Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 59

Za Ka Iya Jimre Tsanantawa

Za Ka Iya Jimre Tsanantawa

A kwana a tashi, mutane za su yi ƙoƙari su sa kowannenmu mu daina bauta wa Jehobah. Ya kamata mu bar hakan ya tsorata mu ne?

1. Me ya sa ya kamata mu san cewa za a tsananta mana?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.” (2 Timoti 3:12) An tsananta wa Yesu domin shi ba ya saka hannu a harkokin duniyar Shaiɗan. Mu ma ba na duniya ba ne. Saboda haka, ba ma mamaki idan gwamnatocin duniya da ƙungiyoyin addinai suka tsananta mana.​—Yohanna 15:​18, 19.

2. Ta yaya za mu iya yin shiri don tsanantawa?

Ya kamata mu riƙa dogara sosai ga Jehobah a yanzu. Muna bukatar mu keɓe lokaci kowace rana don mu yi addu’a kuma mu karanta Kalmar Allah. Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa halartan taron ikilisiya a kai a kai. Waɗannan ayyukan za su ƙarfafa ka ka kasance da ƙarfin zuciya sa’ad da kake fuskantar tsanantawa, ko da membobin iyalinka ne suke tsananta maka. Manzo Bulus wanda ya sha fuskantar tsanantawa ya ce: “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba.”​​—Ibraniyawa 13:6.

Za mu ƙara kasancewa da ƙarfin zuciya idan muna wa’azi a kai a kai. Yin wa’azi yana sa mu dogara ga Jehobah kuma mu daina jin tsoron mutum. (Karin Magana 29:25) Idan muna wa’azi da ƙarfin zuciya a yanzu, za mu ci gaba da yin hakan ko da hukumomi sun saka wa aikinmu takunkumi.​—1 Tasalonikawa 2:2.

3. Ta yaya za mu amfana idan muka jimre tsanantawa?

Gaskiyar ita ce, ba ma farin ciki sa’ad da aka tsananta mana. Amma idan muka jimre, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Za mu kuma kusaci Jehobah domin ya taimaka mana sa’ad da muke gani ba za mu iya jimrewa kuma ba. (Karanta Yakub 1:​2-4.) Jehobah yana baƙin ciki sa’ad da muke shan wahala, amma yana farin ciki sa’ad da muka jimre. Littafi Mai Tsarki ya ce: “In kun yi aiki mai kyau, sa’an nan kun sha wahala a kansa, kun kuma haƙura, to, shi ne abin karɓa ga Allah.” (1 Bitrus 2:20) Idan muka riƙe amincinmu, Jehobah zai albarkace mu da rai na har abada a sabuwar duniya. A lokacin, babu wanda zai tsananta ma waɗanda suke bauta masa.​—Matiyu 24:13.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda zai yiwu mu riƙe amincinmu ga Jehobah ko da mutane suna tsananta mana da kuma yadda Jehobah zai albarkace mu.

4. Za ka iya jimrewa sa’ad da iyalinka suka tsananta maka

Yesu ya san cewa wasu a iyalinmu ba za su so mu bauta wa Jehobah ba. Ku karanta Matiyu 10:​34-36, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne membobin iyali za su iya faɗa ko kuma su yi sa’ad da ɗan’uwansu ya tsai da shawara cewa zai soma bauta wa Jehobah?

Don ku ga wani misali, ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Mene ne za ka iya yi idan wani danginka ko abokinka ya yi ƙoƙari ya hana ka bauta wa Jehobah?

Ku karanta Zabura 27:10 da Markus 10:​29, 30. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya wannan alkawarin zai taimaka maka idan membobin iyalinka ko abokanka suka yi ƙoƙari su hana ka bauta wa Jehobah?

5. Ka ci gaba da bauta wa Jehobah ko da kana fuskantar tsanantawa

Muna bukatar mu kasance da ƙarfin zuciya don bauta wa Jehobah sa’ad da mutane suke ƙoƙari su hana mu yin hakan. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya misalan da aka nuna a wannan bidiyon suka ƙarfafa ka?

Ku karanta Ayyukan Manzanni 5:​27-29 da Ibraniyawa 10:​24, 25. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da bauta wa Jehobah ko da gwamnati ta ce kada mu yi wa’azi ko kuma taro?

6. Jehobah zai taimaka maka ka jimre

Shaidun Jehobah, manya da yara a faɗin duniya sun ci gaba da bauta wa Jehobah duk da cewa ana tsananta musu. Don ku ga abin da ya taimaka musu, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, mene ne ya taimaka wa waɗannan Shaidun su jimre?

Ku karanta Romawa 8:​35, 37-39 da Filibiyawa 4:13. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya wannan nassin ya tabbatar maka da cewa za ka iya jimre kowace jarrabawa?

Ku karanta Matiyu 5:​10-12, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa za ka riƙa farin ciki ko da ana tsananta maka?

Shaidun Jehobah da yawa sun ci gaba da bauta masa duk da cewa ana tsananta musu. Kai ma za ka iya yin hakan!

WASU SUN CE: “Ba zan iya jimre tsanantawa ba.”

  • Waɗanne nassosi ne za su iya taimaka musu?

TAƘAITAWA

Jehobah yana farin ciki don ƙoƙarce-ƙoƙarce da muke yi mu bauta masa ko da ana tsananta mana. Da taimakonsa, za mu iya jimrewa!

Bita

  • Me ya sa ya kamata Kiristoci su san cewa za a tsananta musu?

  • Me za ka yi yanzu don ka kasance a shirye a lokacin tsanantawa?

  • Mene ne zai taimaka maka ka kasance da gaba gaɗin bauta wa Jehobah ko da kana fuskantar jarrabawa?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani matashi ya bayyana yadda Jehobah ya taimaka masa ya jimre sa’ad da aka saka shi a kurkuku domin imaninsa.

Yadda Na Jimre da Tsanantawa (2:34)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da ya taimaka ma wata mata da miji su ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci shekaru da yawa duk da cewa ana tsananta musu.

Bauta wa Jehobah a Yanayi Dabam-dabam (7:11)

Ku karanta talifin nan don ku san yadda za ku kasance da ƙarfin zuciya sa’ad da ake tsananta muku.

“Ku Yi Shiri Yanzu Don Tsanantawa” (Hasumiyar Tsaro, Yuli 2019)

Wane ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi sa’ad da iyalanmu suke tsananta mana, kuma me za mu iya yi don a sami zaman lafiya kuma mu riƙe amincinmu ga Jehobah? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Gaskiya Ba ta Kawo ‘Salama, Amma Takobi’” (Hasumiyar Tsaro, Oktoba 2017)