Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki


Yadda za ka amfana daga wannan kasidar

Yadda za ka amfana daga wannan kasidar

Ka ce a yi nazari da kai: Ka ce mutumin da ya ba ka wannan ƙasidar ya yi nazari da kai, ko kuma ka cika fom da ke dandalinmu, jw.org.

SASHE NA FARKO

Ka karanta kowane sakin layi, har da tambayoyin (A) da nassosin (B) da suka nanata batutuwa masu muhimmanci. Ka lura cewa an rubuta “karanta” a wasu nassosi.

SASHE NA TSAKIYA

Furucin (C) da ke sashen nan Ka Yi Bincike Sosai ya bayyana abin da zai biyo baya. Ƙaramin jigo (D) ya nuna abin da za a tattauna. Ka karanta nassosin, ka amsa tambayoyin, kuma ka kalli bidiyoyin (E).

Ka kalli hotunan, ka karanta bayanin da ke hotunan (F), kuma ka yi tunani a kan yadda za ka amsa tambayar da ke sashen nan Wasu Sun Ce (G).

SASHE NA ƘARSHE

An kammala darasin da sashen nan (H) Taƙaitawa da kuma Bita. Ka rubuta kwanan watan da ka kammala nazarin darasin. A sashen Maƙasudi, (I) za ka sami damar yin amfani da darasin da ka koya. A sashen Ka Bincika, (J) za ka sami ƙarin littattafai da kuma bidiyoyi.

Yadda za ka samo ayoyi

Nassosi na ɗauke da sunan littafin (A), da surar (B), da kuma ayar ko ayoyin (C). Alal misali, Yohanna 17:3 yana nufin littafin Yohanna, sura ta 17, aya ta 3.