Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 60

Ka Ci Gaba da Karfafa Dangantakarka da Jehobah

Ka Ci Gaba da Karfafa Dangantakarka da Jehobah

Ka riga ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah a nazarin nan. Abubuwan da ka koya ya sa ka ƙaunace shi kuma wataƙila ka yi alkawarin bauta masa kuma ka yi baftisma. Idan ba ka yi hakan ba, mai yiwuwa kana da niyyar yin hakan nan ba da daɗewa ba. Amma bayan ka yi baftisma, za ka ci gaba da kusantar Jehobah. Za ka ci gaba da kusantar Jehobah har abada. Ta yaya za ka yi hakan?

1. Me ya sa zai dace ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

Wajibi ne mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Me ya sa? Domin kada mu “juya baya ga Allah Mai Rai.” (Ibraniyawa 3:12) Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah? Yin wa’azi da ƙwazo da kuma neman wasu hanyoyin da za mu inganta bautarmu ga Allah. (Karanta Filibiyawa 3:16.) Bauta wa Jehobah ita ce rayuwa mafi inganci!​—Zabura 84:10.

2. Me kuma za ka ci gaba da yi?

Ko da yake ka zo ƙarshen nazarinka, za ka ci gaba da yin rayuwar da ta dace da Kirista. Littafi Mai Tsarki ya ce mu ‘ɗauki sabon hali.’ (Afisawa 4:​23, 24) Yayin da ka ci gaba da nazarin Kalmar Allah da halartan taron ikilisiya, za ka koyi sabbin abubuwa game da Jehobah da kuma halayensa. Ka yi ƙoƙari ka koyi halayensa a rayuwarka. Ka ci gaba da yin canje-canje da ya kamata ka yi don ka faranta ran Jehobah.

3. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ka sami ci gaba?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah . . . da kansa zai mai da ku cikakku zai kafa ku, zai kuma ƙarfafa ku.” (1 Bitrus 5:10) Dukanmu za mu fuskanci jarrabawar yin abin da bai dace ba. Amma Jehobah yana ba mu abin da muke bukata don mu yi nasara. (Zabura 139:​23, 24) Ya yi alkawari cewa zai sa ka kasance da niyya da kuma ƙarfin bauta masa da aminci.​—Karanta Filibiyawa 2:13.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah da kuma yadda zai albarkace ka.

4. Ka ci gaba da addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki

Yin addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki sun taimaka maka ka zama aminin Jehobah. Ta yaya yin waɗannan abubuwa za su taimaka maka ka ci gaba da kusantar sa?

Ku karanta Zabura 62:​8, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, ta yaya za ka iya inganta yadda kake addu’a?

Ku karanta Zabura 1:​2, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, ta yaya za ka inganta yadda kake nazarin Littafi Mai Tsarki?

Mene ne za ka yi don ka amfana sosai daga nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi? Don samun wasu shawarwari, ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • Wanne cikin shawarwarin da ke bidiyon nan ne za ka so ka bi?

  • Waɗanne batutuwa ne za ka so ka yi nazari a kansu?

5. Ka tsara yadda za ka ƙara ƙwazo a ibadarka

Kafa maƙasudai a ibadarka ga Jehobah zai taimaka maka ka sami ci gaba. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon nan, ta yaya Cameron ta amfana don ta kafa maƙasudai a hidimarta?

Ba kowa ba ne zai iya ƙaura zuwa wata ƙasa don ya yi wa’azi ba. Amma dukanmu za mu iya kafa maƙasudai da za mu iya cim ma. Ku karanta Karin Magana 21:​5, sai ka yi tunanin maƙasudai da za ka so ka kafa wa kanka . . .

  • a ikilisiya.

  • a wa’azi.

Ta yaya ƙa’idar da ke ayar za ta taimaka maka ka cim ma maƙasudanka?

Maƙasudai da za ka iya cim ma

  • Ka inganta yadda kake addu’a.

  • Ka karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya.

  • Ka yi ƙoƙari ka san kowa a ikilisiyarku.

  • Ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani.

  • Ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci ko na kullum.

  • Idan kai ɗan’uwa ne, ka yi ƙoƙari ka zama bawa mai hidima.

6. Ka ji daɗin rayuwa har abada!

Ku karanta Zabura 22:​26, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me za ka yi don ka ji daɗin rayuwa yanzu da kuma har abada?

TAƘAITAWA

Ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma ka kafa maƙasudai a ibadarka. Sa’an nan za ka iya jin daɗin rayuwa yanzu da kuma har abada!

Bita

  • Me ya sa za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka maka ka bauta masa da aminci?

  • Ta yaya za ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

  • Ta yaya ƙara ƙwazo a ibadarka zai taimaka maka ka samu ci gaba?

Ka Gwada Wannan Cikin Shekara Ɗaya

KA BINCIKA

Mene ne Jehobah ya fi so: Mu nuna sau ɗaya cewa mu masu ibada ne sosai ko kuwa mu ci gaba da bauta masa cikin aminci muddar ranmu? Ku kalli bidiyon nan don ku ga amsar.

Ka Zama Mai Aminci Kamar Ibrahim (9:20)

Bawan Allah mai aminci ma zai iya yin sanyin gwiwa. Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da zai taimaka wa mutum ya ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.

Nazari da Bimbini Za Su Sa Ka Ji Daɗin Wa’azi (5:25)

Ta yaya mutum zai kafa maƙasudai a ibadarsa kuma ya cim ma su? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Ka Kafa Maƙasudai da Za Su Taimaka Maka Ka Bauta wa Jehobah” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Yuli, 2004)

Me ya sa yake da muhimmanci mu zama Kirista da ya manyanta, kuma ta yaya za mu iya yin hakan? Ku karanta talifin nan don ku ga amsar.

“Ka Nace Bi Zuwa Kamala Don ‘Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa’” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Mayu, 2009)