Yadda za ka amfana daga littafin nan
Ka soma da karanta bayanan da ke shafin nan da na gaba, sai Ka kalli BIDIYON nan.
SASHE NA FARKO
Don ka shirya nazarin kowane darasi, ka karanta sashe na farko da tambayoyi (A) da kuma nassosi (B) da suka nanata batutuwa masu muhimmanci. Ka lura cewa an rubuta “karanta” ko “ku karanta” a wasu nassosi.
SASHE NA TSAKIYA
Furuci na farko (C) da ke sashen nan Ka Yi Bincike Sosai ya bayyana abin da zai biyo baya. Ƙaramin jigo (D) ya nuna abin da za a tattauna. Ka karanta nassosin tare da malaminka, ka amsa tambayoyin, kuma ka kalli bidiyoyin.
BIDIYOYI da SAUTI za su taimaka maka ka ƙara fahimtar darasin. Wasu bidiyoyin sun nuna asalin abubuwan da suka faru. Wasu kuma wasan kwaikwayo ne, ba asalin abubuwan da suka faru da mutanen da ke cikin wasan ba ne, amma ana dai nuna abin da zai iya faruwa ne.
Ka kalli hotunan da bayanin da ke ƙarƙashinsa (E), kuma ka yi tunani a kan yadda za ka amsa tambayar da ke sashen nan Wasu Sun Ce (F).
SASHE NA ƘARSHE
An kammala darasin da sashen nan Taƙaitawa da kuma Bita (G). Ka rubuta kwanan watan da ka kammala nazarin darasin. A sashen Maƙasudi, (H) za ka sami damar yin amfani da darasin da ka koya. A sashen Ka Bincika, (I) za ka sami ƙarin littattafai da kuma bidiyoyi.
Abin da Ke Ciki
|
|
|
|
Yadda za ka samo ayoyi
Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi ƙananan littatafai guda 66. An raba shi zuwa sashe biyu: Nassosin Ibrananci da Aramaic (“Tsohon Alkawari”) da kuma Nassosin Helenanci (“Sabon Alkawari”).
Idan aka ambata wani nassi a wannan littafin, akan nuna sunan littafin (A), da surar (B), da kuma ayar ko ayoyin (C).
Alal misali, Yohanna 17:3 yana nufin littafin Yohanna, sura ta 17, aya ta 3.