Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Ya ꞌYanꞌuwa:

Yadda muke ƙaunar Jehobah da kuma mutane ne yake sa mu bi umurnin Yesu cewa: “Ku je . . . ku sa [mutane] su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma.” (Mat. 28:​19, 20; Mar. 12:​28-31) Idan muna nuna wa mutane irin ƙaunar nan, za mu taimaki “waɗanda suke da zuciya ta samun rai na har abada.”—A. M. 13:​48, New World Translation.

A dā, muna yawan gaya wa mutane abin da muka haddace ne ko kuma mu ba su littattafanmu. Amma a yanzu, muna bukatar mu kyautata yadda muke tattaunawa da mutane. Muna so mu nuna musu ƙauna ta wajen tattauna abubuwan da suka fi so. Hakan yana nufin mu kasance a shirye don mu canja batun da muke so mu tattauna da su, mu mai da hankali ga bukatu da kuma damuwar kowane mutum. Ta yaya ƙasidar nan za ta taimaka mana mu iya yin hakan?

Ƙasidar tana ɗauke da darussa 12, da suka tattauna halayen da muke bukatar mu kasance da su don mu iya nuna wa mutane ƙauna kuma mu taimaka musu su zama almajiran Yesu. Kowane darasi zai tattauna halin da Yesu ko kuma wani Kirista a ƙarni na farko ya nuna a waꞌazi. Muna so mu mai da hankali ga nuna wa mutane ƙauna, maimakon mu gaya musu abin da muka haddace kawai. Ko da yake muna bukatar dukan halayen a fannoni dabam-dabam na waꞌazinmu, za mu ga yadda wasu halayen za su fi taimaka mana saꞌad da muke tattaunawa da mutane. Za mu kuma ga yadda wasu halayen za su taimaka mana saꞌad da muke komawa ziyara ko kuma muke nazarin Littafi Mai Tsarki.

Yayin da kake nazarin kowanne darasi, ka yi tunanin yadda za ka iya nuna halin idan kana tattaunawa da mutane a unguwarku. Ka yi ƙoƙari don ka ƙara ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Ƙaunar ce hali mafi muhimmanci da za ta sa ka iya taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu.

Muna farin ciki sosai don gatan da muke da shi na yin aiki tare da ku. (Zaf. 3:9) Bari Jehobah ya yi muku albarka yayin da kuke ƙaunar mutane da kuma taimaka musu su zama almajiran Yesu!

ꞌYanꞌuwanku,

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah