Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bitar Sashe na 3

Bitar Sashe na 3

Ka tattauna tambayoyi na gaba da malaminka:

  1. Ku karanta Karin Magana 27:11.

    • Me ya sa kake so ka kasance da aminci ga Jehobah?

      (Ka duba Darasi na 34.)

  2. Ta yaya za ka tsai da shawarwari masu kyau a batun da babu takamaiman doka a Littafi Mai Tsarki?

    (Ka duba Darasi na 35.)

  3. Ta yaya za ka zama mai faɗin gaskiya a dukan abubuwa?

    (Ka duba Darasi na 36.)

  4. Ku karanta Matiyu 6:33.

    • Ta yaya za mu ci gaba da sa bautar Allah a kan gaba fiye da aiki da kuɗi?

      (Ka duba Darasi na 37.)

  5. A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna kana ­daraja rai yadda Jehobah yake yi?

    (Ka duba Darasi na 38.)

  6. Ku karanta Ayyukan Manzanni 15:29.

    • Ta yaya za ka bi dokar Jehobah game da jini?

    • Kana ganin dokokin da ya ba mu game da hakan sun dace?

      (Ka duba Darasi na 39.)

  7. Ku karanta 2 Korintiyawa 7:1.

    • Mene ne kasancewa da tsabta a zahiri da zuciya yake nufi?

      (Ka duba Darasi na 40.)

  8. Ku karanta 1 Korintiyawa 6:​9, 10.

    • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da jima’i? Ka amince da hakan kuwa?

    • Wane umurni ne Littafi Mai Tsarki ya ba da game da shan giya?

      (Ka duba Darasi na 41 da 43.)

  9. Ku karanta Matiyu 19:​4-6, 9.

    • Waɗanne ƙa’idodi ne Allah ya bayar game da aure?

    • Me ya sa wajibi ne a yi aure ko kuma a kashe aure bisa doka?

      (Ka duba Darasi na 42.)

  10. Waɗanne bukukuwa ne suke ɓata wa Jehobah rai, kuma me ya sa?

    (Ka duba Darasi na 44.)

  11. Ku karanta Yohanna 17:16 da Ayyukan ­Manzanni 5:29.

    • Ta yaya za ka guji saka hannu a harkokin duniya?

    • Idan dokar ’yan Adam ta saɓa wa dokar Allah, me za ka yi?

      (Ka duba Darasi na 45.)

  12. Ku karanta Markus 12:30.

    • Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar ­Jehobah?

      (Ka duba Darasi na 46 da 47.)