Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 153

Ka Ba Ni Karfin Hali

Ka Ba Ni Karfin Hali

(2 Sarakuna 6:16)

  1. 1. Allah ina tsoro​—

    Ban san me zan yi ba.

    Amma kana kiyaye ni;

    Kana tare da ni.

    Duk da matsaloli,

    Na gaskata cewa:

    Kai Allah ne mai aminci;

    Ba za ka bar ni ba.

    (AMSHI)

    Jehobah, ka taimaka min

    In rika tunawa

    Cewa kana nan tare da mu.

    Don kar in ji tsoro.

    In yi karfin hali;

    In jimre har karshe.

    Ka ba ni karfin hali;

    Kai mai nasara ne.

  2. 2. Sai da Taimakonka.

    Zan iya jimrewa.

    Ikonka babu iyaka;

    Kana kula da ni.

    Allah ina roko,

    Ka ban karfin hali.

    Domin kada in ji tsoro

    Ko zan rasa raina.

    (AMSHI)

    Jehobah, ka taimaka min

    In rika tunawa

    Cewa kana nan tare da mu.

    Don kar in ji tsoro.

    In yi karfin hali;

    In jimre har karshe.

    Ka ba ni karfin hali;

    Kai mai nasara ne.

    (AMSHI)

    Jehobah, ka taimaka min

    In rika tunawa

    Cewa kana nan tare da mu.

    Don kar in ji tsoro.

    In yi karfin hali;

    In jimre har karshe.

    Ka ba ni karfin hali;

    Kai mai nasara ne.

    Ka ba ni karfin hali;

    Kai mai nasara ne.