi idan mutane suka yaɗa ƙarya game da Shaidun Jehobah.

“Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?” (Hasumiyar Tsaro, Agusta 2018)

Ku karanta talifin nan don ku san yadda mutum zai iya gane ƙungiyoyi ko ayyukan da ke da alaƙa da Babila Babba.

“Ka Ci gaba da Ƙwazo a Ƙarshen ‘Kwanaki na Ƙarshe’” (Hasumiyar Tsaro, Oktoba 2019, sakin layi na 16-​18)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da wasu ’yan adawa suka yi don su raunana bangaskiyarmu.

Kada Ka Yarda A Ruɗe Ka (9:32)

Ku karanta labarin nan “Na Soma Biɗar Allah Tun Ina Yaro,” don ku ga yadda wani firist ɗin addinin Shinto ya daina bin addinin ƙarya.

“Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2011)