Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bitar Sashe na 1

Bitar Sashe na 1

Ka tattauna tambayoyi na gaba da malaminka:

  1. Wane alkawari da ke Littafi Mai Tsarki game da nan gaba ne ka fi so?

    (Ka duba Darasi na 02.)

  2. Me ya sa ka amince cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne?

    (Ka duba Darasi na 03 da 05.)

  3. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi amfani da sunan Allah, wato Jehobah?

    (Ka duba Darasi na 04.)

  4. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ne mai ba da rai. (Zabura 36:⁠9) Ka yarda da hakan?

    (Ka duba Darasi na 06.)

  5. Ku karanta Karin Magana 3:⁠32.

    • Me ya sa Jehobah ne amininmu da babu kamar sa?

    • Mene ne Jehobah yake bukata daga ­aminansa? Kana ganin hakan ya dace?

      (Ka duba Darasi na 07 da 08.)

  6. Ku karanta Zabura 62:⁠8.

    • Waɗanne abubuwa ne ka yi addu’a game da su? Waɗanne abubuwa ne kuma za ka iya yin addu’a a kansu?

    • Ta yaya Jehobah yake amsa addu’o’i?

      (Ka duba Darasi na 09.)

  7. Ku karanta Ibraniyawa 10:​24, 25.

    • Ta yaya za ka amfana daga taron Shaidun Jehobah?

    • Kana ganin zai dace ka halarci taron, ko da yin hakan yana da wuya?

      (Ka duba Darasi na 10.)

  8. Me ya sa yake da kyau ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki? A wane lokaci ne kake karanta ­Littafi Mai Tsarki kowace rana?

    (Ka duba Darasi na 11.)

  9. Mene ne ka fi jin daɗinsa a karatunka na ­Littafi Mai Tsarki?

  10. Tun da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ­waɗanne ƙalubale ne ka fuskanta? Mene ne zai taimaka maka ka ci gaba da nazari?

    (Ka duba Darasi na 12.)